Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 10/05/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 10/05/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Ɗaya daga cikin maniyyatan Najeriya ta rasu a Saudiyya

    Hukumar Alhazan Najeriya ta sanar da rasuwar Mallama Aishatu Muhammadu, ɗaya daga cikin maniyyata hajjin bana a ƙasar Saudiyya.

    Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta hannun mataimakiyar daraktan yaɗa labarai Fatima Sanda Usara, ta ce marigayiyar wadda ta fito daga ƙaramar hukumar Gombi ta jihar Adamawa ta rasu ne sakamakon bugawar zuciya.

    Ta rasu ne a yau Lahadi, a kan hanyarsu ta zuwa Madinah daga Jeddah.

    NAHCON ta ce shugaban hukumar Ambasada Ismail Abba Yusuf ya tattauna da ɗan'uwan marigayiyar ta waya Umar Jauro Koko, inda aka sanar da iyalanta rasuwarta da fatan Allah ya jiƙanta.

    Hukumar ta ce Malama Aisha ta rasu ta bar ƴaƴa da jikoki da dama, cikinsu har da Abdullahi Bello, Babban Baturen Ofishin hukumar sibil difens da ke yankin Ganye.

  2. Dalilin da ya sa na maida akwatin zaɓena Abuja - Pantami

    Tsohon ministan sadarwa na Najeriya Farfesa Isa Ali Pantami ya yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa ya taɓa mayar da akwatin zaɓensa zuwa Abuja daga Gombe.

    A hirarsa da gidan talabijin na TVC a yau Lahadi, Pantami wanda ɗaya ne daga cikin masu neman tikitin takarar gwamnan jihar Gombe a zaɓen 2027, ya kuma yi tsokaci kan zargin da ake masa na watsi da lamuran jam'iyyar ta APC na tsawon lokaci.

    Pantami ya ce ya maida akwatin zaɓensa zuwa Abuja ne a shekarar 2019 saboda muƙamin da ya riƙe na shugaban hukumar NITDA a lokacin, kuma yana daga cikin masu jagorantar abubuwan da suka shafi bayanan intanet da suke da alaƙa da zaɓen, wanda hakan ya sa ake buƙatar kasancewrasa a birnin tarayyar ƙasar.

    Amma ya ce yanzu haka ya maida akwatin zaɓensa jihar Gombe.

    A ƴan kwanakin nan dai Pantami ya ɗauki hankalin ƴan Najeriya, tun bayan da jam'iyyarsa ta APC ta amince da miƙa tikitin takarar gwamnan jihar Gombe ga Jamilu Isiyaku Gwamna bisa tsarin masalaha, abin da Farfesan ya yi watsi da shi, inda ya ce zai yaƙi "rashin adalcin da aka yi".

    Da aka tambaye shi game da rashin ba da gudummuwa ga harkokin jam'iyyar APC a lokacin da yake riƙe da muƙamin minista, Pantami ya ce ba haka batun yake ba.

    Ya ce ya sha bayar da gudummuwar kuɗi ga jam'iyyar a lokuta daban-daban, inda ya yi iƙirarin cewa ko a kwanan nan ya ba da "gudummuwar naira miliyan 50" a yayin babban taron jam'iyar a Abuja, da kuma wata "miliyan 45" a lokacin sabunta rijistar jam'iyyar ta APC.

    Shehin Malamin ya ƙara da cewa, ba a taɓa neman wata gudummuwa daga gareshi ya ƙi yi ba.

  3. Iran ta gargaɗi Birtaniya da Faransa kan tura dakaru Mashigar Hormuz

    Iran ta gargadi Faransa da Birtaniyya cewa idan suka tura sojojinsu zuwa mashigar Hormuz za su fuskanci zazzafan martani.

    A ƴan kwanakin nan, Faransa da Birtaniya sun ba da sanarwar cewa za su tura jiragen yaƙi zuwa Hormuz.

    Kasashen na Turai sun ce tura waɗannan dakaru na da nufin shiga wani shiri da suke yi na tabbatar da tsaron jiragen ruwa a mashigar Hormuz. Ƙasashen biyu sun ce za a fara aikin ne bayan kawo karshen yaƙin.

  4. Saura ƙiris Arsenal ta lashe gasar Premier

    Arsenal na dab da zama gwarzuwar gasar Premier Ingila ta 2025/26, bayan nasarar da ta samu a wasan hamayyar Landan.

