Arsenal na sa ido kan Rashford, Alvarez ba ya son komawa Man City

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ba ta yanke shawarar rabuwa da Marcus Rashford ba, kuma Arsenal da Barcelona na sa ido kan ɗanwasan na Ingila mai shekara 28. (Teamtalk)
Ɗanwasan tsakiya na Monaco da Senegal Lamine Camara, mai shekara 22, zai iya maye gurbin ɗanwasan tsakiya na Chelsea Enzo Fernandez. (Mail)
Newcastle ta nace kan ɗanwasan gaba na Belgium Matias Fernandez-Pardo, mai shekara 21, daga Lille. (Telegraph - subscription required)
Ɗanwasan gaba na Argentina da Atletico Madrid Julian Alvarez, mai shekara 26, ya yi watsi da tayin komawa Manchester City. (Cadena Ser - in Spanish)
Newcastle na son ɗanwasan Stuttgart Bilal El Khannouss, mai shekara 22, kodayake tana fuskantar hamayya daga Everton kan ɗanwasan na Morocco. (Sky Germany)
Arsenal ta sabunta buƙatar ta kan ɗanwasan gaba na Real Madrid da Brazil Endrick, mai shekara 20, wanda ke nuna damuwa kan makomarsa a Bernabeu. (Teamtalk)
Manchester United da Tottenham da Galatasaray na hamayya kan ɗanwasan gaba na Crystal Palace Jean‑Philippe Mateta, mai shekara 29, amma Aston Villa ta fi nuna buƙatar ɗanwasan na Faransa bayan ta taya shi fam miliyan 20. (Caught Offside)
Ɗanwasan tsakiya na Sweden Hugo Larsson, mai shekara 22, na shirin barin Eintracht Frankfurt kuma Crystal Palace ke son ɗanwasan. (Sky Germany)
Valencia na tattaunawa domin ɗauko aron ɗanwasan tsakiya na Ingila Harvey Elliott, mai shekara 23 daga Liverpool. (Matteo Moretto)
Aston Villa ta amince ta biya fam miliyan 47 domin ɗauko ɗanwasan Paris St-Germain da Senegal Ibrahim Mbaye. (Mail)










