Yadda za ku kula da cibiyar sabbin jarirai kafin ta faɗi

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ana yanke cibiyar jariri da zarar an haife shi, domin ba ta da sauran amfani.

Domin da ta daina samun jini sai ta fara bushewa ta yi tauri, a cewar shafin intanet na gidauniyar NHS reshen asibitin jami'ar Milton Kyenes.

Sai dai kafin ta kai ga faɗuwa, akwai wasu shawarwari kan yadda ya kamata a kula da cibiyar sabon jariri.

Abu mafi matuƙar muhimmanci shi ne wanke hannu a kodayaushe a yayin kulawa da jariri.

Haka kuma kada a dinga taɓa cibiyar da hannu domin kauce wa sanya wa jariri ƙwayoyin cuta, a kuma kiyaye sanya wa jariri matsattsun kaya domin cibiyar ta dinga shan iska.

Haka zalika asibitin ya bayar da shawarar kada a cire abin da aka maƙale cibiyar da shi saboda nauyinsa na taimaka wa wajen faɗuwar cibiyar jariri.

Kana kuma za a iya yi wa jariri wanka da ruwa, kuma a goge cibiyar idan har fitsari ko bayan gida ya taɓa ta. Shima a nan a yi amfani da ruwa kawai.

Shafin ya kuma bayyana cewa cibin jariri na faɗuwa ne daga kwana biyar zuwa 15 bayan haihuwa.

Amma kwanakin za su iya zarta hakan idan an baiwa jariri maganin kashe ƙwayoyin cuta ko kuma idan cibiyar ta kamu da ƙwayoyin cuta.

Asibitin ya kara da cewa, idan cibiyar ta zo faɗuwa ta kan bar wani ruwa mai danko-danko, hakan ba abin damuwa ba ne, kuma idan ta fadi ma ta kan fitar da irin wannan ruwan na ƴan kwanaki kafin ta bushe.

Abin da ya dace shi ne a ci gaba da sa ido a kanta har ta bushe ta juye.

Za a iya saka wani abu don cibiyar ta faɗi?

Wasu iyaye na shiga fargaba idan aka ɗauki wani lokaci cibin jariri bai faɗi ba, ko kafin suna, inda su kan sanya abubuwa na gargajiya daban-daban domin ganin ta faɗi da wuri.

A jamhuriyyar Nijar wasu iyaye sun bayyana cewa suna amfani da wasu abubuwa kamar gishiri, balma (mai kama da kanwa), turare mara zafi, suna gasawa, farin kwalli, rammaji (Magi), ta hanyar goyo, man goge baki don sa cibin ya faɗi.

Wata ƙwararriyar likitar yara da ke aiki da asibitin gwamnatin tarayya na Najeriya da ke Jabi, Dokta Naja'atu Mohammed ta ce waɗannan abubuwan da ake zubawa a kan cibiya ba sa haifar da komai sai matsala.

"Cibiya jijiyoyi ne suke bi daga mabiyiyya su kawo abinci ga yaro (lokacin yana ciki) to ba a bari ta bushe ba, duk abin da aka ɗauka aka zuba mata mai ɗauke da ƙwayoyin cuta, kai tsaye zai shiga jikin jariri"

Ta ƙara da cewa "har cutar sanƙarau yana iya janyo wa jariri, wanda zai lalata masa ƙwaƙwalwarsa gaba ɗaya'', inji ta.

''Saka wasu abubuwa a kan cibiya na haifar da cututtuka daban-daban waɗanda ƙwayoyin cuta ke haddasawa. "

Illar sakawa jarirai abu a kan cibiyarsa

Likitar ta ce suna ganin abubuwan tashin hankali a kan jariran da ake zubawa abubuwa a cibiya, kuma ƙwayoyin cuta ne ke kashe jarirai masu yawa a Najeriya.

Inda ta ƙara da cewa akwai maganin da ake amfani da shi sau ɗaya, a shafawa yaro a cibiya idan an yi masa wanka.

Wasu alamomin da za a gane idan cibiyar jariri ta kamu da ƙwayoyin cuta sun haɗa da:

  • Ƙasan cibiyar daidai kan ciki zai sauya launi ya yi ja
  • Wurin zai ɗan kumbura kuma ya yi taushi
  • Cibiya na jini
  • Tana fitar da wani ruwa mai launin kore ko ruwan ɗorawa
  • Kuma idan jaririn baya karɓar mama ko abinci kamar yadda ya kamata
  • Jariri bashi da kuzari
  • Jariri na zazzaɓi.

Da zarar an ga wani daga cikin waɗannan alamomi sai a je asibiti don ɗaukar matakan da suka dace.