    Arsenal ta samu nasara da ci 0-1 a filin wasa na London Stadium, wanda hakan ya ƙara nutsar da West Ham zuwa ƙungiyoyi ukun ƙarshe na gasar Premier da za su faɗa Championship.

    Da wannan nasara Arsenal ta haɗa maki 79, cikin wasanni 36 da ta buga, yayin da ya rage saura wasa biyu a kammala gasar ta bana.

  5. Rundunar sojin Sudan ta ce ta ƙwace wani yankin da RSF ta mamaye

    Rundunar sojin Sudan ta ce ta sake ƙwace wani yankin da a baya mayaƙan RSF suka mamaye a Kudu maso gabashin ƙasar, kusa da kan iyakar Habasha.

    Rundunar ta ce ta ƙwato yankin ne a jiya Asabar, makonni biyu bayan RSF ta ƙwace shi.

    Babu dai wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan iƙirari.

    Bayan yaƙin basasa na shekaru uku, yanzu haka dakarun ƙasar ke da iko da tsakiyar Sudan, ciki harda birnin Khartoum yayin da mayaƙan RSF ke iko da yankin Darfur da ke yammaci.

  6. Dole sai mun lalata uranium ɗin Iran za a dakatar da yaƙi - Netanyahu

    Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu, ya ce dole ne a lalata sinadarin Uranium da Iran ta ke da shi, sannan za a kawo ƙarshen yaƙinta da Amurka da Isra'ila.

    Wannan na daga cikin abin da Firaministan ya faɗa a wata hira da za a saki da shi anjima.

    "Wannan [yaƙin] bai ƙare ba tukuna, saboda makaman nukiliya, tataccen uranium ɗin, dole ne a fitar da su daga Iran. Wuraren da ake amfani da su dole ne a wargaza su," kamar yadda ya faɗa a cikin wata hira da gidan talabijin na CBS.

    Ya ƙara da cewa: "Har yanzu Iran tana goyon bayan dakarun juyin juya hali da ƙera makamai masu linzami. Yawancin waɗannan an lalata su, amma akwai sauran aiki."

    Da aka tambaye shi ta yaya za a fitar da wannan Uranium ɗin, Mista Netanyahu ya ce: “Ku kuka shigo da kuma ku za ku fitar da shi."

  7. Jami'an tsaro sun miƙa Bello Badejo ga hukumar EFCC - Hadiminsa

    Jami'an tsaron Najeriya da suka kama ɗantakarar Sanatan Taraba ta tsakiya a jam'iyar APC, Bello Bodejo, sun miƙa shi ga hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasar ta'annuti EFCC.

    A kama Badejo, wanda shi ne shugaban ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore, a daren Alhamis bayan ya sauka a filin jirgin sama na Danbaba Suntai da ke birnin Jalingo a jihar.

    Hadimin Badejo, Malam Umar, ya shaida wa Daily Trust cewa magoya bayansa ne suka raka shi zuwa ofishin jami'an tsaron da suka kama shi, amma bai bayyana ko su wane ne ba.

    Umar ya ce tuntuni jami'an suka kai Badejo ofishin EFCC da ke Abuja, kuma babu wani ƙarin bayani da aka yi musu game da dalilin kama shi.

    Ya yi zargin cewa wasu abokan hamayyarsa ne suka kitsa kama shi saboda farin jinishi a takarar.

    "Yanzu haka ana tantance ƴantakarar jam'iyar kuma an kusa kammalawa. Manufarsu ita ce su hana shi shiga tantancewar," in ji Umar.

    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Amnesty International ta yi kira hukumomin Najeriya su saki ɗantakarar Sanatan, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa.

  8. Malami ya sayi fom ɗin takarar gwamnan Kebbi a ADC

    Tsohon babban lauyan gwamnatin Najeriya, kuma ministan shari'ar ƙasar, Abubakar Malami ya sayi fom ɗin takarar gwamnan jihar Kebbi a jam'iyyar ADC domin shiga zaɓukan 2027.

    Malami ya ce ya ɗauki matakin shiga takarar ne saboda a cewarsa ba zai yi shiru kan abin da ya kira halin rashin tsaro da talauci da yunwa da taɓarɓarewar lafiya da matsin tattalin arziki da jiharsa ta Kebbi ke ciki ba.

