Sanata Aishatu Binani ta koma jam'iyyar NDC
Tsohuwar ƴar takarar gwamnan jihar Adamawa a jam'iyyar APC Sanata Aishatu Ɗahiru Binani ta sanar da ficewarta daga jam'iyyar ADC, tare da sanar da komawa jam'iyyar NDC.
Tuni jagoran jam'iyyar na ƙasa, tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Seriake Dickson ya mata maraba tare da bayyana cewa za su yi aiki tare domin ciyar da dimokuraɗiyyar Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya gaba.
A saƙon da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ya yi wa Sanata Binani godiya, "bisa aminta da tunani da tsare-tsarenmu da hangen da muke yi kan makomar Najeriya," in ji shi.
Ya ce sun ba Binata jagorancin jam'iyyar, sannan suka buƙaci ta yi aiki da sauran jagororin jam'iyyar a jiharta domin tsara ayyukan jam'iyyar.
Ya ce yana fata shigarta jam'iyyar za ta buɗe ƙofar tuntuɗar mutane da dama daga sassa daban-daban na ƙasar zuwa jam'iyyar tasu da NDC.