Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaya da ƙanwar da ke aiki wuri ɗaya ba tare da sanin cewa ƴan'uwan juna ba ne
- Marubuci, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
Julia Tinetti da Cassandra Madison na da kamanceceniya a abubuwa da dama, kuma jim kaɗan bayan haɗuwarsu a wata mashaya a matsayin ma'aikata, sai suka zama abokai na ƙut da ƙut.
A wannan lokacin, cikinsu babu wanda ya san haƙinanin alaƙar da ke tsakaninsu.
Tinetti da Madison sun taso a jihar connecticut da ke Amurka a shekarun 1990.
Duk da dai basu san juna ba a lokacin ƙuruciyarsu, sun taso ne a gari ɗaya kuma minti 15 ne tsakanin gidajensu, kuma dukkaninsu riƙon su ake yi.
A lokacin ƙuruciyarta, Madison ta daɗe tana tunanin ko wace ce mahaifiyarta, kuma ta yi ta burin haɗuwa da ita wata rana.
Ta kan yi tunanin ko shin murmushinta irin na mahaifiyarta ne, ko kuma idon su ne iri ɗaya.
Ta san dai mahaifan ta ƴan ƙasar Dominican Republic ne da ke yankin Caribbean.
'' Sun yanke hukuncin bayar da ni riƙo ne saboda su talakawa ne sosai, kuma ba su da ƙarfin riƙe ni,'' in ji Madison.
A lokacin da take budurwa, Madison ta yi ƙoƙarin gano iyayen ta, amma kuma ba ta da takardar haihuwa, a don haka haƙar ta bata cimma ruwa ba.
A lokacin da ta kai shekara 19, Madison ta zana tutar ƙasar Dominican Republic a hannunta domin ya riƙa tuna mata da asalinta. '' Zama ƴar Dominican abin alfahari ne gare ni,'' in ji ta.
Shekaru biyar bayan nan, Madison ta fara aiki a wata mashaya. Nan ne ta haɗu da abokiyar aikinta Tinetti, wadda ta ga zanen tuta a hannun Madison.
Abin mamaki ita ma Tinetti tana da zanen tutar Dominican Republic, sai dai nata a gadon bayanta ya ke.
An yi mata zanen ne a lokacin da take da shekaru 22, domin ya riƙa tuna mata da inda aka haife ta.
Jim kaɗan bayan nan Tinetti da Madison suka gano cewa kowannensu riƙonsa ake yi.
'' Na ce mata, daga can aka ɗauko ni ake riƙo na,'' in ji Tinetti. '' Sai ta ce min 'tsaya, ni ma daga can aka ɗauko ni.' wannan abu da mamaki.''
Daga nan suka fara tambayar mutane, '' Shin muna kama? Mutane kuma suka yi ta cewa ''tabbas kuna kama,'' a cewar Tinetti.
Bayan wani lokaci ƙalilan, ita da Madison sai suka riƙa faɗawa mutane cikin wasa cewa su ƴan uwa ne. Madison ma ta taɓa bayar da shawarar su siya kaya ɗaya su riƙa sanyawa saboda su ƙara yin kama.
Suna ta yin komai cikin wasa, amma ko sau ɗaya basu taɓa tunanin cewa su ƴan uwan gaske ba ne.
Sun yanke shawarar su kwatanta takardun bayar da riƙon su - amma babu wani bayani a ciki da ya nuna musu su ƴan uwa ne.
Takardun sun nuna cewa a wurare daban daban aka haife su, kuma sunayen kakannin su ta ɓangaren mahaifiya ya banbanta.
Bayan wani lokaci, dukkaninsu biyu suka sami sabbin wurin aiki, sai suka rabu.
Tinetti ta ci gaba da zama a Connecticut, yayin da Madison ta koma Jihar Virginia.
Sun ci gaba da magana da juna, amma saboda nisan da suka yi sai alaƙar su ta ragu.
Bayan wasu shekaru, Madison ta samu kyautar na'urar gwajin ƙwayar halitta a lokacin Kirsimeti.
Ta hanyar amfani da na'urar, Madison ta gano wani ɗan uwanta, wanda ya faɗa mata cewa mahaifiyarta ta rasu a 2015.
Labarin rasuwar ya girgiza ta, amma kuma bayan nan, ɗan uwan nata ya taimaka mata wajen gano wasu ƴan uwan nata da dama, ciki har da mahaifinta.
