Jadawalin Premier: Da wa Arsenal, City da United za su kara a ranar farko?

Coventry City celebrate after winning the Championship in 2025

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Coventry City ta lashe Championship a bara
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Sabuwar ƙungiyar da ta hau Premier League da za a fara daga watan Agusta, Coventry za ta je gidan Arsenal, wadda ta lashe Premier League don buga wasan farko a kakar 2026/27.

Shi ne wasan da za a buga ranar Juma'a shi kaɗai, kuma karon farko da Coventy za ta buga Premier League tun bayan shekara 25.

Wannan shi ne karon farko da Arsenal ta lashe Premier League ƙarƙashin Mikel Arteta a karon farko tun bayan 2004.

Hull City ta samu gurbin shiga Premier League, bayan nasara a wasan cike gurbi za ta karɓi baƙuncin Manchester Manchester United ranar 22 ga watan Agusta, yayin da wata sabuwar ƙungiyar da za ta fara buga gasar, Ipswich za ta kece raini da Sunderland.

Manchester City za ta fara wasannin ba tare da Pep Guardiola ba tana gida da za ta yi wa Bournemouth masauki ranar Lahadi 23 ga watan Agusta, inda itma Bournemouth za ta fara wasan da sabon koci, Marco Rose.

Wasan Liverpool na farko a bana karkashin sabon koci, Andoni Iraola, wanda ya maye gurbin, Arne Slot, za ta je Newcastle a St James Park.

Chelsea ma za ta fara wasannin kakar nan karkashin sabon koci, Xabi Alonso, za ta je Fulham a Craven Cottage a karawar hamayya ranar Litinin 24 ga watan Agusta, yayin da itama Fulham za ta fuskanci wasannin bana ba tare da Marco Silva ba.

Dukkan wasannin makon farko a Premier League

Friday, 21 August

  • Arsenal v Coventry (20:00)

Saturday, 22 August

  • Hull City v Manchester United (12:30)
  • Everton v Crystal Palace (15:00)
  • Ipswich v Sunderland (15:00)
  • Nottingham Forest v Leeds (15:00)
  • Brentford v Tottenham (17:30)

Sunday, 23 August

  • Brighton v Aston Villa (14:00)
  • Manchester City v Bournemouth (14:00)
  • Newcastle v Liverpool (16:30)

Monday, 24 August

  • Fulham v Chelsea (20:00)

Yaushe ne za a fara wasannin Premier League?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sabuwar kakar wasan Premier League 2026/27, za ta fara ne a ranar Jumma'a, 21 ga Agusta, kwanaki 34 bayan wasan ƙarshe a Gasar Kofin Duniya da take gudana a Amurka da Kanada da Mexico.

Kakar Premier League za ta ƙare a ranar Lahadi, 30 ga watan Mayun 2027, yayin da wasan ƙarshe a Champions League za a buga kwana shida tsakani tsakani da kammala babbar gasar tamaula ta Ingila.

Dukkan ranar fara kakar bana da ranar rufe wasannin, sun zo ne a makare ba kamar yadda aka saba ba, sakamkon tasirin Kofin Duniya.

Za a buga mako 33 kakar wasa mai zuwa a duk karshen mako, yayin da sauran zagaye biyar za su gudana a tsakiyar mako.

Premier League ta ce an tsara jadawalin ne domin "guje wa yin wasa rana ɗaya da na gasar zakarun Turai, inda ƙungiya tara za ta wakilci Ingila a kaka mai zuwa.

Ƙungiyoyi tara daga Premier League za su buga gasar cin kofin zakarun Turai a kaka mai zuwa, wanda ya yi daidai da mafi yawan adadin da aka taɓa samu.

Ƙungiyoyin da za su buga Champions League:

  • Arsenal FC
  • Manchester City FC
  • Manchester United FC
  • Aston Villa FC
  • Liverpool FC

Ƙungiyoyin da za su buga Europa League:

  • AFC Bournemouth
  • Sunderland AFC
  • Crystal Palace FC

Ƙungiyar da za ta buga Conference League:

  • Brighton & Hove Albion

A lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara, ba za a buga wasa biyu ba ƙasa da sa'o'i 60 ba, domin rage cunkoson jadawalin da ƙungiyoyi ke fuskanta.

