Cikakkun sunayen ƴantakarar gwamna na 2027 da INEC ta fitar

Wasu gwamnoni
Bayanan hoto, Gwamnoni masu ci da dama na cikin waɗanda ke takarar 2027
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Ƴan Najeriya na ci gaba da tsokaci kan sunayen ƴantakarar gwamna da hukumar zaɓen ƙasar INEc ta fitar domin fafatawa a zaɓen 2027.

INEC ta tantance tare da amincewa da Kingsley Chinda a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Rivers a zaɓen 2027, bayan ta saka sunansa cikin jerin ƴan takarar gwamnoni da ta fitar a daren Asabar.

Kingsley Ogundu Chinda tsohon jagoran yan adawa ne a Majalisar Wakilan Najeriya. sannan kuma tsohon mamba ne na jam'iyyar hamayya ta PDP.

Kingsley Chinda ya fara ɗaukar hankali watanni da suka gabata lokacin da ya zama ɗan takarar gwamnan Jihar Rivers na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), alhali jama'a sun san shi a matsayin mamba na jam'iyyar PDP.

Daga nan ne 'yan Najeriya suka fara tambayar lokacin da ya sauya sheƙa zuwa APC, da kuma ko har yanzu shi ne jagoran ƴan adawa a Majalisar Wakilai.

O.K Chinda wear white cloth with gold design button, e look inside di camera . E also wear cream colour hat wit black stripe design.
Bayanan hoto, Kingsley Chinda shi ne tsohon shugaban marasa rinjaye na Majalisar Wakilan Najeriya, ƙarƙashin jam'iyyar PDP.

Bayan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a ranar 24 ga Satumba, 2026, sunan Kingsley Chinda ya sake ɗaukar hankali, sakamakon yadda hukuncin ya mayar da wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026 da aka soke a baya.

Kotun Ƙolin ta yanke hukunci kan tanade-tanaden Dokar Zaɓen 2026 da suka shafi rijistar membobin jam'iyyun siyasa da kuma tsayar da 'yan takara.

Kwamitin alƙalai bakwai da Mai Shari'a Adamu Jauro ya jagoranta ya soke hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ya warware sashe na 77(5), 77(6), 77(7) da kuma 84(2) na dokar.

Waɗannan sassa na dokar sun shafi ƙa'idojin da suka danganci rijistar mambobin jam'iyyun siyasa, zaɓen fidda gwani kai tsaye, ko kuma tsarin maslaha wajen zaɓen yan takara da jam'iyyu ke amfani da shi.

Sakamakon wannan hukunci na Kotun Ƙoli, wata ƙungiya mai suna Association of Legislative Drafting and Advocacy Practitioners (ALDRAP) ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta hana Kingsley Chinda tsayawa takarar gwamnan Jihar Rivers a ƙarƙashin jam'iyyar APC a zaɓen 2027.

Ƙungiyar ta roƙi INEC da ta binciki "halaccin zaɓen fidda gwani na APC na takarar gwamna, sharuɗɗan da suka shafi rijistar mambobi, bayanan da APC ta miƙa wa INEC, da kuma matakan da suka dace domin aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli."

Duk da wannan ce-ce-ku-cen, jam'iyyar APC a Jihar Rivers ta bayyana cewa "ba mu da wata matsala", yayin da take mayar da martani kan sauya shekar ɗan takararta, Kingsley Chinda, zuwa jam'iyyar.

Da yake yanzu INEC ta fitar da jerin sunayen ƴan takara, hakan na nuna cewa babu wata matsala da ta hana shi tsayawa takara, kuma zai ci gaba da kasancewa ɗan takarar gwamnan Jihar Rivers na jam'iyyar APC a zaɓen shekarar 2027.

Jerin ƴantakarar gwamnan na kowace jiha

Foto mix of incumbent govnors and candidates wey Inec approve for di 2027 govnorship elections.