Ɗan uwan Madison ya shaida mata cewa iyayenta sun sha wahala a lokacin da take yarinya.
Ta soma yin magana da mahaifinta, Adriano Luna Collado ta waya, inda ya bata labarin wasu daga cikin abubuwan da suka faru a lokacin da suka bayar da ita riƙo.
Ya ce mata su talakawa ne sosai, wanda har ya kasance a ƙasa suke kwana.
A lokacin da mahaifiyar Madison ke da ciki, yayanta na miji ya kasance ba shi da lafiya, a nan ne mahaifinsu ya yanke shawarar cewa abin da ya fi dacewa shi ne ya bayar da Madison riƙo.
Jim kaɗan bayan nan, Madison ta fara shirye shiryen zuwa Dominican Republic.
Dukkanin ƴan uwanta na jini sun tarbe ta a filin jirgin sama sanye da riguna mai hoton ta a jiki.
A lokacin da ta isa, sai ta faɗa hannun mahaifinta, suka rungume juna suna kuka.
Tafiya ce mai daɗi, sai dai zuwan Madison gida ya ƙara sauya labarin.
Wata mata mai suna Molly ta kirata. Molly ta kasance babbar ƙawar Tinetti.
Iyayen riƙon su tare suka je Dominican Republic daga Amurka domin ɗauko yaran da za su riƙe.
Molly na ganin cewa ita ƴar uwar Madison ce ta jini saboda takardar haihuwansu ya nuna sunan iyayensu mata ɗaya.
Amma gwajin halittar gado na DNA ya nuna cewa ba mahaifan su ɗaya ba, amma suna da dangantaka ta nesa, kuma an yi kuskure a sunan da ke kan takardar haihuwarsu.
Sai dai Molly na da hoton mahaifiyar Madison, wadda ta ce na yi mata kama da Tinetti, kuma hakan ya sa ta dage cewa Madison da Tinetti ya da ƙanwa ne.
Madison ta kira mahaifinta ta bidiyo inda ta tambaye shi ko sun ƙara bayar da wasu daga cikin ƴaƴansu riƙo.
'' Sai annashuwar da ke fuskarsa ta watse,'' in ji Madison. '' Sai ya ce 'Eh, na bayar.' Ni kuma sai na ce, ' Ikon Allah, amma baka taɓa faɗa min hakan ba.''
Bayan jin hakan, Madison ba ta tsaya ɓata lokaci ba. Cikin gaggawa ta je ta samo wata na'urar gwajin halittun gado, ta yi tafiyar sa'oi takwas, cikin zubar dusar ƙanƙara zuwa inda Tinetti take.
Sai da aka shafe makonni biyu da rabi kafin sakamakon ya fito.
Dukkaninsu biyu sun shiga wani yanayi a yayin da suke zaman jira, cikinsu babu wanda ke iya mayar da hankali a wajen aiki.
Daga ƙarshe dai sakamakon ya dawo, Tinetti ta buɗe saƙon da aka aiko, kwatsam sai gashi a rubuce, ita da Madison ƴan uwa ne na jini.
''Haƙikanin gaskiya wannan abun mamaki ne,' In ji Tinetti. ' Duk tsawon lokacin nan ashe mu ƴan uwa ne bamu sani ba.''
Madison ta yi kuka a lokacin da ta samu labari. Ta shaidawa mahaifinsu wanda ya yi ta murna, kuma ya matsu ya haɗu da Tinetti.
Daga nan sai suka tsara yadda za su je Dominican Republic tare.
A lokacin da suka isa, kamar yadda suka yi a baya, ƴan uwansu sun tarbe su a filin jirgin sama, a wannan karon suna sanye da riga mai hotonsu su biyu.
Mahaifinsu ya matsa kusa da Tinetti, ya rungume ta, sannan ya ce, ''Mi hija'' - ma'ana 'Ƴata'.
Tafiyarsu ta farko tare a matsayin ƴa da ƙanwa ya kasance cike da farin ciki da kiɗa da rawa.
Collado ya ce sake haɗuwa da ƴaƴan shi, shi ne babbar kyautar da Allah ya yi mishi.
'' Ina matuƙar farinciki, mara misaltuwa. A duk lokacin da suka kawo min ziyara, farinciki na mamaye min zuciyata''. in ji shi.
'' Labarinmu mai daɗi ne, ba kowa ke samun damar bayar da irin wannan labari ba.''