Fafaroma Leo zai gana da masu zargin limaman Cocin Katolika da cin zarafinsu a Faransa
Shugaban cocin Katolika, Fafaroma Leo, zai jagoranci taron ibadar jama'a a garin Lourdes, da safiyar yau yayin da yake ci gaba da ziyararsa ta kwana uku a ƙasar Faransa.
Daga baya, zai gana a asirce da mutanen da limaman cocin Katolika suka taɓa cin zarafinsu ta hanyar lalata.
Wani kwamiti mai zaman kansa ya fitar da rahoto a cikin kwanakin nan da ke nuna cewa, a cikin shekara 70 da suka gabata, yara ƴan kasar Faransa fiye da dubu ɗari uku sun fuskanci cin zarafi a hannun limamai da sauran mutanen da ke da alaƙa da cocin na Katolika.
A jiya Asabar Fafaroman ya jagoranci taron ibada a dandalin Place de la Concorde da ke tsakiyar birnin Paris.