Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/8/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 29 ga watan Agustan 2026.

Taƙaitattu

  • An murƙushe yunƙurin sojoji na yin bore a Nijar - Gwamnati
  • 'Tinubu ya nemi kotu a Amurka ta hana fitar da takardun zarginsa da safarar ƙwaya'
  • Sojoji sun kashe ƴan ta'adda biyu tare da ƙwato makamai a Sokoto
  • An miƙa 'yan Najeriya biyu ga Amurka kan zargin damfarar intanet da ta yi sanadin mutuwar matashi
  • An miƙa 'yan Najeriya biyu ga Amurka kan zargin damfarar intanet da ta yi sanadin mutuwar matashi
  • An miƙa 'yan Najeriya biyu ga Amurka kan zargin damfarar intanet da ta yi sanadin mutuwar matashi
  • Muna buƙatar haɗin kan al'ummar Iran - Mojtaba Khamenei
  • Iran ta ce za ta kai hari kan dukkan wuraren Amurka idan yaƙi ya ci gaba
Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir
  • Kano
  • Seriki Abbas
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammed

  1. Firaministan Pakistan ya dakatar da ma'aikatan asibitin da gobara ta kashe jarirai 14

    Pakistan

    Asalin hoton, Reuters

    Firaiministan Pakistan Shehbaz Sharif, ya bayar da umarnin dakatar da manyan jami'an 8 na asibitin da jarirai 14 suka mutu sakamakon gobara a sashen kula da masu haihuwa.

    Matakin ya biyo bayan rahoton farko game da tashin gobarar ranar Laraba a CibiyarKula da Lafiya ta Pakistan da ke Islamabad, daya daga cikin manyan asibitocin gwamnati na kasar.

    An yi nasarar ceto jariri guda. Wata sanarwa daga ofishin Firaiminista ta bayyana cewa bincike ya gano rashin daukar matakan da suka dace da suka hada da ƙararrawa da sinadaran kashe gobara, har da rashin horo kan yadda ake kashe gobara.

  2. Gwamnatin Nijar ta ce komai ya lafa a ƙasar bayan boren soji

    Nijar

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin sojin Nijar ta ce ta sake karbe iko bayan yunkurin juyin mulki da wasu sojoji ƴan tawaye suka yi, wanda aka fara daga daren jiya zuwa yau.

    An ji ƙarar harbe-harbe da fashewar abubuwa a Yamai babban birnin ƙasar, a yankunan da suka haɗa da fadar shugaban ƙasa da kuma filin jirgin saman na ƙasa da ƙasa.

    Ma'aikatar tsaron ƙasar ta ce ƴan tawayen sun yi garkuwa da sojoji a wani sansanin sojin sama sannan sun buɗe wa wasu muhimman wurare wuta.

    Rahotanni sun ce wasu daga cikinsu sun fito daga cikin dakarun da suka fafata da mayaƙa masu ikirarin Jihadi.

    Har yanzu dai ba a bayyana jagoran yunkurin juyin mulkin ba.

  3. Isra'ila sun kai farmaki a ƙauyen Qusra na Falasɗinawa

    Isra'ilawa ƴan kama wuri-zauna sun sake kai hari kan ƙauyen Qusra na Falasɗinawa da ke yankin Yammacin Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye.

    Mazauna matsugunan sun ƙwace wani gida, duk da cewa akwai iyalan Falasdinawa a ciki.

    Jami'an tsaron Isra'ila sun fitar da su daga gidan, amma rahotanni sun ce sun ci gaba da kasancewa a wasu filaye da ke kusa da wurin.

    Babu wani rahoto da ya nuna cewa an kama wani mutum dangane da lamarin.

    A farkon wannan watan, mazauna matsugunan sun fara hana kai kayan abinci da sauran kayayyaki zuwa wasu gidaje a ƙauyen Qusra.

    Jakadan Amurka a Isra'ila, Mike Huckabee, ya bayyana mazauna matsugunan a matsayin 'yan ta'adda.

  4. Amurka ta shiga yarjejeniyar sarrafa ɗanyen man Venezuela

    Venezuela

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Amurka, tare da haɗin gwiwar wasu kamfanoni masu zaman kansu, sun kulla yarjejeniya da Venezuela wadda za ta bai wa Amurka ikon mallakar mafi rinjayen rijiyoyin man fetur da ke da gangar mai biliyan 65 a ƙasar.

    Mista Trump ya ce yarjejeniyar za ta ninka fiye da sau biyu yawan arzikin man fetur din Amurka, tare da taimakawa wajen rage farashin man fetur ga masu amfani da shi a ƙasar.

