Yan sanda a jihar
Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun ce sun gano wani sansani da ake tsare
da aƙalla matasa 19 masu yi wa ƙasa hidima da ƴanbindiga suka sace a baya-bayan nan.
Kwamishinan ’yan
sandan jihar, Audu Bosso, ya ce jirage marasa matuƙa sun taimaka wajen gano
sansanin, amma jami’an tsaro ba su kai ga isa wajen ba saboda ana kyautata
zaton an dasa abubuwan fashewa a zagayen wajen.
Da yake magana da
manema labarai ranar Asabar, Bosso ya ce: “Jiya mun shiga daji, mun bi sawunsu
har zuwa wani wuri. Amma a
lokacin ba mu iya kutsawa zuwa wurin da bayananmu suka nuna mana cewa suna can
ba.”
Ya ce binciken da
aka yi da jirgi marar matuƙi ya tabbatar da inda sansanin yake.
“Jirgin marar
matuƙin ya nuna mana ainihin inda suke. Amma matsalar da muke fuskanta ita ce,
bisa bayanan sirrin da muke da su, an dasa abubuwan fashewa a sansanin,” in ji
Bosso.
Ya ce ana tura
motocin katapila da motocin yaƙi masu sulke yayin da ’yan sanda ke shirin
gudanar da aikin ceto mutanen.
Omotosho Adewale,
wanda ɗansa ke cikin waɗanda aka sace, ya shaida wa BBC cewa kuɗin fansar da
masu garkuwar ke nema sun fi ƙarfinsa.
Ya ce “Naira
miliyan 50 suke nema,”.
Ya ƙara da cewa “Don
Allah, duk abin da gwamnati za ta iya yi ta taimaka mani... Na samu damar rainon yaron nan ne kawai
saboda taimako da goyon bayan da na samu daga kowa,”.
Biyan kuɗin fansa
abu ne da ya saɓawa doka a Najeriya, kuma hukumomi sun sha gargaɗin iyalan waɗanda
aka sace kada su biya. Sai dai iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su kan
fuskanci matsin lamba na biyan kuɗi domin a sako ’yan uwansu.
Ba a bayyana
takamaiman wurin da sansanin yake ba, kuma ’yan sanda ba su bayyana waɗanda ke
da alhakin sace mutanen ba.
Satar mutane
domin neman kuɗin fansa na ci gaba da kasancewa babbar matsalar tsaro a
Najeriya.
A kudu maso
gabashin ƙasar, an danganta wasu sace-sacen da aka yi a baya da ƙungiyoyin ƴan
aware, ciki har da IPOB. Sai dai hukumomi ba su danganta wannan satar da wata
ƙungiya ba.
Lamarin ya jawo
damuwa sosai, kasancewar sace mutane da yawa lokaci guda ba kasafai ake samun
irin sa a kudancin Najeriya ba kamar yadda ake samu a wasu sassan arewacin
ƙasar.
Waɗanda aka sace
sun taso ne daga Ibadan zuwa sansanin horas da masu yi wa ƙasa hidima a jihohin
Abia da Akwa Ibom, lokacin da ’yan bindiga suka kai wa motocin bas ɗinsu hari
kusa da Umunoha a jihar Imo a ranar Alhamis da ta gabata.