Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manchester City da PSG na hamayya kan Valverde, Arsenal na zawarcin Fernandez
Ɗan wasan tsakiya na Uruguay Federico Valverde yana son ya ci gaba da zama a Real Madrid amma, Manchester City da Paris St-Germain suna sanya ido , idan har kulob ɗin Sifaniya ya yanke shawarar cefanar da ɗan wasan mai shekara 27. (AS)
Paris St-Germain na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan tsakiyar West Ham da Portugal, Mateus Fernandes, mai shekara 21. (Athletic)
Arsenal ma tana sha'awar Fernandes kuma a shirye take ta sayar da ɗan wasan tsakiya na Denmark Christian Norgaard, mai shekara 32, wanda bai taka rawar gani ba tun da ya koma filin wasan Emirates daga Brentford a bazarar da ta gabata. (The Times)
Aston Villa na son ɗaukar ɗan wasan gaban Argentina Matias Soule, mai shekara 23, daga Roma, bayan da kulob ɗin na Italiya ya shirya mayar da zaman aron ɗan wasan Holland Donyell Malen, mai shekara 27, zuwa na dindindin. (Gazzetta dello Sport)
Chelsea na zawarcin golan AC Milan Mike Maignan amma fatan da ƙungiyar ta Stamford Bridge ke da ita na ɗaukar ɗan wasan na Faransa mai shekara 30 na iya fuskantar cikas idan har ba ta samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ba. (Gazzetta dello Sport)
Ana danganta ɗan wasan Brazil Joao Pedro da Barcelona amma Chelsea ba ta da niyyar cefanar da ɗan wasan mai shekara 24. (Mail)
Bayer Leverkusen na shirin korar kocinta Kasper Hjulmand wanda ya karɓi ragamar aiki daga Erik ten Hag a watan Satumba. (Sky Sports Germany)
Shugaban FC Porto, Andre Villas Boas, ya ce ƙungiyar ba ta da kuɗin da za ta iya sayen ɗan wasan gaban Poland Robert Lewandowski mai shekara 37, wanda ake tunanin yana shirin barin Barcelona. (Fabrizio Romano)
Everton da Crystal Palace da Bournemouth sun tuntuɓi FC Midtjylland domin zawarcin ɗan wasan tsakiyar Chile Dario Osorio mai shekara 22. (Give Me Sport)
Manchester United na sanya ido kan ɗan wasan Sporting Lisbon da ɗan ƙasar Denmark Morten Hjulmand, mai shekara 26, wanda kuma ke jan hankalin Arsenal.(Caught Offside)
Ɗan wasan tsakiya na Middlesbrough Hayden Hackney, mai shekara 23, na shirin barin kulob ɗin na Riverside idan suka sha kashi a hannun Southampton a wasan kusa da na ƙarshe na neman gurbin haurowa gasar Premier, kuma Newcastle United na iya miƙa tayi kan ɗan wasan na Ingila. (Chronicle)