    Shugabar riƙon-ƙwarya ta Venezuela, Delcy Rodríguez, ta yi maraba da yarjejeniyar, tana mai cewa yarjejeniyar za ta taimaka wajen ƙara yawan haƙo man fetur a ƙasar da bunƙasa rijiyoyi 17 na kasar, tare da samar da kuɗaɗen harajin da ya haura dala biliyan 200.

    Sai dai masana sun ce har yanzu ba a bayyana ainihin dokar da ta ba da damar kulla wannan yarjejeniyar ba, haka kuma ba a fayyace yadda tsarin yarjejeniyar hayar hakar man zai kasance ba. break

  5. Kotu ta yanke wa tsohon shugaban Ecuador, Lenín Moreno, hukuncin daurin shekara biyar

    Kotu

    Asalin hoton, AFP

    Wata kotu a Ecuador ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar, Lenín Moreno, hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari bayan samun sa da laifin karɓar rashawa daga wani kamfanin ƙasar China da ke da alaƙa da aikin gina babbar tashar samar da wutar lantarki ta ruwa mafi girma a ƙasar.

    Wakilin BBC ya ce, mutumin mai shekara 73 a duniya, wanda ya halarci zaman sauraron hukuncin kotun, an same shi da laifin taimaka wa kamfanin China Sinohydro wajen samun kwangilar gina tashar wutar lantarki, a madadin karɓar kuɗaɗe. Za a yi masa daurin Talala ne na tsawon wadannan shekaru.

    Kazalika an kuma yanke wa matarsa da 'yarsa hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni talatin kowacce, haka ma 'yan uwansa maza biyu da kuma matan 'yan uwansa.

  6. Ba za mu miƙa wuya ba - Hezbollah

    Hezbollah

    Asalin hoton, Reuters

    Naim Qassem, babban sakataren ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon, ya sake yin watsi da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Lebanon da Isra'ila a ranar Juma'a, yana mai cewa ƙungiyar da Iran ke mara wa baya ba za ta "miƙa wuya" ba hakan nan.

    A cikin wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin na Al-Manar, Qassem ya ce: "Ba mu lamunta da yarjejeniyar tsarin ba, kuma muna neman a soke ta."

    Lebanon da Isra'ila sun shiga tattaunawa kai tsaye ƙarƙashin sasancin Amurka bayan yaƙin da ya fara ranar 2 ga Maris, lokacin da Hezbollah ta kai hari kan Isra'ila, wanda daga baya ya biyo bayan hare-hare masu yawa da kuma mamayar sojojin Isra'ila ta ƙasa a Lebanon, inda jami'an Lebanon sun ce fiye da mutum 4,300 ne suka mutu a yaƙin.

    A tattaunawar da aka yi a ƙarshen watan Yuni, ɓangarorin biyu sun cimma wata yarjejeniya, wadda ta tanadi kwance ɗamarar Hezbollah, janye sojojin Isra'ila daga kudancin Lebanon a hankali, da kuma tura sojojin Lebanon zuwa yankin.

    Sai dai Naim Qassem ya bayyana yarjejeniyar a matsayin "haramtacciya, wadda aka yi ba bisa ƙa'ia ba, kuma abin wulaƙanci kuma mai rusa ƴancin Lebanon."

    Ya kuma ce Hezbollah na adawa da kafa yankunan gwaji da kuma duk wata hanya ta sa ido ko tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar.

    Haka kuma, ya nuna goyon bayansa ga aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta watan Nuwamban 2024, wadda aka cimma domin kawo ƙarshen yaƙin da ya gabata tsakanin Hezbollah da Isra'ila.

  7. Shettima ya tafi Angola domin wakiltar Tinubu a taron AU

    ....

    Asalin hoton, Shettima/X

    Mataimakin Shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja zuwa Luanda babban birnin Angola, domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron shugabannin ƙasashen Tarayyar Afirka (AU) na musamman karo na 21.

    Sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, ya fitar ta ce taron zai mayar da hankali kan hanyoyin warware rikice-rikice da kuma bunƙasa zaman lafiya mai ɗorewa a nahiyar Afirka.

    Ana sa ran Shettima zai haɗu da sauran shugabannin Afirka domin tattauna kalubalen tsaro da hanyoyin hana tashe-tashen hankula da warware rikice-rikice.

    Hakazalika, zai gabatar da jawabin Shugaba Tinubu a taron, inda zai bayyana matsayar Najeriya kan batutuwan da za a tattauna tare da jaddada aniyar ƙasar na ci gaba da tallafa wa zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin nahiyar.