    Tsohon ministan ya yi zargin cewa jihar Kebbi na fuskantar ɗaya daga cikin mafiya munin halin jin ƙai da munin shugabanci a Najeriya, inda ya kafa hujja da alƙaluman yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar da kuma matsayin talaucin da jihar ke ciki da yawan mace-macen mata a lokacin haihuwa da rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin tsaro.

    A cewar Malami, fiye da kashi 67 cikin 100 na yaran jihar ƴan tsakanin shekara 6 zuwa 15 ba sa zuwa makaranta, yayin da ya ce fiye da kashi 88 cikin 100 na yaran jihar na fama da talauci ta fuskoki daban-daban.

    A yanzu haka dai tsohon ministan na fuskantar shari'ar zarge-zargen almundahanar miliyoyin kuɗaɗe a lokacin da yake riƙe da muƙamin ministan shari'ar ƙasar, tsakanin 2015 zuwa 2023.

  9. Shugaban Faransa ya isa Nairobi a wata ziyara da yake yi a Afirka

    Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya isa Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya a wata ziyara da yake yi don yauƙaƙa dangantaka da Afirka.

    Mista Macron zai gana da shugaban ƙasar Kenya, William Ruto a yau, kafin shugabannin biyu su jagoranci taron zuba jari na Afirka a gobe Litinin.

    Taron zai samu halartar shugabannin ƙasashen Afirka da jagororin kasuwancin nahiyar domin tattauna batutuwan da suka shafi kasuwanci da ƙirƙira da kuma ci gaba mai ɗorewa.

    A shekarun baya-bayan nan, Faransa ta rasa tasiri a ƙasashen da ta yi wa mulkin mallaka a Afirka ta Yamma.

    A baya-bayan nan ƙasashen Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar suka kori dakarun Faransa da suka shafe shekaru suna yaƙar ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi a ƙasashen.

  10. Amnesty ta nemi hukumomin Najeriya su bincike kisan wani almajiri a hannun ƴansandan Katsina

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International a Najeriya ta buƙaci hukumomin ƙasar su binciki mutuwar wani almajiri mai shekara 16 a ofishin ƴansanda na Ƴankara da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina.

    Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce binciken da ta yi ya nuna cewa almajirin ya mutu ne sakamakon azabtarwa ta hanyar dukansa da wayar ƙarfe da ƴansandan suka yi.

    Amnesty ta ce ƴansandan sun kama almajirin ne mai suna Bishir Malam Dauda daga makarantar tsangayarsu bayan da wani abokinsa ya ambaci sunansa a lokacin da ƴansandan ke yi masa binciken zargin satar wake.

    Ƙungiyar ta zargi jami'an ƴansandan Ƴankara da azabtar da yaron har sai da ya mutu, sannan suka kai gawarsa ƙaramin asibitin Ƴanƙara.

    ''Abin da ya faru da almajirin na azabtarwa, tsantsar keta haƙƙin bil'adama ne... Don haka dole ne a gudanar da bincike tare da hukunta duka ƴansandan da ke hannu a lamarin'', in ji sanarwar.

    Malamin Almajirin da BBC ta zanta da shi ya ce ƴansandan sun ɗauke shi daga makarantarsa da nufin gudanar da bincike, amma sai baturen ƴansandan yankin ya sanar masa da mutuwar yaron.

    Kawo yanzu dai rundunar ƴansandan jihar ba ta ce komai ba game da lamarin.

  11. 'Mun aika wa Pakistan amsa kan shawarar Amurka ta kawo ƙarshen yaƙinmu'

    Iran ta ce ta aika wa Pakistan amsa kan matsayin da ta ɗauka game da sabuwar shawarar da Amurka ta gabatar na kawo ƙarshen yaƙin ƙasashen biyu.

    Ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi ya ce ƙasarsa ''ta fitar da matsayin nata ne'' bayan cikakken bincike na nazari.

    Sai dai ba ta yi arin haske kan abin da ke cikin amsar tata ba.

    Amma rahotonni sun ce saƙon na na Iran ya ƙunshi raba tattaunawar zuwa matakai guda biyu, na farko shi ne mayar da hankali don kawo ƙarshen rikicin da ake yi kan mashigar Hormuz, yayin da mataki na biyun zai ƙunshi tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran da takunkuman da aka sanya mata.

