Mene ne sakamakon yiwuwar haramta fitar da dizel daga Amurka?

    • Marubuci, فرانسیسکو ولاسکس
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, بی‌بی‌سی
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana goyon bayan haramta sayar da man dizal daga masana'antun Amurka zuwa kasuwannin ƙasashen waje, matakin da ya zo a lokacin da tashin farashin makamashi ke ƙara matsin lamba ga direbobi gabanin zaɓukan tsakiyar wa'adin mulkin ƙasar.

A cewar Ƙungiyar Motoci ta Amurka (American Automobile Association), matsakaicin farashin fetur ya kai kusan dala $6.45 a kowace galan, kusa da mafi girman matakin da aka taɓa samu.

Yaƙin da ke gudana tsakanin Amurka da Isra'ila da Iran da kuma takurawar wadatar mai a kasuwar duniya na daga cikin abubuwan da suka haddasa tashin farashin.

Trump da masu goyon bayansa sun ce hana fitar da dizal daga Amurka zai kare masu amfani da makamashi a cikin gida daga waɗannan ƙarin farashi, amma masana na ganin aiwatar da irin wannan mataki na iya haifar da manyan sakamako na tattalin arziki a cikin Amurka da ma duniya baki ɗaya.

Nawa ne Amurka ke samarwa da fitarwa na dizal?

Amurka na ɗaya daga cikin manyan masu samar da makamashi a duniya, kuma a cewar Hukumar Bayanan Makamashi ta Amurka (U.S. Energy Information Administration), matatun man ƙasar na samar da gangunan dizal miliyan huɗu zuwa biyar a kullum.

'Amurkawa suna amfani da kusan ganguna miliyan 3.6 na wannan adadi a kowace rana.

Matatun man na fitar da sauran ganguna miliyan 1.2 zuwa 1.5 zuwa ƙasashen waje, lamarin da ya sa Amurka ta zama muhimmiyar mai samar da dizal ga kasuwar duniya.

Tsakanin kashi 60 zuwa 70 cikin ɗari na wannan man da ake fitarwa na zuwa ƙasashen Latin Amurka.

Ƙasashe kamar Mexico, Brazil, Chile da Ecuador suna matuƙar dogaro da dizal da suke shigo da shi daga Amurka domin tafiyar da harkokin sufuri, noma da masana'antu.

Ana kuma fitar da adadi mai yawa na wannan mai zuwa ƙasashen Turai kamar Faransa, Netherlands da Birtaniya, waɗanda ke neman madadin hanyoyin samun makamashi daga Gabas ta Tsakiya.

Me ya faru da farashin fetur a Amurka da sauran ƙasashe?

Farashin fetur a Amurka ya kai sabon matsayi mafi girma na sama da dala $6.50 a kowace galan, adadin da ke nuna kusan karuwar kashi 70 cikin ɗari idan aka kwatanta da bara.

Karuwar ta samo asali ne galibi daga girgizar kasuwannin makamashi bayan rikicin da ke gudana da Iran, wanda ya shafi muhimman hanyoyin jigilar kaya ta mashigar Hormuz, wata hanya ta ruwa da ke kudancin Iran wadda a yanayi na al'ada ke ɗaukar kusan kashi ɗaya cikin biyar na man fetur da iskar gas na duniya.

A Amurka, dizal ne ke ba da ƙarfin aiki ga motocin kasuwanci kamar manyan motoci, injinan noma da jiragen ƙasa masu jigilar kaya, waɗanda ake amfani da su wajen sufuri da aiwatar da ayyukan gine-gine.

Saboda haka, hauhawar farashin dizal na iya haifar da ƙarin kuɗin kayan abinci, ayyukan gine-gine da sauran kayayyaki da ayyuka da dama.

A wajen Amurka, ana amfani da dizal a motocin kasuwanci da kuma na kashin kai, kuma sakamakon tashin farashinsa iri ɗaya ne.

A Birtaniya, farashin dizal a gidajen mai ya kai matakin da ba a taɓa gani ba, tare da gargadin ƙarin kuɗin sufuri da kuma ƙarin matsin lamba ga kasafin kuɗin gidaje.

Ministan Kuɗi na Birtaniya John Healy ya shaida wa BBC cewa ƙasarsa na tattaunawa da jami'an Amurka game da yiwuwar hana fitar da dizal kuma tana shirin fuskantar irin wannan yanayi.

A halin yanzu, a Faransa da sauran ƙasashen Turai, gwamnatoci na fuskantar irin waɗannan matsalolin tsadar rayuwa sakamakon tashin farashin makamashi.

Me Trump ya ce kuma menene hujjarsa?

Donald Trump ya ce a ƙarshen makon da ya gabata cewa taƙaita ko ma hana gaba ɗaya fitar da dizal daga Amurka na iya sa karin mai ya kasance a kasuwar cikin gida tare da rage farashi ga masu amfani da makamashi na Amurka.

Ya ce gwamnatinsa na nazarin batun "cikin matuƙar muhimmanci."

Kalaman nasa sun yi kama da waɗanda ya yi a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya, inda ya ce "ya kamata a hana fitar da dizal zuwa ƙasashen waje."

Trump na cewa ajiye waɗannan karin gangunan mai a cikin Amurka na iya rage farashin makamashi tare da rage matsin lamba kan direbobi, masu tuka manyan motoci da 'yan kasuwa gabanin zaɓukan tsakiyar wa'adin mulki.

Masu goyon bayansa, ciki har da wasu 'yan majalisar Republican kamar wakili Ashley Hinson da sanata Dan Sullivan, na ganin wannan dabara a matsayin hanya mai inganci ta kare tattalin arzikin cikin gida daga girgizar waje, kuma suna cewa makamashin Amurka ya kamata ya fi amfanar ma'aikatan Amurka.

Wane tasiri ne haramta fitarwa za ta yi ga Amurka da duniya?

Ga tattalin arzikin Amurka, irin wannan haramci na iya rage farashin makamashi a ɗan gajeren lokaci ta hanyar ƙara wadatar mai a kasuwar cikin gida.

Sai dai masana nazarin makamashi sun yi gargaɗin cewa wannan mataki na iya juyawa da akasin sakamako.

David Fyfe, babban masanin tattalin arziki na Argus Media, ya ce dakatar da wadatar da Amurka ke yi wa kasuwannin duniya zai iya haddasa gagarumin tashin farashi a kasuwannin duniya.

A cewarsa, irin wannan yanayi zai ƙara kuɗin sufuri, abinci da samar da kayayyakin masana'antu a duniya, wanda a ƙarshe zai "dawo da hauhawar farashi cikin tattalin arzikin duniya."

"Za a rusa amincin Amurka a matsayin abin dogaro wajen samar da makamashi ga duniya da shawara guda ɗaya," in ji Fyfe.

Cire fiye da ganguna miliyan ɗaya a rana daga wadatar da Amurka ke yi zai haifar da gasa mai tsanani tsakanin ƙasashen Latin Amurka da Turai masu shigo da mai.

Sarah Rafol, daraktar nazari a Argus Media, ita ma ta ce ko da yake tashin farashin duniya na iya rage buƙata daga baya, a ɗan gajeren lokaci ƙarancin da zai biyo baya zai sanya matsin lamba mai tsanani ga dangantakar kasuwanci tare da ƙara hanzarta hauhawar farashi a duniya.