  8. 'Tinubu ya nemi kotu a Amurka ta hana fitar da takardun zarginsa da safarar ƙwaya'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi wata kotu a Amurka ta hana Ma’aikatar Shari’a ta Amurka (DOJ) da hukumomin FBI da DEA fitar da wasu takardunsa da ake dangantawa da zargin safarar miyagun ƙwayoyi da aka taɓa yi masa, a cewar lauyoyinsa.

    Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa Tinubu ya shigar da ƙorafi ne a wani shari’ar neman bayanai da wani ɗan gwagwarmayar neman gaskiya a Amurka, Aaron Greenspan, ya buɗe ƙarƙashin dokar ’Yancin Samun Bayanai (FOIA).

    Greenspan na neman a ba shi cikakken fayil ɗin FBI da sauran bayanan binciken da suka shafi Tinubu, ciki har da wasu bayanan da suka danganci shari’ar kwace kusan dala 460,000 a Amurka a shekarar 1993.

    Sai dai lauyoyin Tinubu sun ce fitar da waɗannan takardu na iya ƙeta haƙƙinsa na sirri, suna masu cewa ko da an taɓa bayyana wasu bayanai a baya, har yanzu yana da haƙƙin kare bayanan da ba a fitar da su ba.

    Tinubu dai ya sha musanta aikata wani laifi da ya shafi zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

  9. 'An koma haƙo man fetur a yankin Kurdistan na Iraq'

    ....

    Asalin hoton, AFP VIA GETTY

    Ministan Albarkatun Ƙasar Iraq, Kamal Mohammed, ya bayyana cewa an koma haƙo man fetur a yankin Kurdistan bayan hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da suka kai wa wasu filayen mai da cibiyoyin samar da shi hari.

    Ya ce kamfanonin mai sun koma aiki, kuma yawan man da ake haƙowa a yankin ya kai tsakanin ganga 220,000 zuwa 230,000 a rana.

    Ministan ya ce dukkan filayen mai sun koma aiki baya ga filin mai na Sarsang, wanda har yanzu ke fuskantar matsaloli sakamakon barnar da hare-haren jiragen sama marasa matuƙa suka yi masa.

    A watan Yulin 2025 ne kamfanin HKN Energy na Amurka, mai kula da filin mai na Sarsang, ya dakatar da aiki bayan wasu hare-hare da suka haddasa fashe-fashe a wurin..

  10. Sojoji sun kashe ƴan ta'adda biyu tare da ƙwato makamai a Sokoto

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation FANSAN YAMMA sun kashe ƴan ta'adda biyu tare da kwato bindigogi da babura uku a wani samame da suka kai a ƙaramar hukumar Rabah da ke Jihar Sokoto.

    A cewar rundunar, samamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu a safiyar ranar 28 ga Agusta 2026 cewa wasu ƴan ta'adda na jan ɗaruruwan shanun da suka sace ta yankin Maikujera.

    Daga nan ne sojojin suka yi gaggawar kai farmaki domin tare su.

    Yayin da sojojin ke kan hanyarsu ta zuwa wurin, sun ci karo da kwanton ɓaunar da ƴan ta'addan suka yi musu.

    Sai dai dakarun sun mayar da martani da ƙarfin wuta, inda anan ne suka kashe mutum biyu daga cikin maharan, yayin da sauran suka tsere zuwa cikin daji.

    Rundunar ta ce shanun da aka sace sun watse cikin dazuka yayin fafatawar, amma ana ci gaba da haɗin gwiwa da ƴan sa-kai domin gano su.

  11. An murƙushe yunƙurin sojoji na yin bore a Nijar - Gwamnati

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yi bayani kan harbe-harben da aka kwashe tsawon dare ana ji har zuwa wayeywar garin Asabar a Yamai, babban birnin kasar inda ta ce ta murƙushe yunƙurin bore da wasu sojoji suka yi.

    Lamarin ya tayar da hankulan mazauna birnin tare da jawo hankalin ƙasashen duniya.

    A cikin sanarwar da ya karanta ta gidan talabijin na gwamnati, ministan tsaron Nijar, Janar Salifou Modi, ya ce kimanin ƙarfe 12:20 na dare wani rukuni na sojoji sun kutsa cikin sansanin soji na 101 da ke kusa da filin jirgin saman Diori Hamani a Yamai, inda suka yi garkuwa da wasu daga cikin abokan aikinsu.

    Sai dai ya ce dakarun ƙasar sun yi gaggawar mayar da martani, inda suka dakile yunƙurin tare da dawo da doka da oda.

