Yadda ƴansanda suka tilasta wa shugaban yaƙi da rashawa na Najeriya bayar da cin hanci

Wani abu mai kama da almara ko? Amma da gaske ne ya faru.
An daɗe ƴan Najeriya na kokawa game da ƙazancewar ayyukan rashawa a ma'aikatu da hukumomin gwamnati, kuma hukumar ƴansanda ta ƙasar na cikin waɗanda a kodayaushe ake nunawa, kan cewa jami'anta na yawan karɓar kuɗi daga al'umma sa'ilin da suke bakin aiki.
Amma an ce kwana dubu ta ɓarawo, kwana ɗaya kuma ta mai kaya.
A wannan karo shugaban hukumar yaƙi da rashawa da laifuka makamantan haka ICPC na Najeriya, Musa Aliyu ne ya faɗa hannun wasu jami'an ƴansanda a birnin Abuja, waɗanda suka buƙace shi ya ba su kuɗi bayan zargin shi da laifin karya doka.
Tuni hukumar ƴansanda ta tabbatar da faruwar lamarin har ma ta bayyana cewa ta fara ɗaukar matakin kan lamarin.






















