'Yadda muka tara sunayen mutum 547 da ƴanbindiga suka sace a masallacin Neja'

Ƴanbidiga sun sace mutane da dama a wasu hare-hare da suka kai a wani masallaci da kasuwa a jihar Neja a watan Agusta
    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Mutanen da aka sace wa ƴan'uwansu sama da 500 a wani hari da ƴanbindiga suka kai yankin Dekara da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja, sun ce ƙididdigar da suka yi ta tabbatar musu cewa adadin waɗanda aka sace ya sha bamban da abin da gwamnati ke cewa.

A ranar 21 ga watan Agusta ne wasu ƴanbindiga sanye da kayan soji suka kai hari ƙauyukan Dekara da Gidan Zana da Kpenya da Giagbasso da Sabon Gida da kuma Masaka da kewaye.

Zuwa yanzu, mutanen sun shafe aƙalla kwanaki 40 a hannun masu garkuwa da su.

A kwanakin baya kuma, masu garkuwar sun fitar da bidiyon da ya nuna halin da waɗanda aka sace ke ciki.

Mutanen yankin sun shaida wa BBC yadda suka tantance tare da tattara sunayen mutum 547 da suka ce an sace a lokacin harin.

Yadda aka gano adadin mutanen da aka sace

Alƙaluman da mazauna garuruwan suka tattara sun nuna cewa jimillar mutum 547 aka sace a harin, inda aka sace mutum 88 a Dekara, 104 a Giagbasso, 341 a Gbenji, tara a Kpenya, sannan biyar a Gbebara.

Alhaji Zubairu Umar Dekara, Talban Dekara kuma shugaban matasan da suka jagoranci aikin tattara sunayen, ya ce tun bayan da aka kwashi mutanen suka riƙa kai koke ga gwamnati, amma har yanzu ba su ga wani gamsasshen mataki da aka ɗauka ba.

A baya, Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, ya musanta adadin da ake yaɗawa, inda ya bayyana cewa an "kambama" lamarin.

A cewarsa, mutum 63 ne aka sace, ciki har da 33 daga wani masallaci da 30 daga kasuwa. Ya kuma ce an kashe mutum uku, yayin da aka ceto mutum 14.

Sai dai Alhaji Zubairu ya ce sun tabbatar adadin ya haura 500 ne bayan da suka yi tattaki gida-gida domin tattara bayanan mutanen da aka sace.

"Mun tattara sunayen mutum 547. Bayan mutane sun koma gari, kowa ya zo aka haɗu aka yi lissafi. Kowa ya faɗi mutum nawa aka ɗaukar masa, daga nan ne aka gano adadin mutanen da aka kwashe," in ji shi.

Ya ce ba su da wani dalilin ɓoye gaskiya ko kambama adadin, musamman ganin cewa shi kansa mahaifinsa da surukinsa na cikin waɗanda aka sace.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shi ma Habib Zubairu, ɗaya daga cikin shugabannin yankin, ya ce tun daga bidiyon da ƴanbindigar suka fitar ne suka fara fahimtar girman lamarin.

"Da farko ba mu san mutum nawa aka sace ba. Sai da ƴanbindigar suka ankarar da mu bayan fitar da bidiyo suka ce sun kama sama da mutum 500. Daga nan ne muka ce kowa ya kawo sunayen mutanensa," in ji shi.

Baya ga waɗanda aka sace, mazauna yankin sun ce mutum 39 sun rasa rayukansu a yayin harin, inda aka "yanka su".

Saboda haka, Habib ya ce suna roƙon gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa domin ceto mutanen, yana mai cewa sun miƙa jadawalin sunayen waɗanda aka sace ga hukuma, amma har yanzu ba su ga wani abin a zo a gani ba.

Shi ma wani mazaunin Dekara, wanda mahaifinsa na cikin waɗanda aka sace, ya ce tun bayan aukuwar lamarin iyalansu ke cikin halin damuwa.

Ya ƙara da cewa abin da ya fi ci musu tuwo a ƙwarya shi ne yadda suke ganin ana ƙoƙarin musantawa ko rage girman matsalar maimakon a mayar da hankali kan ceto mutanen.

Ya ce iyalan waɗanda aka sace na ci gaba da rayuwa cikin fargaba da rashin tabbas, yayin da suke jiran duk wani mataki da zai kai ga dawo da ƴan'uwansu gida lafiya.

Jihar Neja

Mutane nawa suka gudu daga hannun ƴanbindigar?

Mazauna yankin sun ce an samu wata mata da ta tsere daga hannun ƴanbindigar tare da wasu yara biyu bayan ta shafe kwanaki a tare da su.

