Dalilinmu na zaɓar tsarin falle ɗaya na mulkin Najeriya - NDC

Asalin hoton, Saifullahi Hassan/FB
A Najeriya, jam'iyyar hamayya ta NDC ta yi ƙarin haske kan dalilan da suka sa ta yanke shawarar miƙa takarar kujerar shugaban ƙasar ga kudancin ƙasar a zaɓen 2027, domin yin wa'adin mulki na falle ɗaya tsawon shekara huɗu, daga nan sai arewacin ƙasar ya karɓa.
Shugabannin jam'iyyar da magoya bayansu sun ce sun amince da wannan tsari, domin samar da zaman lafiya da hadin kan kasa, da tabbatar da adalci a tsarin dimokuradiyya, da kuma kokarin ganin ana damawa da kowa a fagen siyasar Najeriya.
Jam'iyyar ta zartar da wannan matsaya ne a babban taronta na farko tun bayan kafuwarta, wanda aka yi a Abuja, babban birnin tarayya na kasar.
Taron ya samu halartar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, da takwaransa da ya yi wa NNPP takarar shugaban kasar a 2023, kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Bisa ga dukkan alamu jam'iyyar Peter Obi ne zai kasance dantakarar shugaban kasa, Kwankwaso mataimakinsa na jam'iyyar, a zaben 2027, na Najeriya.
Akwai kuma shugaban jam'iyyar, Henry Seriake Dickson da sauran kusoshi da 'ya'yan jam'iyyar da dama.
Abubuwan da aka cimma a taron
Dakta Yunusa Tanko wanda shi ne jagoran ƙungiyar magoya bayan Peter Obi, wato Obidient Movement, ya ce an cimma yarjeniyoyi uku:
- Ɗan takarar shugabancin ƙasa zai futo daga kudanci, yayin da za a ɗauko mataimakin daga arewacin Najeriya.
- Kudanci za su yi shekaru hudu (Falle ɗaya) , sannan mulki zai koma arewacin Najeriya.
- Shugabannin jam'iyyar ta NDC za su ci gaba da kasancewa a matsayin shugabanni har zuwa bayan zaɓen shugaban ƙasar na 2027.
- An yi gyare-gyare a wasu sassan kundin tsarin mulkin jam'iyyar biyu zuwa uku.
Dakta Yunusa Tanko ya ce dukkan waɗannan yarjeniyoyi ƴan jam'iyyun sun amince da su da dukkan batutuwa da aka yi yarjejeniyar da su.
Sai dai kuma wasu na ganin cewar duk da wannan yarjejeniya da aka cimma ta yin mulkin shekaru hudu na falle ɗaya ba lallai ta tabbata ba, inda akan samu wasu lokutan da shawara kan chanja, wani batu da Dr Tanko Yunusan ya ce abu ne ba ba zai yiwu ba kasancewar yarjejeniya ce a rubuce.
''Ai ba zai yiwu ba, saboda abu ne da a aka yi yarjejeniya aka kuma rubuta shi, Mr Peter Obi ya yi alƙawari kuma zai cika shi, kuma zai yi ƙoƙari wajen fitar da al'ummar Igbo daga zargin da aka jima ana yi musu na cewar za su raba ƙasar idan suka sami mulki"
Dakta Yunusa Tanko ya jaddada cewar: 'In Allah Ya yarda wa'adi ɗaya zai yi, kamar yadda ya yi alƙawari, sannan kuma bayan ya yi falle dayansa, zai miƙa mulkin zuwa ga arewacin ƙasar tare da gudunmawa daga tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso," in ji Dakta Yunusa Tanko.
Me Kwankwasiyya ke cewa?
Dakta Habib Saleh Mailemo shi ne mai magana da yawun tafiyar Kwankwasiyya ta Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ce kowa ya bi:
"Babban buri shi ne dukkan abun da za a yi shi ne a samar da haɗin kai da zaman lafiya a kasar baki daya, kuma mun amince cewar in wannan zai tabbatar da hadin kan ƴan Najeriya da samar da damar ɗorewar dimokaradiyya a Najeirya, to gaskiya mun aminta da shi muna goyan baya." A cewaer Dakta Habib Saleh Mailemo
Masu sharhi kan lamuran siyasar Najeriya dai sun yi tsoakci, cewa ya zama wajibi shugabanni da sauran 'ya'yan wannan jam'iyya su bi matakan da duk suka kamata, don kaucewa bullar rikicin cikin gida, wanda ka iya tadiye wannan shiri da suka yi.










