An fara jarjejeniyar zaman lafiya ta dogon zango tsakanin Iran da Amurka
An gudanar da kashin farko na tattaunawar yarjejeniyar zaman lafiya mai dogon zango tsakanin Amurka da Iran.
Yayin da ya bayyana zaman da na tarihi, mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya ce an samu gagarumin ci gaba a tattaunawar.
To amma kafofin yaɗa labaran Iran na bayar da rahoton cewa wakilan ƙasar sun ƙi wallafa hoton ganawar da aka kwashe mintuna 80 ana yi.
Haka kuma bayanai sun ce wakilan na Iran sun fusata da sabon barazanar Trump na yi wa Iran ruwan bama-bama idan ta kasa dakatar da mayaƙan Hezbollah da ke goyon baya a Lebanon.
Babban mai shiga tsakani na ƙasar, Mohammad Bagher Ghalibaf ya gargaɗi Amurka ta shiga taitayinta.
Rahotonni na cewa Tehran ta ƙi yarda a tattauna batun nukiliyarta har sa Isra'ila ta dakatar da hare-harenta a Lebanon.