Ko Rasha za ta iya kai wa NATO hari?

.
Bayanan hoto, Putin ya zargi ƙasashen Turai da ɗarsa fargabar yuwwar yaƙi tsakanin Rasha da NATO
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Batun yiwuwar Rasha ka iya ɗaukar matakin soja a yankin wata ƙasa mamba a ƙungiyar tsaro ta NATO ya sake tasowa, matakin da a baya Moscow ta sha musantawa da jaddada ba ta da aniyar aiwatar da hakan, to amma a yanzu kafafen yada labarai sun kara bijiro da shi a baya-bayan nan.

A ranar 5 ga Oktoba, 2026, jaridar Financial Times ta ruwaito cewa Estonia na matsar da dakarunta kusa da iyakar Rasha saboda fargabar yiwuwar harin da Moscow za ta kai.

A ranar 24 ga Satumba, 2026, Hukumar Leken Asirin Sojin Denmark ta yi gargadin cewa akwai barazanar cewa Rasha za ta iya tura ƙaramin adadin sojoji zuwa wata ƙasa makwabciya mamba ta NATO a cikin watanni masu zuwa.

Kasashen Poland da Jamhuriyar Czech su ma sun bayyana damuwa kan yiwuwar sojojin Rasha ka iya shiga yankin wata ƙasa ta NATO ko kuma kai hare-hare ta sama.

A ɓangare guda kuma, jami'an Moscow na ci gaba da nuna Rasha a matsayin wadda ke fama da faɗaɗawar NATO, suna kuma zargin ƙungiyar da ƙoƙarin kewaye Rasha ko hana ta samun cikakken shiga yankin Kaliningrad, wani yanki na Rasha da ke ware kuma a kan gabar Tekun Baltic.

Saboda haka, tambayar ita ce: Shin da gaske Rasha ka iya kai wa ƙasashen NATO hari, kuma wacce barazana hakan ka iya yi a yankin?

Mecece matsayar Moscow?

Sauran manyan jami'an Rasha ma sun bayyana matsayi iri ɗaya.

Mai magana da yawun fadar Kremlin, Dmitry Peskov, ya ce jita-jitar da ake yaɗawa kan Rasha na iya tura sojoji zuwa wata ƙasa mamba ta NATO a matsayin:

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Labarai masu tayar da hankali."

Shi kuma Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya ce:

"Moscow ta sha bayyana cewa ba ta da niyyar kai hari ga Turai."

Sai dai jami'an Rasha ba su yi bayani kan duk wani sauyin manufar sojin ƙasar game da NATO ba, duk da cewa rundunar sojin ruwan Rasha a Tekun Baltic ta gudanar da atisayen soja da dama a cikin watannin baya-bayan nan.

A farkon watan Agustan shekarar 2026, rundunar ta gudanar da atisaye da ya haɗa da ƙungiyoyin da ke kula da fannin makamai masu linzami, da ƙungiyoyin yaƙi da masu tayar da ƙayar baya sun shiga atisayen kare wani sansanin sojin ruwa daga wani harin da aka ƙirƙira a matsayin gwaji.

A ranar 3 ga Oktoba, 2026, kamfanin United Shipbuilding Corporation, wanda shi ne mafi girma cikin kamfanonin gina jiragen ruwa a Rasha, ya sanar da cewa jirgin ruwan ƙarƙashin teku na "Veliky Loki" ya gudanar da atisayen harba torpedo cikin nasara.

A lokaci guda kuma, ƙawancen Rasha da Belarus, ya gudanar da wani babban atisayen sarrafa rundunoni na tsawon kwanaki huɗu daga ranar 15 zuwa 18 ga Satumba, 2026, kusa da iyakokin ƙasashen Lithuania da Poland.

An gudanar da wannan atisaye ne a kusa da Mashigar Suwałki, wani ɗan ƙaramin yanki da ke kan iyakar Poland da Lithuania wanda ke raba Belarus da yankin Kaliningrad na Rasha.

Mashigar Suwałki tana da muhimmanci matuƙa a fannin tsaro saboda ana kallonta a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da suka fi muhimmanci a tsakanin NATO da Rasha.

Idan aka samu rikici, ikon sarrafa wannan yanki na iya yin tasiri sosai ga damar NATO na kai taimako ga ƙasashen Baltic da kuma damar Rasha ta haɗa Kaliningrad da Belarus.

Me Rasha ke yi a yankin tekun Baltic?

A taron shekara-shekara na masan harkokin ƙasashen waje na Valdai da ke gudana a kusa da ƙasar sa cewa Rasha ba da ta aniyar kai hari ga kowa, ba ta da niyyar kai hari a shekarar 2029, ko 2030, kuma ba za ta kai hari a shekarar 2050 ba.

Ya kuma zargi ƙasashen Turai da ƙoƙarin karkatar da hankalin jama'arsu daga matsalolin cikin gida ta hanyar tayar da fargabar ƙarin tsamin dangantaka tsakanin Rasha da NATO, a daidai lokacin da yake cewa tattalin arziki da siyasa a Turai na ƙara taɓararewa.

A lokaci guda kuma, Putin ya sake yin gargadin cewa Rasha za ta yi amfani da "dukkan makaman da take da su" idan NATO ta kai mata hari.

Da yake amsa wata tambaya daga masanin harkokin siyasar Rasha, Fyodor Lukyanov, game da atisayen sojan NATO a Tekun Baltic da kuma abin da ya kira "barazana" ga yankin Kaliningrad, Putin ya ce:

"Idan aka kai hari kai tsaye daga NATO kan Tarayyar Rasha, a wannan yanayin musamman kan Kaliningrad, ko ma wasu wurare daban, to batun amfani da dukkan makaman da Rasha take da su zai kasance cikin abubuwan da za su zama dole kuma na gaggawa."