    A makon da ya gabata ne Amurka ta fitar da sabuwar shawarar kawo ƙarshen yaƙin, inda Donald Trump ya ce suna jiran martanin Iran game da hakan.

    A cewar kafofin yaɗa labaran Amurka, sabuwar shawarar Amurka, takarda ɗaya ce mai sakin layi 14.

  12. Jirgin Qatar ɗauke da gas ya tsallaka mashigar Hormuz zuwa Pakistan

    Cibiyoyin kula da sufurin jiragen ruwa na duniya sun ce wani jirgin man Qatar ɗauke da gas ya tsallaka mashigar Hormuz, inda ya kama hanyar zuwa Pakistan

    Idan ta tabbata mai ya fitar - bayan amincewar Iran - zai kasance jirgin Qatar na farko da ya fitar da kaya daga Gabas ta Tsakiya tun bayan fara yaƙin.

    A wani labarin na daban kuwa firaministan Qatar ya soki Iran kan harin da ta kai wa wani jirgin dakon kaya mai ɗauke da tutar Amurka a gaɓar ruwar Qatar.

    Harin ya haifar da ƴar ƙaramar gobarar, amma babu rasa rai.

    Kuwait da UAE sun bayar da rahoton kakkaɓo jiragen Iran marasa matuƙa, da suka zarga da keta sararin samaniyarta.

  13. An yi zanga-zangar adawa da gwamnatin Netanyahu a Tel Aviv kan yaƙin Iran

    Wasu mazauna birnin Tel Aviv sun gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Benjamin Netanyahu kan yaƙin Iran.

  14. Indiya ta yi gwajin sabon makaminta na linzami na zamani

    Rundunar sojin Indiya ta yi nasarar yin gwajin sabon makaminta na linzami na zamani mai suna Agni wanda ya faɗa gaɓar ruwan Odisha.

    Makamin zai kuma iya harba kayuwa masu yawa a lokaci guda zuwa wurare daban-daban.

    Ma'aikatar taron ƙasar ta ce an yi gwajin makamanin ne a ranar Juma'a, 8 ga watan Mayu.

    "An har makamin ne daga tsibirin Abdul Kalam zuwa Odisha'', a cewar ma'aikatar tsaron cikin sanarwar da ta fitar.

    An fara ƙera makamin na Agni ne a shekarar 1983, inda aka riƙa sabunta shi lokaci zuwa lokaci, har zuwa yanzu da aka sabunta shi a karo na biyar, wanda zai iya yin tafiyar nahiya zuwa nahiya, wanda kuma zai iya ɗaukar kan makamin nukiliya.

    Makamin zai iya yin tafiyar tazarar kilomita fiye da 5,000 kafin ya sauka.

  15. Atiku, Amaechi da Hayatudeen sun sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasa a ADC

    Jiga-jigan adawar Najeriya na haɗakar jam'iyyar ADC uku sun sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar.

    Mutanen uku da kawo yanzu suka sayi fom ɗin sun haɗa da jagoran adawar ƙasar, Atiku Abubakar, da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da kuma Mohammed Hayatu-Deen.

    Hayatu-Deen ne ya fara sayen fom ɗin, kafin daga baya sauran mutanen biyu suka bi sahunsa.

    Matakin na zuwa ne ƙasa da shekara guda kafin babban zaɓen ƙasar na 2027.

    Yanzu abin da ya rage shi ne zaɓen fitar da gwani tsakanin ƴantakarar uku, domin tunkarar Tinubu na APC da kuma wanda NDC za ta tsayar.

    ADC na ɗaya daga cikin manyan jam'iyyun hamayya a ƙasar, sai dai sakamakon rikicin shugabancin da take fama da shi a baya-bayan nan ta rasa biyu daga cikin manyan jiga-jiganta, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso da suka koma NDC.

  16. Fars: Jirgin Amurka aka kai wa hari a gaɓar ruwan Qatar

    Kamfanin dillancin labarai na Fars ya ruwaito cewa jirgin dakon kayan nan da aka kai wa hari a gaɓar ruwan Qatar na Amurka ne.

    Fars ya ambato wata majiya na cewa jirgin dakon kayan na tafiya ne ɗauke da tutar ƙasar Amurka a jikinsa.

    Kawo yanzu dai Amurka ba ta ce komai ba game da harin jirgin.