  12. An miƙa ’yan Najeriya biyu ga Amurka kan zargin damfarar intanet da ta yi sanadin mutuwar matashi

    ...

    Asalin hoton, FBI Director Kash Patel

    Wasu ’yan Najeriya biyu sun isa Amurka domin fuskantar shari’a bayan an miƙa su daga Najeriya kan zargin hannu a damfarar intanet ta hanyar barazanar yaɗa hotunan tsiraici, lamarin da ake zargin yayi sanadin mutuwar wani matashi ɗan Amurka.

    Hukumar EFCC ta bayyana sunayensu da Mudashiru Afeez Olawale da Adebola Festus Adekunle, tana mai cewa an miƙa su ne ga hukumomin Amurka bayan binciken da FBI ta gudanar kan zargin cin zarafin yara ta intanet.

    A cewar EFCC, ana zargin mutanen biyu da yi wa yara maza masu shekaru tsakanin 13 zuwa 17 barazana da hotuna na batsa domin karɓar kuɗi.

    Daraktan FBI, Kash Patel, ya ce ɗaya daga cikin waɗannan zarge-zargen ya yi sanadin mutuwar wani yaro.

    Hukumar ta ƙara da cewa an kama mutanen biyu a Najeriya a shekara ta 2023.

    EFCC ta ce miƙa waɗannan mutanen ga Amurka wani ɓangare ne na haɗin gwiwar da ke tsakanin Najeriya da Amurka wajen yaƙi da laifukan intanet da kuma cin zarafin yara.

    Sai dai har yanzu mutanen biyu ba su mayar da martani kan zarge-zargen ba, kuma ba a tabbatar da su a kotu ba.

  13. Rediyo da talabijin na Nijar sun koma aiki bayan katsewa na dan lokaci

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Mazauna birnin Niamey sun shaida wa BBC cewa gidajen rediyo da talabijin na gwamnatin Nijar sun koma bakin aiki bayan katsewar dan lokaci.

    Rahotanni sun ce kafafen sun koma aiki da misalin karfe 10:30 na safe agogon ƙasar, bayan sun katse shirye-shiryensu da misalin karfe 9:00 na safe.

    Katsewar ta zo ne a daidai lokacin da aka ruwaito karar harbe-harbe da fashe-fashe a wasu sassan Niamey, ciki har da yankin filin jirgin sama na Diori Hamani, wani sansanin soja da kuma kusa da fadar shugaban ƙasa.

    Mahukuntan Nijar sun yi kira ga jama'a da su kwantar da hankulansu, amma har yanzu ba su yi karin bayani kan abin da ya faru ba.

  14. Iran ta musanta iƙirarin Trump kan buɗe mashigar Hormuz

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta musanta kalaman shugaban Amurka Donald Trump cewa mashigar Hormuz tana a buɗe, suna masu cewa har yanzu ba a bar jiragen ruwa su ratsa ba tare da amincewar hukumomin Iran ba.

    Rundunar ta bayyana kalaman jami'an Amurka a matsayin "ƙarya ƙarara", tana mai cewa an yi su ne domin tasiri kan farashin man fetur da kuma ɓoye abin da ta kira gazawar Amurka.

    IRGC ta kuma yi iƙirarin cewa har yanzu ita ce ke da cikakken iko kan mashigar Hormuz, tare da jaddada cewa za ta ci gaba da aiwatar da wannan mataki har sai an kawo ƙarshen ayyukan sojin Amurka kan Iran da kuma cika sharudan da Tehran ke nema.

  15. Gwamnatin Kwara ta haɗa mutum 146 da aka sace a Woro da iyalansu

    ....

    Asalin hoton, AbdulRahman AbdulRazaq/X

    Gwamnatin Jihar Kwara ta sanar da cewa ta haɗa mutum 146 da aka sace daga ƙauyen Woro da iyalansu bayan sun shafe kwanaki 21 a cibiyar kula da lafiyar kwakwalwa da farfaɗo da su daga abin da suka fuskanta.

    An kai hari ƙauyen Woro ne a ranar 3 ga Fabrairu, inda aka yi garkuwa da mutum 146, kafin daga bisani aka kuɓutar da su a ranar 5 ga Agusta.

    Gwamnatin jihar ta kuma ba waɗanda aka kuɓutar tallafin kuɗi, inda manya suka samu naira miliyan ɗaya kowannensu, matasa naira dubu 500,000, yayin da yara suka samu naira dubu 200,000 domin taimaka musu su fara rayuwa ta sabo.

    Shugaban ƙaramar hukumar Kaiama, Abubakar Abdullahi Danladi, ya yaba wa Shugaba Tinubu da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan rawar da suka taka wajen ceto da kuma kula da waɗanda aka sace.

