Me ya sa masu gidajen haya ke tsuga farashi a jihar Kano?

.
Bayanan hoto, '
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Majalisar dokokin jihar Kano ta buƙaci a sake duba dokar kula da haya a jihar, sakamakon hauhawar kuɗin hayar gidaje da shaguna da ke ƙara jefa magidanta da ƙananan 'yan kasuwa cikin matsin tattalin arziki.

Majalisar ta ce gidan da ake biyan naira dubu dari a baya yanzu ya koma naira dubu dari biyu ko fiye, lamarin da ta ce akwai bukatar a yi duba na tsanaki akai.

Tun da farko ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Takai a majalisar dokokin jihar Kano, Hon. Musa Kachako ya gabatar da ƙuduri kan matsalar hauhawar kudin haya a Kano a zauren majalisar.

Hon Kachako ya shaida wa majalisar cewa kuɗin hayar gidaje da a baya ake biyan naira 100,000 a shekara yanzu ya tashi zuwa tsakanin naira 200,000 da 300,000, yayin da hayar shaguna ta ƙaru daga naira miliyan ɗaya zuwa miliyan biyu cikin shekara guda.

Dan majalisar ya nuna damuwa kan yadda wasu masu gidaje ke ƙara kuɗin haya ba tare da bai wa 'yan haya isasshen sanarwa ba, lamarin da ya ce yana ƙara wa 'yan kasuwa da manoma da masu ƙaramin ƙarfi wahalar rayuwa.

Tuni dai wasu Kanawa suka fara tsokaci kan matakin:

Idan da gwamnati tana bibiyar irin wadannan matsaloli da an sami fahimtar juna da saukakawa juna

''Yanzu idan ka ɗauki yadda masu haya suke shan wahala a wurin wanda suke haya a wurinsu ya kamata a ce dama tuntuni gwamnatin a ce ta shigo'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa yanzu kana haya a gidan mutum, fargabar a ce shekara ta zagayo, saboda shekara a ce ta zagayo ba mamaki ya ninka kudin

'Ƙudiri ne mai kyau'

Wasu mazauna jihar sun yaba wa ƙudirin majalisar ya yi na fatan rage kuɗin haya a jihar.

''Wannan ƙudiri ya tabbata kudiri ne mai kyau, a nan jihar Kano, ba dan komai ba saboda gaskiya halin da ke ciki su fa masu karɓar hayar nan, in shago ne da mutum, to sai shekara ta ɓare ba sai abinda yake so ba har ya ce ya yi riba'' in ji shi.

Ɗan majalisar da ya gabatar da wannan ƙudiri, ya jaddada cewa duk da haƙƙin masu gidaje da shaguna na samun ribar jarin da suka zuba, ya kamata a samar da tsari dokokin da za su tabbatar da adalci da sanarwar lokacin karin kudin haya da kuma hana ƙarin haya fiye da kima, da kuma fayyace ƙa'idojin ƙara kuɗin haya tare da daidaita hakkokin masu gidaje da 'yan haya.

Bayanai na cewa nan gaba ne majalisar za ta saka ranar da 'yan majalisar za su tattauna akan wannan kudiri.

Tsadar gidajen hayar ruwan dare ne a Najeriya

Batun tsadar haya abu ne da ya zama ruwan dare a Najeriya musamman a manyan birane kamar Legas da Abuja.

Samun matsuguni mai kyau babban ƙalubale ne a ko'ina, amma haɗa kuɗin haya na shekara guda kafin a ba ka gidan ƙarin nauyi ne ga miliyoyin ƴan Najeriya.

Masu gidajen haya sun fi son a ba su kuɗin hayan a dunkule saboda yana rage yiwuwar gazawar ɗan haya wajen biyan kuɗin haya.

A ganinsu, gara a matsa wa ɗan haya sau daya a shekara maimakon sau 12, wato kowane wata ke nan cikin shekara.