Me ya sa wasu ƴan Kannywood ke fita daga Triple R mai tallata Tinubu?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

A baya-bayan wasu jaruman Kannywood na ci gaba da ficewa daga wata ƙungiyar da wasu ƴan masana'antar suka kafa da nufin tallata Shugaba Tinubu da jam'iyyarsa ta APC gabanin zaɓen 2027.

Mutum na baya-bayan nan da ya sanar da ficewarsa daga ƙungiyar Triple R Kannywood for Renewed Hope, shi ne fitaccen jarumi Rabiu Rikadawa, wanda ya ce ya fita daga ƙungiyar saboda abin da ya kira ''rashin tabbas da rashin aiki da dokokin ƙungiya''.

Kafin Rikadawa an ga wasu fitattun jarumai da suka sanar da ficewarsu daga ƙungiyar, irin su Mansura Isa da fitaccen marubucin nan Ibrahim Birniwa da Yusuf Sasen fitaccen jarumi a masana'antar.

Ba wannan ne karon farko da Kannywood ke samun saɓani bayan kafa wata ƙungiyar siyasa ba.

Ko a 2023 ma ƙungiyar ta kafa ƙungiyar 13x13, da nufin tallata ƴansiyasa, amma ta fuskanci cikas sakamakon abin da wasu daga cikin ƴaƴan ƙungiyar suka bayyana da rashin haɗin kai.

Yaushe aka kafa Triple R?

An kafa ƙungiyar Triple R Kannywood for Renewed Hope cikin watan Afrilun 2026 a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Fitaccen mawaƙin siyasar nan na ƙasar, Dauda Kahutu Rarara ne ya jagoranci kafa ƙungiyar, kuma shi ke jagorantarta.

Fitaccen jarumin nan kuma Furodusa Lawan Ahmad shi ne a matsayin shugaban ƙungiyar.

Sai kuma Ahmad Bifa - Furodusa kuma jarumi - da ke riƙa da matsayin babban sakataren ƙungiyar.

Mene ne maƙasudin kafa Triple R?

Ƙungiyar na da wasu manufofin da suka saka aka kafata.

Wasu daga cikin dalilan kafa ƙungiyar kamar yadda Ahmad Bifa ya shaida wa BBC sun haɗa da:

  • Haɗa kai domin taimaka wa ƴan ƙungiyar marasa lafiya da marasa ƙarfi
  • Haɗa kai domin samun wakilcin muryar Kannywood mai ƙarfi a gwamnati
  • Bunƙasa ƙungiyar Kannywood
  • Tallata jam'iyyar APC da ƴantakarta a zaɓen 2027
  • Tallata kyawawan manufofin gwamnatin Tinubu
  • Faɗa wa gwamnati matsalolin da talakawa domin magance su

Me ya sa wasu ƴaƴanta ke fita?

To sai dai wasu daga cikin ƴan ƙungiyar da suka fice sun zargeta da rashin yin adalci tsakanin duka ƴayan ƙungiyar.

Rabiu Rikadawa ɗaya daga cikin waɗanda suka fita daga ƙungiyar a baya-bayan nan ya shaida wa BBC cewa ya fita ne saboda abin da ya ce ƙungiyar ta yi musu bayan wata ziyarar aiki da ta je jihar Gombe.

''A lokacin da aka kafa Triple R, an faɗa mana cewa duk wanda ya shiga ƙungiyar ba zai ƙara yin wata ƙungiyar siyasa ba, an yi hakan ne kuma saboda inganta haɗin kai da ƙarfafa ta'', in ji shi.

Sai dai ya ce tun kafin kafuwar Triple R suna da wata ƙungiya da suke zama da wasu ƴansiyasa domin kai kokensu, har ma kuma sun samu alƙawarin wani zama da ɗan gidan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu.

''A lokacin da muka shiga Triple R, mun faɗa musu cewa to akwai alƙawarin wani zama da muka yi da Seyi Tinubu, sai aka yarje mana cewa idan lokacin ya yi mu je mu gan shi amma, daga nan gaba ba za mu sake shirya wani zama ba, sai a ƙarƙashin Triple R'', kamar yadda ya shaida wa BBC.

Ya ce a lokacin da zamansu da Seyi ya ƙarato, sai tafiyar Triple R ta taso zuwa Gombe.

''Sai muka faɗa musu cewa muna da wata ziyara a Minna, sannan za mu zauna da Seyi a Abuja, wanda kuma duk mun tsara shi tun a tsohuwar ƙungiyarmu kafin shiga Triple R, haka kuma ta amince mana'', in ji shi.

