Me ya sa yaƙin Iran ya zama matsala ga Trump a zaɓe?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Khashayar Junidi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
- Aiko rahoto daga, Washington
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Wata shida da fara yaƙi, gwamnatin Donald Trump na fuskantar wata babbar matsala da ta jefa cikin tsaka mai wuya: Ko dai janyewa daga yaƙin na iya nufin amincewa ko kuma miƙa wuya.
A ɗaya gefe kuma ci gaba da yaƙin zai iya ƙara yawan asarar rayuka, kuɗaɗen da ake kashewa, da kuma rage tarin makaman Amurka, ba tare da tabbacin samun wata gagarumar nasara a siyasance ba.
Gidan talabijin na ABC a Amurka ya bayyana a cikin wani rahoton nazari cewa, tun da farko, Donald Trump ya yi tunanin cewa hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai a faɗin wurare, tare da kashe wasu shugabanni, kwamandoji da lalata wasu muhimman ababen more rayuwa, za su tilasta wa Iran ta amince da sharuɗɗan Washington cikin ƴan makonni.
Sai dai Iran ta ci gaba da riƙe wasu daga cikin ƙarfin makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa, kuma ta samu damar kai wa jiragen ruwan Amurka, sansanonin soji da wuraren ajiya da jigilar kayayyaki hari.
Raunin sansanonin Amurka da cibiyoyin jigilar kayayyaki a yankin, tare da saurin amfani da makamai masu linzami masu kariya da kuma makamai masu linzami masu cin dogon zango, ya haifar da damuwa game da shirin Washington na tunkarar yiwuwar wasu rikice-rikice a nan gaba.
A cewar ABC, Amurka ta yi wa sojojin Iran mummunar asara, amma har yanzu ba ta iya mayar da nasarorin soja zuwa wata nasara ta siyasa ko kuma samar da mafita mai ɗorewa ba.
"Zaɓen majalisar dokokin Amurka da yaƙin Iran"

Asalin hoton, Getty Images
Yaƙin da ake yi da Iran ya zama babban batu a zaɓen tsakiyar wa'adi na majalisar dokokin Amurka, a cewar jaridar Washington Post. Ƙarin farashin man fetur, taki, sufuri da kayan masarufi ya sa masu jefa ƙuri'a da dama ke ganin cewa yaƙin yana da alaƙa kai tsaye da tsadar rayuwa.
Kimanin kashi biyu bisa uku na manyan ƴan Amurka sun yi imanin cewa bai kamata a fara yaƙin ba, a cewar wani sabon binciken jin ra'ayin jama'a na Associated Press. Wannan rukunin ya ƙunshi mafi yawan ƴan Democrat da waɗanda ba su da jam'iyya da kuma sama da kashi ɗaya bisa uku na ƴan Republican. Tsawaitar yaƙin kuma ta saɓa da alƙawarin kamfen ɗin Trump na kiyaye Amurka daga shiga rikice-rikicen ƙasashen waje.
Wasu ƴan Republican a majalisa ma sun nuna damuwa game da kuɗin da ake kashewa da tsawon lokacin yaƙin, duk da cewa shugabannin jam'iyyar har yanzu suna adawa da ƙoƙarin taƙaita ikon shugaban ƙasa na yin yaƙi.
Washington Post ta yi nuni da cewa akwai wasu gundumomin zaɓe masu tsananin fafatawa a Pennsylvania, California, Iowa da wasu jihohi, inda tashin farashin man fetur zai iya sauya sakamakon zaɓen.
Wasu masu jefa ƙuri'a sun ce albashinsu bai ƙaru ba, yayin da farashin fetur, haya da kayan abinci ya ƙaru. Ƴan takarar Democrat na ƙoƙarin ɗora alhakin wannan yanayi kan Trump da ƴan Republican.
Ƴan Republican a majalisa, waɗanda da farko suka goyi bayan matakin soja, suna ƙara nuna damuwa game da tsadar yaƙin da kuma yadda yake ɗaukar lokaci mai tsawo. Sai dai shugabannin jam'iyyar suna ci gaba da adawa da ƙoƙarin taƙaita ikon Trump na yin yaƙi ko kuma rage kuɗaɗen da ake warewa.
Rahoton ya kuma jaddada cewa ba dukkan magoya bayan Trump ne suka juya masa baya ba. Wasu har yanzu sun yi imanin cewa yaƙin ya zama dole domin hana Iran mallakar makaman nukiliya.
Washington Post ta yi hasashen cewa yaƙin zai yi tasiri a gundumomin zaɓe da ake fafatawa sosai tsakanin ƴan Democrat da Republican, amma ba lallai ne ya sauya ma'aunin zaɓen gaba ɗaya ya karkata zuwa ga ƴan Democrat ba.
