Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu 14 da ke ƙunshe a yarjejeniyar da Iran da Amurka suka saka wa hannu
Da yammacin ranar Laraba ne shugaban Amurka, Donald Trump ya rattaɓa hannu kan yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran da za ta kawo ƙarshen yaƙi tsakanin ƙasashen biyu.
Donald Trump ya sanya hannu a kan yarjejeniyar ne a Faransa.
Shi ma shugaban Iran, Masoud Pezeshkian ya saka hannu a kan yarjejeniyar ta hanyar intanet.
Shugabannin biyu sun saka hannu ne a kan yarjejeniyar ne bayan kakakin majalisar dokokin Iran, Mohamed Bagher Ghalibaf da mataimakin shugaban Amurka, JD Vance duka sun sanya hannu a kan yarjejeniyar ta intanet a ranar Lahadi, kamar yadda Fadar White House ta sanar.
Abu 14 da ke ƙunshe a yarjejeniyar
1. Dakatar da yaƙi na yanzu da dundundun a dukkan ɓangarori ciki har da Lebanon.
2. Amurka da Iran "za su martaba ƴancin cin gashin junansu sannan kuma su kame daga shiga sha'anin cikin gidan juna."
3. Sun "amince da tattaunawa da kuma cimma yarjejeniyar ƙarshe a kwanaki 60 masu zuwa, da za a iya ƙarawa bisa amincewar juna"
4. Ba tare da ɓata lokaci ba Amurka za ta "fara cire shingen sojin ruwa da ta saka a tashoshin ruwa na Iran...sannan kuma za ta kawo ƙarshen shingen baki ɗayansa a cikin kwanaki 30."
5. A mashigar Hormuz, Iran "za ta fitar da tsarin da zai tabbatar da shigi da ficin jiragen ruwa ba tare da saka musu haraji ba, a cikin kwanaki 60."
6. Amurka ta sha alwashin cewa "tare da ƙasashen yankin ƙawayenta za su kafa wani tsarin sake gina da haɓaka tattalin arziƙin ƙasar Iran da kuɗi dala biliyan 300."
7. Amurka za ta "cire dukkannin takunkuman da aka ƙaƙaba wa" Iran.
8. Iran "ta tabbatar da cewa ba za ta samar da makamin nukiliya ba", amma za a tattauna sauran batutuwan da suka jiɓanci hakan a nan gaba. Dukkannin "ɓangarorin sun amince da tattauna batun inganta makamashin nukilya da sauran batutuwa masu alaƙa da buƙatar da Iran take da ita na makamashin nukiliyar"
9. Kafin kammala yarjejeniyar, Amurka da Iran " sun amince da su tsaya a inda ake"
10. Bayan rattaɓa hannu, Baitilmalin Amurka zai "yi wa Iran sassauci dangane da fitar da manta da dangoginsa, kafin ɗage takunkuman da aka ƙaƙaba mata baki ɗaya.
11. Amurka ta sha alwashin "ta sakar wa Iran kuɗaɗenta da ta sanya wa takunkumi"
12. "Za a kafa wani tsari da zai rinƙa saka idanu wajen zartar da" wannan yarjejeniyar.
13. Bayan rattaɓa hannu, da kuma zartar da yarjejeniyoyi masu lamba 1 da 4 da 5 da 10 da 11, Amurka da Iran "za su fara tattaunawa dangane da sauran yarjejeniyoyin da ke ƙunshe" a kundin.
14. "Yarjejeniyar ƙarshe za ta zama wajibi a kan dukkan ɓangarorin ta hanyar amfani da dokokin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya".
Ko Iran ta yi nasara a yarjejeniyar da ta ƙulla da Amurka?
Ga iyalai da yawa, tambayar ba ita ce ko yarjejeniyar ta yi kama da nasara ba, amma ko ta rage farashin kayayyaki kuma ko ta rage fargabar sake ɓarkewar yaƙin.
Mataimakin shugaban ƙasar Amurka JD Vance ya ce Iran ba za ta karɓi kuɗaɗen Amurkawa masu biyan haraji ba amma za ta iya samun damar samun biliyoyin daloli idan ta cika alƙawuran da ta ɗauka kuma aka sassauta mata takunkumai.
Hakan ya bai wa Tehran damar gabatar da yarjejeniyar a matsayin hanyar sa samun hannun jari da sake gina ta maimakon dogaro da Amurka.