Kalaman Putin sun zo ne kwanaki kaɗan bayan ofishin jakadancin Rasha da ke Ireland ya zargi NATO da ƙokarin "toshewar iska da ruwa" ga Kaliningrad. Kaliningrad wani yankin Rasha ne da ya rabu da babban yankin ƙasar, kuma wasu ƙasashe ne ke kewaye da shi. Ofishin Jakadancin ya ce Rasha a shirye take ta kare yankin, har da amfani da makaman nukiliya idan buƙatar hakan ta taso.

Shin Rasha za ta kai hari NATO?

Wasu masana da ke bibiyar harkokin ƙasar Rasha sun yi imanin cewa tabbas aƙwai yiwuwar ɓarkewar rikici kai tsaye tsakanin Rasha da NATO, musamman a yankin ƙasashen Baltic.

A watan Satumbar 2026 wani mai sharhi kan sha'anin siyasa Vladimir Pastukhov, ya ce ra'ayinsa ya sauya cikin watanni shida da suka gabata, kuma yanzu yana ganin aƙwai yiwuwar Rasha za ta kai hari ƙasashen Baltic.

Pastukhov ya ce, duk da cewa yaƙin da Rasha ke yi a Ukraine a halin yanzu na sa irin wannan hari ya zama kamar ba shi da ma'ana ta fuskar dabarun soja, akidar siyasar Putin da manufofinsa suna sa hakan ya zama "mataki na gaba."

Sai dai, wannan ra'ayi ba shi ne mafi rinjaye tsakanin masana ba.

Masana da dama, ciki har da fitaccen mai nazarin harkokin soja Ruslan Leviev, suna ganin cewa abu ne mai wahala Rasha ta kai cikakken hari ƙasashen NATO a ƴan shekarun masu zuwa, saboda Moscow na fuskantar ƙalubalen samar da isassun dakarun da za su ci gaba da yaƙi a Ukraine.

A lokaci guda, wasu manazarta suna nazarin yiwuwar Rasha ta gudanar da ƙananan ayyukan soja a cikin yankunan Baltic maimakon mamaya mai girma.

Wani ɗan jarida mai bincike kan harkokin tsaro da ke zaune a Isra'ila, Sergei Auslander, ya yi imanin cewa aƙwai yiwuwar Rasha ta yi ɗan ƙaramar kutsen soji a Nato, amma babu batun mamaya.

Ya bayar da misalin cewa Rasha za ta iya ƙwace wani ƙaramin yanki na ƙasar Estonia mai faɗin kilomita kaɗan, ta amfani da wani dalili na siyasa ko tsaro. Haka kuma ya ce Rasha na iya ɗaukar wani mataki mai tada hankali da nufin abin da zai kira:

"Kare al'umma da ke amfani da harshen Rashanci a Narva," wani dan ƙaramin birni da ke cikin Estonia a kusa da iyakar Rasha, inda ake da yawan mazauna masu magana da harshen Rashanci.

Saboda haka, duk da cewa mafi yawan masana ba sa ganin akwai yiwuwar Rasha ta ƙaddamar da cikakken yaƙi da NATO nan kusa, akwai fargabar za ta iya gwada ƙarfin haɗin kan ƙungiyar NATO ta hanyar aiwatar da ƙaramin matakin soja ko wani aiki da zai iya haifar da rikicin siyasa da na tsaro a yankin Baltic.

..

Shin manufar ita ce ganin martanin da NATO za ta yi?

A watan Maris 2026, masana daga shirin nazari na "Re:Russia" sun bayyana cewa idan Rasha za ta aiwatar da wani ƙaramin hari ko kutse, hakan ba zai buƙaci manyan rundunonin soja ba. Sun ce babbar manufa a irin wannan mataki ba lallai ya kasance mamaye ƙasa ba, sai dai gwada haɗin kai da ƙarfin NATO tare da haifar da saɓani tsakanin ƙasashen ƙungiyar.

Rahoton ya kuma nuna cewa irin wannan hari ba lallai ne ya zo ne bayan ƙarshen yaƙin Ukraine ba, domin yana iya kasancewa wani ɓangare na rikicin da ake ciki a halin yanzu.

A cewar rahoton: "Kasawar Moscow wajen cimma manufofinta a Ukraine, ta fuskar soja ko diflomasiyya, na iya tilasta mata ta matsa lamba ga Turai ta hanyar barazanar rikicin soja mafi girma, domin ta sa Turai yin sassauci a duk wata yarjejeniya da za ta kawo ƙarshen yaƙin Ukraine."

Sai dai ba dukan masana ne suka yarda cewa ƙaramin hari ne zai zama mafita ga Kremlin ba. Sun yi gargadin cewa irin wannan dabara na iya juyawa ta zama matsala ga Rashar kanta.

Wani rahoto da jaridar Nezavisimaya Gazeta ta wallafa a watan Yulin 2026 cewa manufar "gwada juriyar NATO" tana tattare da manyan haɗurra tun daga farko. Jaridar ta ce irin wannan mataki na iya haifar da akasin abin da ake nema, inda ƙungiyar NATO za ta ƙara haɗin kai da ƙarfi maimakon ta rarrabu, sannan kuma ta mayar da martani mai tsauri.

Haka kuma, masanin siyasa Anton Barbashin, a wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Meduza da ke Latvia a watan Satumba 2026, ya nuna shakku kan hujjar cewa kai hari ga Turai zai iya haddasa rarrabuwar kai a cikinta.

A cewarsa, akwai yiwuwar akasin haka ya faru, wato ƙasashen Turai su ƙara haɗewa da ƙarfafa haɗin gwiwarsu wajen fuskantar barazana.