    Cibiyar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Birtaniya - wadda ke lura da hanyoyin sufurin jiragen ruwa na duniya - ta ce wani makami da ba a san daga inda aka harbo shi ba, ya faɗa kan jirgin ruwan a kusa da gaɓar ruwan Qatar.

    Rahotonni sun ce harin ya faɗa kan jirgin ne tazarar kilimota 43 daga arewa maso gabashin Qatar, lamarin da ya sa wuta ta kama jirgin, amma ba wanda ya rasa ransa.

  17. Ƙasashen da suka saka mana takunkumi ba za su wuce ta Hormuz ba - Iran

    Rundunar sojin Iran ta ce ƙasashen da ke aiki da takunkuman da Amurka ta sanya wa ƙasar za su fuskanci wahalar wucewa ta Hormuz.

    Kamfanin dillancin labaran ƙasar, IRNA ya ambato kakakin rundunar sojin ƙasar, Mohammad Akraminia na cewa ''daga yanzu duk ƙasar da ke aiki da takunkuman da Amurka ta sanya mana, jiragenta ba za su wuce ta mashigar Hormuz cikin sauƙi ba''.

    ''Amurka ba za ta iya tare duka wannan na Tekun Arewacin Indiyan mai faɗin gaske ba, da abin da take na datse jiragenmu ba'', in ji shi.

    Ya ci gaba da cewa ''babu shakka maƙasudin wannan datsewar shi ne matakin farfaganda na yunƙurin kisan jami'an Iran masu lura da mashigar Hormuz, kuma yaƙin da muke yi na ci gaba da tafiya yadda muke so, kawo yanzu jirage ƙalilan aka kama, yayin da mu kuma muka samu nasarar hana jiragen gwamnatin Yahudawa zirga-zirgar muka kuma kama wasu''.

  18. An rantsar da tauraron fina-finan Indiya a matsayin babban ministan Tamil Nadu

    An rantsar da tauraron fina-finan Indiyan nan da ya jagoranci jam'iyyarsa wajen lashe zaɓen majalisar dokokin jihar Tamil Nadu a kudancin Indiya, a matsayin babban ministan jihar.

    C Joseph Vijay, jagoran jam'iyyar TVK (Tamilaga Vettri Kazhagam), ya sha rantsuwar kama aiki a gaban dubban magoya bayansa a Chennai, babban birnin jihar.

    Mista Vijay zai jagoranci gwamnatin haɗaka, wadda jam'iyyarsa ta lashe kujeru 108 a majalisar dokokin jihar.

    Jam'iyyarsa ta TVK ta ƙulla ƙawance da wasu jam'iyyun uku domin samun rinjayen kujeru 118 da take buƙata domin kafa gwamnati.

  19. Firaministan Qatar ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya gana da firaministan Qatar a birnin Miami na Amurka.

    Kakakin ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ya ce Mista Rubio da Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani sun tattauna buƙatar aiki tare ''domin kawar da barazana da inganta zaman lafiya da tsaro a faɗin Gabas da Tsakiya.''

    Yanzu haka dai Amurka na jiran martanin Iran kan sabuwar shawarar yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da ƙasashen biyu ke yi, domin fara zaman tattaunawar zaman lafiya tsakanin ɓangarorin.

    A ƴan kwanakin nan an yi musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu a kewayen mashigar Hormuz, karon farko tun bayan fara aiki da yarjejeniyar dakatar wuta.

    Tun bayan fara yaƙin ne dai Iran ta hana jiragen ruwan da ba nata ba wucewa ta mashigar.

  20. 'An kai wa jirgin ruwan ƴan kasuwa hari a gaɓar ruwar Qatar'

    Cibiyar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Birtaniya - wadda ke lura da hanyoyin sufurin jiragen ruwa na duniya - ta ce wani makamai da ba a san daga inda aka harbo shi ba, ya faɗa kan wani jirgin ruwa na ƴan kasuwa a kusa da gaɓar ruwan Qatar.

    Rahotonni sun ce harin ya faɗa kan jirgin ne tazarar kilimota 43 daga arewa maso gabashin Qatar, lamarin da ya sa wuta ta kama jirgin, amma ba wanda ya rasa ransa.

    Matakin na zuwa ne yayin da rundunar juyin juya halin Iran ta sake yin barazanar kai hare-hare kan cibiyoyin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, idan har aka kai wa jiragen Iran hare-hare, yayin da ake ci gaba da zaman ɗarɗar a mashigar Hormuz.