Abia

Opah Eric Chinemeucheya - APC

Kalu Kalu Agwu - ADC

Ijioma Uchechukwu Charles - APGA

Otti Alex Chioma - LP

Ogah Iroetugo Ndubuisi - NDC

Anosike Kelechi - PDP

Adamawa

Modibo Hammantukur Ribadu - ADC

Umaru Babangida Bajabure - ADP

Amini Ahmed Galadima - APC

Ishaku Elisha Cliff - LP

Dahiru Aishatu Ahmed - NDC

Vunobolki Maurice Michael - PDP

Akwa Ibom

John James Akpanudohedehe - ADC

Eno Umoh Bassey - APC

Jimmy Stella Monday - APGA

Mbaba Michael Bush - LP

Enyong Michael Okon - NDC

Brownson Ibanga Akpan - PDP

Bauchi

Halliru Dauda Jika -ADC

Shehu Jinda Yunusa - ADP

Abubakar Mohammed Abdullahi - APC

Aliyu Idris Muhammed - LP

Kashim Ibrahim Muhammed - NDC

Adamu Usman Ahmed - PDP

Benue

Hembe Iowase Herman - ADC

Nyimba Kwaghshir - ADP

Alia Hycinth Iormem - APC

Byuwan Mathias Terwase - LP

Shija Terhemba - NDC

Aondoakaa Michael Kaase - PDP

Borno

Babagana Buhari - ADC

Munguno Rufai Alhaji - ADP

Gubio Alhaji Mustapha - APC

Konto Umar - LP

Ibrahim Sanusi Kashim - NDC

Abba-Gana Ibrahim Baba - PDP

Cross

Otu Bassey Edet - APC

Obu Ogar Osim - LP

Archibong Arthur Javis - PDP

Joelyn Ita Hogan - Bassey - ADP

Delta

Ogboru Ovedje Great - ADC

Oborevwori Sheriff - APC

James Esther - LP

Itovwaye Chris - NDC

Mrakpor Peter - PDP

Obuseh Felix Ogechukwu - SDP

Ebonyi

Ukpai Mbah Udeh - ADC

Nwifuru Ogbonna Francis - APC

Nwodom Lucy Chinwe - APGA

Eze Oko Spledour - LP

Igwe Nwagu Palinus - NDC

Chukwuma Odii Ifeanyi - PDP

Enugu

Ocho Bodoeze Chukwuma - ADC

Mbah Peter Ndubuisi - APC

Ugwu Okwudilichukwu Chukwudera - LP

Ohaa Chiyeaka Christian - NDC

Nnaji Uchechukwu Geoffrey - PDP

Iloka Friday - SDP

Gombe

Bala Bello - ADC

Adeh Nuhu Milah - ADP

Gwamna Jamil Isyaku - APC

Muazu Zubairu Halilu - LP

Ardo Babayo Kumo - NDC

Jigawa

Sabo Mohammed Nakudu - ADC

Sulaiman Ibrahim - ADP

Namadi Umar - APC

Abdul'aziz Aminu - LP

Dutse Aminu Sani - NDC

Sule Mustapha Lamido - PDP

Kaduna

Sani Uba - APC

Isa Mohammed Ashiru - ADC

Bawa Shehu Usman - PDP

Abdulfattah Muhammad Aminu - PRP

Idris Adamu Abubakar - SDP

Rilwanu Muhammad Lawal -LP

Kano

Ibrahim Ali Amin - ADC

Muhammed Abdullahi - ADP

Yusuf Abba Kabir- APC

Santuraki Hamisu - LP

Abacha Muhammed Sani - PDP

Hussaini Bello Ado - SDP

Katsina

Ahmed Baba Kaita - ADC

Ahmed Murtala - ADP

Umar Dikko Radda - APC

Ilu-Barde Aliyu - NDC

Gard Yakubu Lardo - PDP

Kwara

Zakari Muhammed - ADC

Adeshina Ajisafe - ADP

Yakubu Danladi Salihu - APC

Abdulmunin Yinka Ajia - NDC

Kawu Suleman Bolakale - PDP

Amokanye David Adetoyese - NNPP

Kebbi

Malami Abubakar - ADC

Yahaya Ayuba - ADP

Idris Nasir - APC

Usman Aliyu - LP

Umar Faruk - SDP

Niger

Mohammed Kpataugi - ADC

Mohammed Umaru Bago - APC

Mohammed Adamu - APGA

Mohammed Usman - LP

Muhammed Yahaya Adam - NDC

Muhammed Mamman Nami - PDP

Lagos

Gbadebo Rhodes Vivour - ADC

Hamzat Kadri Obafemi - APC

Odunaike Oluwapemilerin Olurotimi - LP

Doherty Olufunsho Adeshina - NDC

Doherty Adedeji Olugbemiga - PDP

Olaniyi Olufemi - SDP

Ogun

Lawal Jimi Adebisi - ADC

Anifowose Johncrownfit Kayode - ADP

Adeola Solomon Olamilekan - APC

Ola Williams Adeyinka - SDP

Rivers

Pidomson Gabriel Baritulem - ADC

Kingsley Ogundu Chinda - APC

Boms Chima Ernest - LP

Lulu-Briggs Dumo Owukori - NDC

Ejekwu Samuel Soni - PDP

Ben-Gurion Peter - SDP

Nasarawa

Nuhu Angbazo- ADC

Christopher Mamman - ADP

Aliyu Ahmed Wadada - APC

Gaza Jonathan Gbefwi - LP

Emmanuel David Ombugado - PDP

Muhammed Abubakar Adamu - SDP

Oyo

Adegoke Taofeek Adeboyega - ADC

Alli Sharafadeen Abiodun - APC

Salami Gbolagade Tajudeen - APGA

Kareem Thompson Sola - LP

Yusuf Akim Adebola - NDC

Gbolarumi Hazeem Ola - PDP

Plateau

Sura John Sunday - ADC

Dawop Sani Sai'du - ADP

Muftwang Caleb Manasseh - APC

Nura Tanko - LP

Ropshik Kefas Wungak - PDP

Sokoto

Manir Muhammad Dan'iya - ADC

Sarkin Larabawa Nasiru - ADP

Aliyu Ahmed Sokoto - APC

Haliru Abubakar Dikko - LP

Aliyu Shamsudeen Ahmad - NDC

Abdullahi Sokoto Abubakar - PDP

Taraba

Abubakar Umar Tutare - ADC

Mamman Abubakar Mustapha - ADP

Kefas Agbu - APC

Shiddi Danjuma Usman - APGA

Nathan Sanda - LP

Yahaya Mohammed Sani - NDC

Bwacha Emmanuel - PDP

Yobe

Kassim Gaidam - ADC

Mohammed Nasiru Saleh - ADP

Wali Baba Mallam - APC

Kolomi Aji - LP

Ibrahim Mallam Shuaibu - NDC

Usman Abdullahi - PDP

Zamfara

Aliyu Bashir - APGA

Yusuf Sani - LP

Marafa Kabiru Garba - NDC

Shehu Gusau Ibrahim - PDP

Musa Hamza - SDP