Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal da United sun rasa Gomes, Bayern da Madrid na son Gvardiol
Arsenal da Manchester United ba za su samu dan wasan tsakiya na Wolves ba Joao Gomes, mai shekara 25, saboda dan wasan na tawagar Brazil na dab da cimma yarjejeniya da Atletico Madrid. (Sun)
Bayern Munich da Real Madrid sun tuntubi wakilan dan bayan Croatia Josko Gvardiol, mai shekara 34, game da halin da ake ciki da kwantiraginsa a Manchester City. (Teamtalk)
Kociyan Paris St-Germain Luis Enrique, mai shekar 56, na dab da cimma yarjejeniya a kan sabon kwantiragi da kungiyar ta Faransa.
Kociyan dan Sifaniya an ce yana dab da kulla yarjejeniyar ci gaba da zama na sabon wa'adin shekara hudu. (Sunday Mirror)
Liverpool na sha'awar mai tsaron ragar Aston Villa da Argentina Emi Martinez, mai shekara 33, idan Allison na Brazil ya yanke shawarar tafiya. (Tuttojuve - in Italian)
A shirye Arsenal take ta sayar da matashin dan gabanta, Ethan Nwaneri, na Ingila mai shekara 19, a lokacin bazara, kuma Chelsea na daya daga kungiyoyin da ke sonshi. (Fabrizio Romano, on YouTube)