A kakar da ta gabata, wasan Manchester United da Newcastle wanda United ta yi nasara da ci 1-0 shi ne kaɗai a Premier League da aka buga ranar Boxing Day. Amma a wannan karo, dukkan ƙungiyoyin za su fafata a ranar Asabar, 26 ga watan Disamba.

Haka kuma, maimakon hutun wasannin kasa da kasa guda uku wato International break, yanzu biyu za a yi kawai.

Hutun kasa da kasa na watan Satumba da na Oktoba za a haɗa su zuwa sabon hutu, wanda zai fara bayan ƙarshen makon ranar 19/20 ga watan Satumba, yayin da hutun makonni biyu na watan Nuwamba zai ci gaba da kasancewa yadda yake.

Mahimman abubuwa a Premier League ta bana

Za a samu sauyi a yadda alkalan wasan Premier League za su yi hukunci kan jan gashi da ƴan wasa ke yi, Inda aka kori ƴan wasa uku saboda wannan laifi da suka aikata a kakar 2025-26.

Dukkan jan katin guda uku da aka bayar saboda laifin jan gashi sun zo ne bayan duba bidiyon VAR, amma daga kakar wasa mai zuwa, ba duk lokacin da aka ga ɗan wasa ya ja gashin abokin hamayyarsa ba ne za a kore shi.

Maimakon haka, za a fi mayar da hankali kan girman laifin da aka yi da kuma niyyar ta aikata lafin.

An yi wannan sauyin ne domin bai wa ƴan wasa damar guje wa hukunci a lokutan da suka kama gashin abokin hamayya ba da gangan ba.

Bugu da ƙari, za a buƙaci alkalai su fi mayar da hankali kan runguma ɗan wasa ko riƙe ƴan wasa a cikin da'ira ta 18, bayan da hakan ya zama ruwan dare a lokacin bugun kusurwa da sauransu.

Za a umarci alkalai su ba da kulawa sosai ga "ayyukan riƙe da ke da tasiri kai tsaye a lokacin wasanni."

Wannan ya haɗa da ƴan wasan da "a bayyane yake cewa hankalinsu yana kan abokan hamayya ne kawai kuma suna aiwatar da riƙe maimakon kula da wasa."

Haka kuma ana shirin samar da mafita domin dakile abin da ake kira ɓata lokaci daga wajen masu tsaron raga.

Masu horarwa na amfani da wannan dabara ne domin rage kuzarin abokan hamayya, ko amfani da hakan don rike nasarar da suka yi a wasa, domin su samu makin da suke bukata.

A irin wannan yanayi, mai tsaron raga kan faɗi cikin filin wasa, sannan ya yi alamar neman likitan ƙungiya ya duba lafiyarsa, yayin da sauran ƴan wasa ke zuwa wajen koci, domin shan ruwa ko kara karɓar umarni.

Premier League na tattauna kan yadda za ta kafa dokar da za ta dakile ɓata lokaci daga wajen masu tsaron raga.

Da zarar mai tsaron raga ya ɓata lokaci sanda ya kama ƙwallo ko kuma a bugun tazara, alkalin wasa zai kirga dakika biyar, idan lokaci ya cika bai buga ƙwallon ba, za a bai wa abokiyar hamayya bugun kusurwa.

An amince da waɗannan matakai ne a taron shekara-shekara a Premier League (AGM) da aka gudanar a farkon wannan wata.

Za ka iya bibiyar wasannin ƙungiyar da kake goyon baya

Idan kai masoyin wata ƙungiya ce ta Premier League, muna da shafi na musamman da aka tanada domin samun dukkan abin da kake bukata.

Wannan shi ne wurin da za ka samu duk abin da kake buƙata a wuri guda, ciki har da sabbin labarai, bayanai na musamman, nazarin ƙwararru, ra'ayoyin magoya baya, ƙididdiga da kuma jita-jitar kasuwar 'yan wasa.

Domin fara amfani da shi, zaɓi ƙungiyarka daga cikin jerin ƙungiyoyin da ke ƙasa.

Idan kana amfani da manhajar BBC Sport, za ka iya amfani da alamar ƙararrawa (bell icon) domin yin rajista don samun sanarwar labarai kai tsaye.