Yadda maslahar tsayar da Shekarau ta bar baya da ƙura

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A jihar Kano, alamu sun nuna cewa maslahar da aka yi a jam'iyyar APC da ta kai ga tsayar da Malam Ibrahim Shekarau a matsayin ɗan takarar sanatan Kano ta tsakiya, ta bar baya da ƙura, kasancewar yadda ɓangaren A A Zaura su ke ci gaba da nuna rashin amincewarsu.

Wannan ya sa wasu ƙungiyoyin mata yin zanga zanga cikin lumana domin nuna adawa da matsayar da masu neman takarar sanatan Kano ta tsakiya su ka cimma.

Mutun 6 ne suka samu ganawa da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da shugabancin APC inda suka amince da Malam Ibrahim Shekarau, ya yi takarar sanatan Kano ta tsakiya.

To sai dai wasu ƙungiyoyin mata daga shiyyar sun bayyana rashin amincewa da matakin.

Barista Binta Rabi'u ta shaidawa BBC cewa sun yi zanga zangar ne domin jan hankalin gwamnatin jihar Kano.

''Mu na zanga zanga ne na lumana , mu na jan hankalin ne dangane da ɗan takararmu da ya cancanta, Alhaji Abdulsalam Abdulkarin da aka fi sani da AA Zaura wanda gwamnati ta yi wancakali da shi''

''APC ta yi watsi da duk hidindimun da ya ke yi, saboda haka sai mu ka yi zuciya mu ka fito mu nunawa gwamnati a cikin lumana cewa mu ba za mu yi zaɓe ba, tun da Zaura baya cikin tafiyar'', in ji ta.

Ƙungiyar ta yi iƙirarin cewa ba a saka AA Zaura a cikin tattaunawar maslahar ba.

''Ba maslaha aka yi ba, a ƙarshe ma maslahar da aka kira, shi ba a kira shi ba, kawai rana ɗaya a matsayinsa na ɗan takara ya ga cewa Shekarau ya cika fom ya mayar''

''Sannan kuma sai mu ka ga an kirawo dukannin ƴan takara sun haɗa hannayensu a wuri guda, mu an tsame muna namu, wannan abin ma ya daɗa sa matan Kano central sun yi fushi'', in ji ta.

To sai dai jam'iyyar APC a Kano ta ce masu neman takarar ne da kansu suka amince da tsohon gwamnan Kanon yayi takarar ba tilastawa kowa aka yi ba, sun yi hakan ne saboda maslahar al'umma.

Hon. Umar Haruna Doguwa shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Kano ya shaidawa BBC cewa an nuna wa kowane ɗan takara girman jam'iyya.

''Abinda aka yi shi ne kowane dan takara an nuna masa girman jam'iyya da kuma muhimancin a hada abu daya domin samun tsarin da Kano za ta dogara da shi kuma an nemi cewa su dubi kansu, su yi wa kansu adalci su fitar da mutum daya a tsakaninsu''

''Gaskiyar magana bayan duk maganganun da aka yi su da kansu sun duba shekaru da kum acewa shi Malam ya taba yin gwamna sau biyu, ya yi minista da sanata suna ganin bisa girmamawa suka ce sun janye sun bar masa''

''Zan yi matukar mamaki idan shi ya fada ba a yi maslaha ba domin na san an yi magana da shi kuma ana kan magana da shi domin shi mutum ne mai daraja da girma a cikinmu'', in ji shi.

Hon Doguwa ya ya yi ikirarin cewa wasu 'yan tsiraru ne suka koma gefe domin rigima ta tashi a cikin jam'iyyar ta APC.

Ya kuma ce kawo yanzu AA Zaura dan jam'iyya ne mai matukar muhimanci kuma kwana nan zaa ga makomarsa a cikin jam'iyya.

Rahotanni na cewa tsarin maslaha ko sassanci da jam'iyyar APC ta dauka yana ci gaba da haifar da gunaguni da nuna rashin amincewa a sassan Najeriya ba kawai jihar Kano ba.

Masu sharhi kan harkokin siyasa da dama na gargadin jam'iyyar da cewa tayi kafa-kafa da wannan tsari saboda yadda wadanda aka ce su yi hakuri ke nuna fushi a fili, wasu kuwa sun yi shuru tamkar ba bu komai.