Ɗaya daga cikin hadiman shugaban Najeriya ya yi kira ga ga Hukumar EFCC da takwararta ta DSS da ƴansanda ba su faɗaɗa bincike tare da bankaɗo waɗanda suka taimakawa Adeyemi Adeniyi Matthew wajen da baɗaƙalar kafa hukumar bogi.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin X, babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Temitope Ajayi, ya ce ba za a rasa haɗin bakin wasu ƴan cikin gida ba a harƙallar, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Ya ce suna zargin akwai wasu mutane daga cikin gwamnati da suka taimaka wa Prince Adeniyi, amma suke ƙoƙarin jefa zargin tare da ɓata sunan shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa Femi Gbajabiamila.
A kwanakin baya ne dai wata sabuwar ce-ce-ku-ce ta kaure daga fadar shugaban Najeriya, yayin da ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasar, da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga suka musanta iƙirarin da wani mutum mai suna Prince Adeniyi Adeyemi ya yi cewa Shugaba Tinubu ya naɗa shi shugaban wata hukuma.
Cikin iƙirarin nasa, Adeniyi Adeyemi, ya ce shugaban ƙasa ne ya naɗa shi matsayin shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan shawarwarin tattalin arziki.
To sai dai, wata sanarwa da Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa ya fitar, ta ce gwamnatin Najeriya ba ta da wannan hukuma, kuma Shugaba Tinubu bai taɓa naɗa Adeyemi wani muƙami ba.