Trump da batun farfaɗo da yarjejeniyar da wa'adinta ya ƙare
A cewar Mujallar Wall Street , ƙoƙarin Qatar, Oman da Pakistan na farfaɗo da tattaunawar Iran da Amurka ya fuskanci wata babbar matsala.
A saboda haka, Donald Trump ba ya son komawa ga tattaunawar fahimtar juna da aka cimma a watan Yuni, kuma ya fi son jira domin ganin tasirin matsin tattalin arziki da ake yi wa Tehran.
An tsara yarjejeniyar ne domin a buɗe mashigar Hormuz, a fara tattaunawar nukiliya, sannan a ɗauki matakai zuwa ga kawo ƙarshen yaƙin. A madadin haka, Washington ta shirya sassauta wasu daga cikin takunkuman da ta ƙaƙaba wa Iran tare da taimakawa wajen bai wa Iran damar samun wasu kadarorinta da aka ƙwace.
Sai dai sake komawar hare-hare kan jiragen ruwa ya sa Amurka ta ajiye yarjejeniyar a gefe, tare da ƙara tsaurara shingen ruwan teku da kuma yaƙin "ware Iran daga harkokin tattalin arziki."
A cewar Mujallar Wall Street, Washington na fatan cewa ta hanyar ƙara matsin tattalin arziki, Tehran za ta koma teburin tattaunawa cikin wani matsayi mafi rauni.
CBS, ta ambato gwamnatocin Qatar, Oman da Pakistan, inda ta rubuta cewa rashin tabbas na tsaro a mashigar Hormuz na ci gaba da sa fitar da man fetur daga yankin Tekun Fasha ta kasance ƙasa da yadda take kafin yaƙin.
A halin da ake ciki, duk da cewa Shugaban Iran Masoud Pezzekian ya yi magana kan yiwuwar warware saɓanin da ke tsakanin ɓangarorin ta hanyar tattaunawa, Donald Trump ya ce babu wata tattaunawa da ake yi da Iran.
A cewar wannan gidan talabijin, rashin samun matsaya a fagen siyasa a halin yanzu ya ƙara haɗarin sake komawa yaƙi.

Asalin hoton, Getty Images
"Kasuwancin Iran a Dubai na ci gaba"
Mujallar Wall Street Journal ta kuma ruwaito a wani rahoto cewa harkokin tattalin arziki da suka shafi Iran na ci gaba da gudana a Dubai.
A cewar jaridar, duk da sanar da fara wani "aikin ware Iran daga harkokin tattalin arziki", harkokin kasuwanci da na banki da suka shafi Iran suna ci gaba da gudana a fili a Dubai. Har ma reshen Bankin Ƙasa na Iran, wanda Washington ta nemi a rufe, har yanzu yana ci gaba da ba abokan ciniki hidima.
An ƙiyasta cewa darajar cinikayya tsakanin Iran da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa kafin yaƙin ta kai dubban miliyoyin daloli, kuma wani muhimmin ɓangare na jarin Dubai da harkokin kasuwancinta yana da alaƙa da ƴan kasuwar Iran.
Ba kamar Abu Dhabi ba, Dubai ba ta da ɗimbin kuɗaɗen shiga daga man fetur. Tattalin arzikinta ya fi dogaro da kasuwanci, yawon buɗe ido da kuma hannun jarin ƙasashen waje. Yanke hulɗa da Iran cikin gaggawa na iya haifar da asara ga Dubai.
Wasu ƴan kasuwar Iran sun shirya kansu don yiwuwar rufe hanyoyin kasuwanci na hukuma, amma wannan rahoton ya nuna cewa kawo yanzu ba a buƙaci a mayar da harkokin kasuwanci da yawa zuwa hanyoyin da ba na hukuma ba.
Wall Street Journal ta rubuta cewa wannan yanayin yana nuna babban ƙalubalen dabarun Donald Trump: sanar da takunkumi ya fi sauƙi fiye da aiwatar da su gaba ɗaya.
Saboda haka, nasarar yaƙin tattalin arzikin Amurka da Iran ta dogara ne kan ainihin haɗin gwiwar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, China, India, Turkiyya da sauran ƙasashen da ke hulɗa da Iran.
Idan Washington na son aiwatar da barazanar da ta yi gaba ɗaya, za ta iya tilastawa ta ɗauki mataki kan wasu daga cikin ƙawayenta da muhimman abokan hulɗarta na tattalin arziki. Irin wannan mataki na iya haifar da sabbin tashe-tashen hankula a dangantakar Amurka da sauran ƙasashe.