Habib Zubairu, ɗaya daga cikin shugabannin yankin, ya ce matar na da ciki lokacin da aka sace ta, kuma ta haihu ne tana hannun ƴanbindigar.

A cewarsa, bayan haihuwar ne matar ta shiga wani hali na rashin lafiya, lamarin da ya sa ƴanbindigar suka rage sanya ido a kanta. Sai dai ya ce jaririn da ta haifa bai rayu ba.

"Daga baya, da ta samu sauƙi kuma ta ga ba a tsaurara mata tsaro ba, sai ta tsere," in ji Habib.

Ya ce a yayin da take ƙoƙarin tserewa ne ta ci karo da wasu ƙananan yara da su ma aka bari a wurin, inda ta tafi da su domin neman mafita.

Habib ya ce matar ta shafe kwanaki uku tana tafiya cikin daji kafin daga bisani ta isa wani gari mai suna Garoji.

Bayan dawowarta ta ba su labarin halin da mutanen ke ciki, wanda ya bayyana a matsayin abin tausayi da ɗaga hankali.

"Abin da ta ba mu labari game da halin da mutanen ke ciki ba abu ne mai daɗin ji ba," in ji shi.

Sunayen wasu daga cikin waɗanda aka sace da mazauna garuruwan suka tattara
Bayanan hoto, Sunayen wasu daga cikin waɗanda aka sace da mazauna garuruwan suka tattara

Ko ƴan bindigar sun tuntuɓe su?

Mazauna yankin sun ce har yanzu ba su samu damar wata tattaunawa da masu garkuwa da mutanen ba, duk da cewa sama da wata guda ke nan da sace su.

Habib ya ce tun bayan bidiyon da ƴanbindigar suka fitar kwanaki uku bayan harin, ba su sake samun wani bayani kan halin da ƴan'uwansu ke ciki ba.

"Har yanzu ba su ce mana komai ba tun lokacin da suka fitar da wannan bidiyon," in ji Habib Zubairu.

Ya ce iyalan waɗanda aka sace na ci gaba da shiga cikin damuwa da fargaba, musamman ganin yadda aka kwashe kwanaki da dama ba tare da an samu wani ci gaba a lamarin ba.

Habib ya ƙara da cewa mazauna yankin na tsoron kada a mance da halin da mutanen ke ciki, inda suke fatan gwamnati da jami'an tsaro su ƙara kaimi wajen ganin an kuɓutar da su.

A wane hali mutanen da aka sace ke ciki?

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa matar da ta tsere daga hannun ƴanbindigar ta ba su labarin mawuyacin halin da mutanen ke ciki, inda ta ce yara na ta rasa rayukansu sakamakon wahala da kuma matsanancin yanayin da suke fuskanta.

Ya ce har yanzu ba a san ainihin adadin mutanen da suka rage a hannun masu garkuwa da su ba.

"Mutanen suna shan wahala, yara na ta mutuwa, sannan akwai marasa lafiya da tsofaffi a cikinsu," in ji shi.

Alhaji Zubairu ya ce matar ta shaida musu cewa waɗanda aka sace ba sa samun kulawar da ta dace.

Sai dai ya ce an tura jami'an tsaro na sojoji zuwa garin Dekara, duk da cewa har yanzu iyalan waɗanda aka sace na jiran ganin wani ci gaba a ƙoƙarin ceto su.

Abin da gwamnati ta ce

Gwamnan jihar Neja, Umaru Muhammad Bago
Bayanan hoto, Gwamnan jihar Neja, Umaru Muhammad Bago

BBC ta tuntubi gwamnatin Jihar Neja domin jin martaninta kan ƙorafe-ƙorafen mazauna yankin, amma kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Obed Nuhu, bai amsa kiran waya da aka yi masa ba.

Sai dai a kwanakin baya, kakakin rundunar ƴansandan jihar, Wasiu Abiodun, ya shaida wa BBC cewa maharan sun kashe fiye da mutum 40.

Amma ya ce rundunar ba za ta iya tabbatar da ainihin adadin mutanen da aka kashe ko kuma waɗanda aka yi garkuwa da su ba.

A cewarsa, ranar 21 ga watan Agustan 2026 ne rundunar ta samu rahoton cewa da misalin ƙarfe biyu na rana wasu da ake zargin ƴan ta'adda ne sun kai hari ƙauyukan Gidan Zana da Kpenya, bayan sun bi ta yankin Dekara da ke ƙaramar hukumar Borgu.

Ya ce maharan sun kai hari wani masallaci da ke Kpenya, inda suka yi garkuwa da mutane masu yawa, yayin da wasu suka tsere zuwa cikin daji domin tsira da rayukansu.

Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin a ƙara tura jami'an tsaro yankin domin ƙaddamar da aikin ceto mutanen da aka sace.