Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu uku da ke haifar da rashin fahimta tsakanin Trump da Fafaroma
Sakataren harkokin Amurka Marco Rubio ya gana da Fafaroma Leo XIV a fadar Vatican a daidai lokacin da takun-saƙa ke ƙara ta'azzara a tsakanin fadar da Donald Trump.
Fadar ɗarikar Katolika ta tabbatar da an yi taron ne a ranar Alhamis a gidan Fafaroma, amma har yanzu babu cikakken bayani kan abin da ya wakana a taron.
Wannan ne karo na biyu da Rubio, wanda shi ma ɗan Katolika ne ya gana da Fafaroma. Rubio da Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, wanda shi ma ɗan Katolika ne sun gana da Fafaroma Leo bayan rantsar da shi a ranar 18 ga watan Mayun 2025.
Tsare-tsaren ƙasashen waje
A watan jiya ne saɓani tsakanin Fafaroma da Trump ya ta'azzara bayan shugaban na Amurka ya caccaki jagoran addinin a kafar sadarwa ta Truth, inda ya kira shi da "mai rauni kan masu aikata laifuka, wanda kuma bai da ƙwarewa a harkokin ƙasashen waje."
"Ba na so Fafaroma ya yi tunanin cewa babu matsala Iran ta mallaki makamin nukiliya," kamar yadda Trump ya bayyana.
Ya ƙara da cewa, "ba na so Fafaroma ya yi tunanin cewa wani babban laifi ne don Amurka ta kai hari a Venezuela, ƙasar da ke tura ƙwayoyi Amurka, sannan take sakin ƴan ƙasarta da suke ɗaure a gidan yari, ciki har da masu kisa da dilolin ƙwaya suna kwarara ƙasarmu."
Daga baya sai Trump ya wallafa wani hoto da aka haɗa da ƙirƙirarriyar basira da ke nuna shi kamar Almasihu yana ƙoƙarin "warkar" da wani mutum, lamarin da ya ja masa suka sosai. Daga bisani dai an goge hoton.
Shugaban na Amurka ya fara caccakar Fafaroma ne bayan ya soki gargaɗin da Trump ya yi cewa Amurka za ta iya "kawar da mulkin Iran" idan Tehran ta ƙi amincewa da buƙatunsa na nukiliya da mashigar Hormuz.
A ranar Litinin, Trump ya yi wa Fafaroma shaguɓe, inda ya alaƙanta shi da cewa, "ya jefa rayuwar ƴan Katolika da wasu mutane cikin haɗari," sannan ya yi zargin cewa jagoran addinin na farin cikin ganin Iran ta mallaki makamin nukiliya.
Jawabin ne ya sa ministan harkokin wajen Italiya, Antonio Tajani ya yi martani, inda ya ce caccakar jagoran addinin babu abin da za ta yi sai ƙara ta'azzara matsalar.
A ranar Talata Fafaroma Leo ya ce babu laifi mutane su caccake shi, amma ya ce idan ma za a yi, a faɗa gaskiya, sannan ya ƙara da cewa babbn aikin Cocin shi ne yaɗa wa'azi da neman zaman lafiya.
Kwanaki kaɗan bayan rantsar da shi, Fafaroma Leo ya yi kira da a kawo ƙarshen yaƙin Gaza, tare da buƙatar a saki dukkan waɗanda Hamas ke riƙe da su, sannan a kai kayan agaji.
A Agustan 2025, Fafaroman ya soki abin da ya kira "haɗin kai wajen azabtar da Falasɗinawa," sannan ya bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin "abin rashin jin daɗi."
Duk da cewa Fafaroma Leo da Trump ba su taɓa musayar yawu a zahiri ba, masana diflomasiyyar Vatican sun yi amannar cewa akwai takun-saƙa a tsakani.
A watan Janairun bara, jagoran addinin ya bayyana rashin jin daɗinsa kan kamen da Amurka ta yi wa shugaban Venezuela na wancan lokacin, Nicolas Maduro.
Shigar baƙi
Harkar shigi da fici na cikin manyan abubuwan da suka ƙara janyo saɓanin.
Fafaroma ya sha sukar matakn Trump kan shigi da ficen baƙi, inda ya alaƙanta hakan da aikinsa na wa'azi da tausayi da girmama ɗan'adam.
A Nuwamban 2025, ya ce ana mu'amala da baƙin da suka shiga Amurka "ba tare da girmamawa ba."
"Ina tunanin ya kamata mu lalubo hanyoyin mu'amalantar mutane cikin girmamawa," in ji Fafaroma Leo.
Jagorancin addini da mulki
Rubutun Trump a kafar sadarwa a watan jiya ya zargi Fafaroma da wuce makaɗi da rawa, inda ya ce, "ba na so Fafaroma ya soki shugaban ƙasan Amurka saboda ina aikin da aka zaɓe ni ne domin shi."
Trump ya ƙara da cewa jagoran addinin ya zama jagoran ne saboda shi ɗan Amurka ne, "idan da a ce ba ni ba ne shugaban ƙasa, Leo ba zai kasance Fafaroma ba."
Da aka tambaye shi me yake nufi, sai ya ce, "ba na tunanin yana aikinsa da kyau. Ina tunanin yana son masu aikata laifi."
Washegarin jawabin da aka tambayi Fafaroma, sai ya ƙi cewa komai, inda ya nuna cewa ba ya so ya yi cacar-baki da Trump.
"Zan cigaba da bayyana rashin amincewa da yaƙi tare da ɗabbaƙa zaman lafiya da sulhu."
Ya ƙara da cewa ba ya "tsoron gwamnatin Trump," sannan ya ƙara da cewa zai cigaba da magana kan kare aikinsa na wa'azi.
Jam'iyyar Republican ta Trump ce ta samu kusan kashi 55 na ƙuri'un ƴan Katolika a zaɓen 2024 kamar yadda ƙididdigar Associated Press ta nuna, sannan ƙididdigar Amurka ta nuna cewa ƴan Katolika ne kusan kashi biyar na mutanen Amurka.
Abin da masana suke cewa
Masana na cewa irin jawaban Fafaroma na nuna cewa yana so ne ya zama kan gaba wajen adawa da wasu matakan na Trump.
"Ina tunanin ba ya so a zarge shi da sassautawa Trump da matakansa saboda shi ma ɗan Amurka ne," in ji Massimo Faggioli, ɗan Italiya kuma mai bincike, wanda yake bibiyar Vatican sosai a zantawarsa da Reuters.
Marie Dennis, tsohuwar jagorar ƙungiyar zaman lafiya ta Katolika, Pax Christi, ta ce jawaban Fafaroma Leo na kwana-kwanan nan na neman zaman lafiya ne.
"Yana kira ne ga duk waɗanda suka gaji da rikice-rikice, kuma suke neman zaman lafiya da maslaha," in ji ta.