    Sai dai shugaban kwamitin da ke hulɗa tsakanin gwamnati da al'ummar Woro, Ahmed Ibn Ahmed, ya ce har yanzu mutum 13 na hannun masu garkuwa da mutane, tare da kira ga gwamnati ta ƙara ƙoƙari domin ceto su.

  16. Muna buƙatar haɗin kan al'ummar Iran - Mojtaba Khamenei

    ....

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Jagoran addinin Iran Mojtaba Khamenei, a wani saƙo da aka danganta da shi, ya jaddada goyon baya ga gwamnatin Shugaban kasar, Massoud Pezeshkian tare da kira ga haɗin kan al'umma da kauce wa duk wani abu da zai haddasa rarrabuwar kawuna.

    Bayan saƙon ne kuma wasu manyan jami'an Iran suka sake jaddada kira da a ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

    Mohsen Rezaei, sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa, ya ce haɗin kan al'umma na daga cikin muhimman ginshiƙan ƙarfi da tsaron ƙasa.

    Shi ma shugaban majalisar dokoki, Mohammad Baqer Qalibaf, ya ce ya kamata jami'ai su guji duk wani abu da zai haifar da sabani a tsakanin al'umma, yana mai cewa duk wani aiki da zai raunana haɗin kai bai dace ba.

    Ministan Al'adu, Abbas Salehi, ya ce saƙon ya nuna cikakken goyon baya ga shugaban ƙasar, tare da rage damar masu son haddasa rarrabuwar kawuna ta siyasa, al'adu ko zamantakewa.

  17. Iran ta ce za ta kai hari kan dukkan wuraren Amurka idan yaƙi ya ci gaba

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta yi gargaɗin cewa za ta kai hare-hare kan dukkan sansanonin soja da sauran wuraren Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya idan yaƙin da ake yi ya ci gaba.

    Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya ce Tehran ta riga ta sanar da ƙasashen yankin cewa duk wani hari da Amurka ta kai wa Iran zai fuskanci martani kai tsaye kan muradun Amurka a yankin.

    Ya kuma bayyana hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai Iran ba bisa ka'ida bane, yayin da ya ce Iran za ta mayar da martani ne domin kare kanta.

    Araqchi ya ce makamai masu linzamin Iran sun nuna ƙarfinsu a yaƙin baya-bayan nan, yana mai iƙirarin cewa Amurka da Isra'ila sun kasa dakile su yadda ya kamata.

    Haka kuma ya ce Iran na son inganta dangantaka da ƙasashen Musulmi da maƙwabtanta, ciki har da Masar da Lebanon.

  18. Amurka ta samu iko da fiye da rabin man fetur ɗin Venezuela - Trump

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin cewa Amurka ta samu iko da fiye da rabin arzikin man fetur na Venezuela, yana mai cewa hakan ya ƙarfafa tasirin Washington a fannin makamashi a yankin.

    Trump ya bayyana haka ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan manufofin makamashi da dangantakar Amurka da ƙasashen Latin Amurka.

    Sai dai bai yi cikakken bayani kan yadda Amurka ta samu wannan iko ba.

    Venezuela na ɗaya daga cikin kasashen masu manyan arzikin man fetur a duniya, kuma albarkatun makamashinta na ci gaba da kasancewa muhimmin batu a siyasa da tattalin arzikin duniya.

  19. Iran ta ce tana da wadataccen mai da zai samar mata kuɗaɗen kasafi

    ...

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Iran ta ce tana da isasshen man fetur da za ta sayar domin samar da kuɗaɗen da ake buƙata a kasafin kuɗinta duk da toshe tasoshin ruwanta da Amurka ta yi kamar yadda kamfanin dillanacin labaran Fars ya ruwaito.

    Fars ya ce ma’aikatar man tetur ta ƙasar ta ce kuɗaɗen da aka samu daga man fetur a watanni huɗun farko na shekarar nan sun kai kashi 99 cikin 100 na abin da aka tsara a kasafin kuɗi.

    Haka kuma, ma’aikatar ta ce ta tura dala biliyan 7.5 da aka samu daga sayar da man fetur zuwa Babban Bankin Iran a cikin watanni huɗun farko na shekarar, kuma ana sa ran kuɗaɗen za su taimaka wajen biyan buƙatun kuɗaɗen musayar ƙasashen waje na gwamnati daga watan Afrilu zuwa Janairu.

  20. Assalamu alaikum!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Asabar daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce za ta kasance da ku daga yanzu zuwa yamma.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.