Duk da haka, haɗarin a bayyane yake. Ba a fitar da cikakkun bayanai kan yarjejeniyar ba, kuma ana sa ran za a fara tattaunawa a ƙasar Switzerland ranar Juma'a.
Batutuwan da suka fi ɗaukar hankali da suka haɗa da makomar sinadarin Uranium da Iran ke da shi, da matakin inganta sinadarin da aka amince da shi, da sassauta takunkumai, da Hormuz da kuma Labanon, za su kasance kan gaba tattaunawar.
Akwai kuma rashin tabbas game da Isra'ila. Firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu ya yi watsi da rahotannin da ke cewa Isra'ila za ta janye daga kudancin Lebanon, yana mai cewa sojojin Isra'ila za su ci gaba da zama a Labanon na tsawon lokacin da ya dace.
Shi kuwa Donald Trump, ya fito fili ya soki lamirin Isra'ila a Lebanon, yana mai cewa an kashe mutane da yawa. Ya kuma ce bai ji dadin harin da Isra'ila ta kai a Beirut jim kaɗan kafin cimma yarjejeniyar tsakanin Iran da Amurka ba, yayin da ya ce dangantakarsa da Natanyahu ta ci gaba da kasancewa mai aminci.
Ga Tehran, wannan takun saƙa tsakanin Washington da Isra'ila na da matuƙar muhimmanci.
Ana iya gabatar da shi a matsayin shaida cewa matsin lambar da Iran ke yi ya dagula ƴancin da Isra'ila ke ganin tana da ita na yin abin da ta ga dama. Amma kuma yana sanya yarjejeniyar ta na tangal-tangal.
Idan Isra'ila ta ci gaba da aiki a Lebanon, Iran za ta fuskanci matsin lamba don mayar da martani.
Idan Washington ba za ta iya hana Isra'ila ba, za a iya jayayya da iƙirarin Teheran na cewa yarjejeniyar ta ƙunshi Labanon.
Martanin masu sauraron sashen Persia na BBC sun nuna cewa ba kowa ne ya amnice da batun cewa yarjejeniyar nasara ba ce ga Iran.
Ɗaya daga cikin masu sauraron tashar ya ce sun damu matuƙa game da wani harin da Isra'ila ta kai, amma ko da suka ji labarin yarjejeniyar, ba su amince da ita ba kuma sun damu kan ko za a tafiyar da ƙasar yadda ya kamata idan yarjejeniyar ta ɗore.
Wani ɗan ƙasar Iran mai adawa da gwamnatin ƙasar, wanda tun da farko ya goyi bayan matakin sojan Amurka, ya sanya alamar tambaya kan abin da harin na Amurka ya cimma, tun da ba zai haifar da sauye-sauyen siyasa a Iran ba:
"Fatanmu shi ne tsarin mulki ya sauya. To amma baya ga ƙunci da hauhawar farashin kayayyaki, da ƙara taɓarɓarewar tattalin arziki, wane fa'ida yake da shi ga mutane?"
Wasu kuma sun mara wa gwamnatin baya. Ɗaya daga cikin masu sauraron ya bayyana Iran a matsayin wadda ta yi nasara, yana mai cewa yaƙin ya nuna cewa yana mai cewa ''bara'' da ''roƙo'' ba su za su sanya a cire takunkumai ba, amma ana iya cire su ne ta hanyar amfani da ƙarfi.
Wani kuma ya yi taka-tsan tsan wurin yin maraba da yarjejeniyar, ta bai wa mutane damar komawa bakin aiki da rayuwa cikin kwanciyar hankali.
"Ina tsammanin na ɗan lokaci ne," in ji su, "amma muna buƙatar samun ƴan watanni da za mu sarara mu samu kwanciyar hankali."
Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman gabatar da yarjejeniyar a matsayin nasara saboda ba za ta iya tallata ta a matsayin abin da ya zame ma ta dole ba.
Amma ga Iraniyawa da dama, ba za a auna nasararta ta hanyar kirari ba. Za a auna ta ne kan mizanin ko yaƙin ya tsaya, da samun sauƙin farashi, ko idan za a samu sauƙin takunkumai, da kuma ko shugabanni na iya tafiyar da matakin yarjejeniyar na gaba ba tare da ƙara samun wani tashin hankali ba.