Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya kamata ku sani kan zaɓen gwamnan jihar Ekiti na yau
A yau ne ake gudanar zaɓen gwamnan jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya, domin zaɓar mutumin da zai jagorancin jihar nan da shekara huɗu.
Mutum fiye da miliyan daya ne suka yi rajistar zaɓe domin kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen na yau, kamar yadda INE ta bayyana.
Zaɓukan gwamna a Najeriya kan ɗauki hankalin ƴanƙasar, la'akari da irin muhimmancin kujerar a siyasar ƙasar.
Gwamna matsayi ne mai matuƙar tasiri a siyasar Najeriya, wanda shi ne ke juya duka al'amuran jihar da yake jagoranta.
Ekiti ta kasance ɗaya daga cikin jihohin Najeriya takwas da ake gudanar da zaɓukansu daban da lokacin da ake gudanar da zaɓen.
Wace ce jihar Ekiti?
An ƙirƙiri jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya a ranar 1 ga watan Oktoban 1996 daga tsohuwar jihar Ondo zamanin mulkin tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Sani Abacha.
Jihar na kan iyakar yankin kudu maso yammacin Najeriya da kuma yankin Arewa ta tsakiyar ƙasar, inda ta yi iyaka da jihohin Ondo da Osun da Kwara da kuma jihar Kogi
Ekiti na da ƙananan hukumomi 16, da ƴanmajalisar dokokin jiha 26.
Ekiti Kamar kowace jiha a Najeriya, Ekiti na da sanatoci uku, sai kuma ƴanmajalisar wakilai na tarayya 6.
A cewar alƙaluman hukumar ƙididdiga ta Najeriya, jihar na da yawan jama'a fiye da miliyan uku.
Harshen Yarabanci shi ne aka fi magana da shi a jihar, sai kuma Turanci.
Jiha ce da take da masu ilimin boko da yawa, kusan a iya cewa takan kan gaba a jerin jihohin ƙasar da suka fi yawan masu matsayin Farfesa a Najeriya.
Me ya sa ake zaɓen jihar daban da sauran jihohi?
Tarihin ficewar jihar daga lokacin da aka saba gudanar da zaɓukan jihohin ƙasar ya samo asali ne daga zaɓen 2007.
A dokar Najeriya gwamna na da wa'adin shekara huɗu daga ranar da aka rantsar da shi.
A zaɓen 2007, hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana Segun Oni na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara, aka kuma rantsar shi ya fara mulki.
To amma sai abokin takararsa na jam'iyyar ACN mai hamayya a lokacin, Kayode Fayemi ya garzaya kotu domin ƙalubalantar nasarar mista Oni.
Bayan da aka ɗauki dogon lokaci ana shari'a, sai kotun ɗaukaka ƙara da ke birnin Ilorin ta rushe nasarar Segun Oni a ranar 15 ga watan Oktoban 2010 watanni kafin zaɓen 2011, sannan ta tabbatar da Kayode Fayemi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen na 2007.
Bayan hukuncin kotun da kwana ɗaya aka rantsar da Fayemi a matsayin sabon gwamnan jihar.
Don haka bisa doka wa'adin Fayemi ya fara ne daga 2010 maimakon 2007 da aka yi zaɓen.
Tun daga lokacin ne kuma lokacin zaɓen jihar ya sauya daga na sauran jihohin ƙasar.
Su wane ne ke takara a zaɓen?
Mutum 11 ne ke fafatawa a zaɓen ciki har da gwamna mai ci Biodun Oyebanji na jam'iyyar APC.
Hukumar zaɓen ƙasar (INEC) ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar gwamnan jihar gabanin zaɓen.
INEC ta fara fitar da sunayen ƴan takara 12, amma daga baya ɗan takarar jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) Joseph Anifowose ya janye tare da mara wa gwamna Biodun Oyebanji baya.
Fitattun ƴantakara
Sai dai masu bibiyar lamuran siyasar jihar na ganin takarar za ta fi zafi ne tsakanin ƴantakara huɗu da suka haɗa da:
Biodun Oyebanji - APC
Gwamnan jihar mai ci, Biodun Abayomi Oyebanji na jam'iyyar APC. An haife shi a shekarar 1967 a yankin Ikogosi Ekiti.
A shekarar 2022 aka fara zaɓensa a mastayin gwamnan jihar ƙarƙashin APC, don haka a yanzu yana neman wa'adi na biyu ne.
Kafin nan shi ne shugaban ma'aikata a ƙarƙashin tsohon gwamna Kayode Fayemi. Haka kuma ya riƙe wasu sauran muƙaman siyasa a gwamnatin jihar.
Oluwadare Bejide - ADC
Oluwadare Bejide shi ne ɗan takarar jamm'iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaɓen.
An haife shi ne a watan Agusta 1959 a yankin mazaɓar Ekiti ta kudu.
Ya riƙe muƙamin sakataren gwamnatin jihar Ekiti daga 2007 zuwa 2010.
Ya yi takarar kujerun siyasa da dama amma bai taɓa yin nasara ba.
Oyebanji Olajuyin - LP
Oyebanji Olajuyin ne ɗan takarar a jam'iyyar mai wadda ke cikin masu hamayya.
Mista Olajuyin likita ne, malami kuma ɗan siyasa daga yankin Ikere Ekiti.
Ya kasance farfesa a aikin tiyatar kunne da makogwaro, kuma mai bincike a fannin ilimin likitancin sassan jiki a asibitin koyarwa na jami'ar Jihar Ekiti da ke birnin Ado - Ekiti.
Oluwole Oluyede - PDP
Oluwole Oluyede ne ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen gwamna na jihar Ekiti.
An haife shi a watan Yuni 1964 a birnin Ado-Ekiti.
Oluyede ya yi takarar gwamna a zaɓen 2022 ƙarƙashin jami'yyar ADC, amma bai yi nasara ba.
Wane shiri INEC da jami'an tsaro suka yi?
Tuni dai hukumar zaɓen ƙasar ta ce ta kammala shirye-shirye domin gudanar da zaɓukan cikin lumana.
Cikin wata hira da BBC, kakakin hukumar zaɓen, Hajiya Zainab Aminu ta ce tuni hukumar ta kammala shirye-shiryenta domin gudanar da zaɓen.
''Tuni aka rarraba kayyaki masu muhimmanci zuwa ƙananan hukumomi, waɗanda su kuma za su rabar da su zuwa rumfunan zaɓe daban-daban'', kamar yadda ta yi ƙarin haske.
A nata ɓangare rundunar yansandan ƙasar ta ce ta kammala shirinta domin tunkarar zaɓen na yau.
Kakakin rundunar yansanda ta ƙasar, DCP Anthony Placid, ya jaddada cewa tuni aka tura ƙwararrun jami'ai domin bayar da tsaro a lokacin zaɓen na yau.
Ya ce jami'an tsaron za su bayar da tsaro a rumfunan zaɓe da cibiyoyin tattara sakamako na faɗin jihar.