Ya ce bayan sun je Abuja, ba su samu zama da Seyi Tinubu ba, sai suka tafi Gombe a cikin dare domin haɗewa da suran ƴan ƙungiyar Triple R, inda aka shirya wani aiki da ganawa da gwamnan jihar.

''Mun isa Gombe a mota cikin dare, bayan mun samu ɗaki a otal, za mu kwanta, sai aka kira mu daga Abuja cewa gobe Seyi zai gana da mu, don haka babu yadda za mu yi dole mu tafi Abuja'', in ji shi.

'An hana mu kuɗin da aka samo a Gombe'

Sai dai ya ce kafin tafiyarsu sai da suka shaida wa jagororin ƙungiyar, musamman sakatarenta, Ahmad Bifa, wanda ya ce su tafi, zai faɗa wa sauran jagororin ƙungiyar uzurinsu.

''Haka muka kama hanya cikin daren nan, washe gari muka isa Abuja, domin ganawa da Seyi'', in ji Rikadawa.

Jarumin na Kannywood ya ce bayan sun kammala da Seyi sun yi nufin komawa Gombe, sai aka ce an gama aikin Gombe cikin kwana ɗaya, don haka har ma sun dawo.

''Amma abin da ya ba mu mamaki abin da ƙungiya ta samo a Gombe an zo an raba, mu ba a bamu ba, ana cewa mu da wanda bai je ba duk ɗaya ne'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Ya ce haka dai suka yi ta bibiya, amma daga ƙarshe aka ce babu su a rabon kuɗin da aka samo.

''Yanzu mutum ya yi tafiya cikin dare daga Minna zuwa Gombe, sannan daga Gombe zuwa Kano zuwa Abuja, duk a cikin dare kuma a mota, sannan a raba kuɗi, ko na mai a gaza ba shi''?

Martanin shugabannin ƙungiyar

To sai dai jagororin ƙungiyar sun musanta wannan iƙirari na Rikadawa, suna masu cewa son rai ne ya su Rikadawa ficewa daga Triple R.

Babban sakataren ƙungiyar, Ahmad Bifa ya ce wanda suka fitan suna fifita son ransa ne maimakon ƙungiyar.

Ya ƙara da cewa waɗanda suka fitan sun fita ne saboda sun fi so su kaɗai su je su ga wani ya ba su kuɗi su kaɗai.

Ya ce duka Kannywood babu wanda ya san manyan mutane kamar Rarara.

''Don haka taimakon ƴanƙungiyar ya yi, idan ya ga dama sai ya je ya yi abinsa shi kaɗai, saboda babu wani ɗansiyasar da Rarara buƙaci ganinsa a ce bai samu ba, cikin ƙasa da kwana ɗaya'', in ji shi.

''Ko shugaban ƙasa ya san Rarara kai tsaye, ya kuma san irin taimakonsa da ya yi a baya, da wanda zai yi a nan gaba, in har zai haƙura da abin da zai samu ya kira mutane a haɗu don taimakon juna, babu dalilin da wani zai ce ba haka ba'', kamar yadda ya bayyana.

Ahmad Bifa ya kuma ce duk tafiyar babu wanda zai ce ya fita ƙungiyar ta mutu, in ba Rarara ba.

''Rarara ne kawai zai ce ya fita yau ƙungiyar Triple R ta mutu'', in ji shi.

Ya kuma ce tun da aka kafa ƙungiyar babu wanda ya taɓa yin sanadin zuwa wurin wani ɗansiyasa in ba Rarara ba.

'Su ma kuɗi suka je nema Abuja'

Ahmad Bifa ya amince cewa shi ya ba su damar tafiya Abuja, sannan ya yi alƙawarin ɓoye maganar tsakaninsu, ba tare da ya sanar da shugabannin ƙungiyar ba saboda ɓoye laifinsu matsayinsu na abokan sana'a.

Ahmad Bifa ya ce su Rikadawa sun tafi Abuja ne saboda rashin bai wa aikinsu na Gombe muhimmanci.

''In da sun bai wa aikin Gombe muhimmanci da sun zauna, abin da Seyi zai yi musu, shi za mu samu a Gombe'', in ji shi.

Ya kuma amince cewa ya yi kuskure da bai faɗa wa Rarara uzurin su Rikadawa ba, amma kuma ya ce ya yi hakan ne saboda ya rufa musu asiri.

Sakataren na Triple R ya yi zargin cewa su ma su Rikadawa kuɗi suka je nema wajen Seyi.

''Sun haƙura da Gombe ne saboda sun yi imanin cewa kuɗi za su je su samo a wajen Seyi, to mene ne laifi idan an bai wa wasu da suka je Gombe kuɗi su ba a ba su ba''?