Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka yi sulhu tsakanin Barau Jibrin da Abdullahi Gwarzo
Alamu na nuna cewa an daƙile faruwar wani ɓangare na rikicin da ke ƙoƙarin ruruwa a jam'iyyar APC reshen jihar Kano da ka iya jefa jam'iyyar cikin wani hali na rashin tabbas.
Rikicin dai ya kunno kai ne tsakanin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin da tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano kuma tsohon ƙaramin ministan gidaje na Najeriya, Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo kan takarar majalisar dattawa a yankin Kano ta Arewa.
Ana dai alakanta rikicin da daɗaɗɗe wanda yake rikiɗa sakamakon al'amuran siyasa da suka faru a baya-bayan.
To sai dai wasu jerin zama da aka yi guda biyu a Abuja da Kano domin haƙurƙurtar da ɓangarorin na su yafi juna su yi aiki tare domin ciyar da APC gaba ya yayyafa wa wutar ruwa.
Na janye takarata ta sanata - Gwarzo
A wani bidiyo da ke yawo dangane da yadda aka yi zaman sulhun a Kano, tsohon mataimakin gwamnan na Kano, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya ce sakamakon sulhu da aka yi bisa jagorancin gwamnan Kano da wasu dattawan jam'iyyar APC, ya janye takarar sanatan Kano ta Arewa da ya ƙudiri niyyar yi.
"Na nemi mai girma gwamna ya ba ni lokaci na je na tuntuɓi mutanena kuma na zo na tuntuɓe su kuma sun bayar da izinin cewa a ci gaba kuma sun amince da duk abin da aka yarda da shi sannan ni ma na amince. Wannan ya sa muka rubuto takarda muka kawo wa mai girma gwamna...
"Magana ta ƙare, ni a matsayina na wanda ya yanki fom na tsayawa takara ta sanatan Kano ta Arewa na janye takarata domin al'ummarmu su zauna lafiya da kuma cigaban jam'iyyarmu," in ji Abdullahi Gwarzo.
Kafin wannan zaman dai sai da mataimakin shugaban ƙasa ya zauna da Abdullahi Tijjani Gwarzo kan batun duk da cewa bayanai ba su fito ba na haƙiƙanin abin da aka tattauna.
Ana dai yi wa Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo kallon ɗan siyasa mai tasiri a siyasar yankin Kano ta Arewa da ma jihar Kano baki ɗaya, bisa la'akari da gogewarsa da alaƙarsa da ƴan siyasa kasancewar ya fara siyarsa tun daga shugabancin ƙaramar hukuma.
Za mu yi aiki tare da Gwarzo - Barau
Shi ma mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Barau Jibrin ya nuna jin daɗinsa ga sulhun da aka gudanar da kuma irin dattakon da Abdullahi Tijjani Gwarzo ya nuna na janye muradinsa na takara da ya yi.
"Hakan ya nuna irin dattakon da ke cikin jam'iyyarmu da kuma irin son tafiyar sabuwar Kano da muke son gani. Kuma insha Allah za mu bai wa gwamnan Kano haɗin kan da yake buƙata kasancewarsa mai son ganin an samar da maslaha," in ji Barau Jibrin.
Alamu sun nuna cewa babban burin mataimakin shugaban majalisar, Barau Jibrin bai wuce na zama gwamnan jihar Kano ba kuma dukkan wasu alamu sun nuna haka musamman kafin komawar gwamnan jihar Kano zuwa APC.
Kuma bayan maslaha da jam'iyyar ta APC ta yi na bar wa Abba Kabir Yusuf takarar gwamnan ne ya sa shi Barau Jibrin yake son komawa kujerarsa ta ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Kano ta Arewa, kujerar da Abdullahi Tijjani Gwarzo ya sayi fom domin yin takara.
Mece ce alaƙar Barau da Gwarzo?
Dukkanin ƴan siyasar biyu sun fito ne daga yanki ɗaya, wato yankin Kano ta Arewa kuma dukkanninsu suna da tasiri a siyasar yankin da ma Kano.
Masu fashin baƙin siyasa na yi wa mutanen biyu kallon masu hamayya da juna kasancewar ba su taɓa haɗa tafiya tare ba koda kuwa sun haɗa jam'iyya guda.
Saɓani ya fito fili tsakanin mutanen biyu bayan da aka sauke Abdullahi Tijjani Gwarzo daga kujerar ƙaramin ministan gidaje na Najeriya, inda magoya bayan Gwarzon suka zargi mataimakin shugaban majalisar dattawan da hannu a cikin hakan.
Duk da cewa babu tabbas dangane da hannun Barau Jibrin a cire Gwarzo daga muƙamin amma ana ganin idan har hakan ma ta tabbata ba zai rasa nasaba da ƙoƙarin Barau ɗin na rage wa ɗan siyasar tasiri a yankin ba domin gudun ƙalubalantar sa.
Masu fashin baƙin siyasa na ganin ƙullatar da Abdullahi Gwarzo ya yi wa mataimakin shugaban majalisar dattawan ka iya zama matsala ga takarar Barau Jibrin, abin da ake ganin shi ne babban dalilin neman yin takara da shi.
To amma yanzu sakamakon sulhun da aka yi tsakanin ƴan takarar ana ganin komai ka iya kwaranyewa.