Me janye sojojin Amurka daga Najeriya ke nufi?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Masana tsaro, sun fara tsokaci kan matakin Amurka na janye dakarunta da ta tura Najeriyar domin aikin haɗin gwiwa na yaƙi da ta'addanci a yankin Tafkin Chadi.

Masanan na tsokaci ne bayan wata sanarwar da kwamandan Amurka a Afirka da Turai Janar Dagvin R.M. Anderson, yayin wata ganawa da manema labarai da ya yi kan taron manayan jami'an harkokin tsaro na Afirka na 2026.

A yayin jawabi ga manema Labaran ya bayyana irin rawar da Amurka ta taka wajen musayar bayannan sirri , a yunkudin ƙasashen wajen yaƙi da ta'addanci da ISIS da Daesh.

Sai dai masanan tsaron irin su Audu Bulama Bukarti, mai sharhi kan lamuran tsaro a nahiyar Afirka, ya shaida wa BBC cewa, ya na ganin kai tsaye ba za a ce kwalliya ta biya kudin sabulu ba a game da zaman sojojin a Najeriya.

Ya ce, "A gaskiya na dauka sojojin za su dauki lokaci mai tsayi a Najeriya, saboda sun ce sun zo domin taya Najeriya yaki da kungiyar Boko Haram, to amma mu a iya abin da muka sani babban aikin da suka yi a game da yaki da Boko Haram, kwalli daya daya ne tal, shi ne kashe Abu Bilal al Mainoki tare da wasu mukarrabansa."

"Kisan da aka yi wa wadannan 'yan Boko Haram din babban ci gaba ne kuma koma baya ne ga 'yan kungiyar," in ji shi.

Bukarti, ya ce,"mu a zatonmu shi ne su waɗannan sojoji na Amurka za su ci gaba da irin wadannan ayyuka har sai an gurgunta kungiyar Boko Haram kafin su ce sun janye."

Ya ce "a gaskiya daga mahangar Najeriya za a iya cewa kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba, to amma da an ce sun ci gaba da zama har sai an ci karfin 'yan Boko Haram da 'yan bindiga, to za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu."

"To amma daga bangaren Amurka fa, kwalliya ta biya kudin sabulu, domin tun daga lokacin da suka ce za su shigo, muka ce dama a wajen shugaban kasar siyasa ce don bukatarsa ta biya," in ji shi.

Masanin tsaron ya ce, "Yanzu ni ina ganin tun da sojojin na Amurka za su fice daga Najeriya, to abin da ya kamata shi ne, shi ne ita Amurkan da kawayen Najeriya wato kasashen yamma su sayar wa da Najeriya kayan aikin da ta ke bukata wajen yakar ta'addancin, sannankuma idan akwai wata kwarewa da suke da ita wadda babu a Najeriya to su taimaka."

Tun a watan Fabrairun 2026 ne, Amurka ta sanar da shirin tura sojoji 200 zuwa Najeriya domin horas da dakarun ƙasar dabarun yaƙi da ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya.

Matsalar tsaron da Najeriya ke fuskanta galibi hare-hare ne na sari-ka-noƙe ko yaƙin sunƙuru.

Galibi ƙungiyoyin ƴanbindigar da ke addabar Najeriya na da mafaka ne cikin dazuka ko tsaunuka ko ma cikin tafki, kamar Tafkin Chadi da ake tunanin Boko Haram da ISWAP na ciki.

Ita kuwa rundunar sojin Amurka na da ƙwarewa sosai a wannan fanni, domin suna shiga wurare masu sarƙaƙiya su kuma yi nasara.