Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 20/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 20/11/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • INEC
  • Atiku
  • Shugaba Tinubu
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Ƴar Arewan da ke buga wa Najeriya ƙwallo
  • waya
  • Gwamna Adeleke na Accord
  • Jihohi masu talauci
  • Buba Galadima

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Imam Saleh

  1. Muna da cikakken iko da mashigar Hormuz - Trump

    Amurka

    Donald Trump ya mayar da martani ga wani ɗan jarida da ya tambaye shi kan abin da ya kira "rashin jin daɗinsa" game da kalaman mataimakinsa, J.D. Vance, bayan shan kaye da jam’iyyar Republican ta yi, da kuma ikirarinsa cewa yaƙin da aka yi da Iran ya taka rawa wajen sakamakon zaɓen.

    Trump ya ce: “Magana ce mai kyau. Tabbas yaƙin ya shafi farashin makamashi, amma ba kamar yadda ake zato ba. Wannan yaƙi ne da babu makawa, kuma da za a mayar da hannun agogo baya, da zan sake ɗaukar wannan mataki (na yaƙin Iran).”

    Ya ci gaba da cewa: “Yaƙin ya ƙara farashi da kuɗin fetur, amma ba kamar yadda na yi zato ba. Na yi tunanin cewa farashin ɗanyen mai zai kai dala 300 kan kowace ganga. Amma yanzu yana kusan dala 80 ne kawai kan kowace ganga.

    "A gaskiya, a makon da ya gabata mun kafa tarihin yawan man da ya ratsa ta mashigar Hormuz. Tarihi ne da ba a taɓa yin irinsa ba. Rundunar ruwanmu ta kafa katanga ta tsaro. Rundunar ruwanmu abin alfahari ce. Sojojinmu ma abin alfahari ne. Muna da cikakken iko a mashigar Hormuz.”

    Trump ya ƙara da cewa: “Ina ganin zan iya magana a madadin kowa, duk da cewa ba na son yin magana a madadin wasu. Mutanen da nake aiki tare da su suna da ’yancin bayyana ra’ayinsu. Amma na san jami’an Iran, kuma a gaskiya suna yin abubuwan da ba a saba gani ba. Sun shafe shekaru 51 suna aikata haka, ba shekaru 47 ba.

    "Lokacin da muka fara magana kan wannan batu shekaru 47 ne, amma idan aka duba abubuwan da suka faru tsawon shekaru, ko batun kai hari ga ofishin jakadancin Amurka ko kuma kashe Amurkawa da yawa, za a iya cewa sun fara wannan rikici shekaru 51 da suka gabata.”

  2. An kashe kusan mata 600 a Afirka Ta Kudu cikin watanni uku

    Mata

    Kusan mata 600 aka kashe a Afirka Ta Kudu tsakanin Yuli da Satumbar wannan shekara, kamar yadda sabbin ƙididdigar laifuka na ƙasar suka nuna.

    Wannan adadi ya haɗa da mata 13 waɗanda aka tsinci gawarwakinsu da raunuka a jikinsu kuma ba cikakkun tufafi a jikinsu ba, an yar da su a wuraren jama'a a ciki da kewayen birnin Johannesburg.

    Waɗannan kashe-kashen sun tayar da hankalin al'umma a faɗin ƙasar, lamarin da ya sa ƴansanda suka fuskanci matsin lamba domin gano waɗanda suka aikata laifukan. Afirka Ta Kudu na daga cikin ƙasashen da ke da mafi girman yawan cin zarafin mata da kashe-kashe a duniya.

    A sabon lamarin da ya girgiza ƙasar, an harbe mata biyar da ƙaramin yaro ɗan shekara guda zuwa biyu har lahira a lardin Free State a farkon wannan makon.

    Sabbin alƙaluman laifukan da aka fitar a ranar Juma’a sun nuna cewa an kashe mata 581 tsakanin Yuli da Satumba a faɗin ƙasar, ciki har da mata 131 a lardin Gauteng, wanda ya haɗa da birnin Johannesburg.

    Haka kuma alƙaluman sun nuna ɗan raguwar yawan kashe-kashen baki ɗaya.

    Ƴansanda sun ce an samu kashe-kashe 5,590 a wannan lokaci, wato mutum 204 ƙasa da adadin da aka samu a daidai wannan lokacin na bara. Duk da haka, hakan na nufin cewa ana kashe kusan mutum 60 a kowace rana a ƙasar.

    Ba a tabbatar ko adadin matan da aka kashe ya ƙaru ko ya ragu ba, saboda ‘yan sanda sun daina fitar da irin waɗannan alkaluma a baya-bayan nan. Sun ce hakan ya faru ne sakamakon abin da suka bayyana a matsayin "manyan matsaloli da rashin daidaito" a cikin bayanan ƙididdigar.

    Muƙaddashin ministan ƴansanda, Firoz Cachalia ya ce akwai buƙatar a ƙara "ƙaimi wajen kare cin zarafin mata da ƙananan yara."

  3. Amurka ta kashe dala biliyan 48 a yaƙin Iran - Pentagon

    Amurka

    Wani babban jami’in ma’aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ya ce yaƙin da aka yi da Iran ya laƙume kusan dala biliyan 50 daga kuɗin sojojin Amurka.

    Arthur Miller, wanda ke kula da harkokin saye da samar da kayan aikin tsaro, ya ce wannan adadi ya haɗa da kuɗin makamai da harsasai, kuɗin maye gurbin kayan aiki da suka lalace ko aka yi amfani da su, da kuma kuɗaɗen gudanar da ayyukan soja.

    Sai dai ya bayyana cewa wannan adadi bai haɗa da asarar da sansanonin sojojin Amurka da ke yankin Gulf suka yi ba. Wasu daga cikin sansanonin sun fuskanci munanan hare-haren jirage marasa matuƙa (drones) da makamai masu linzami daga Iran a yayin yaƙin, wanda yanzu ya shafe fiye da watanni tara yana gudana.

    Mista Miller ya yi wannan bayani ne ga ‘yan majalisar dokoki a lokacin wani zaman sauraren ra’ayi da aka shirya dangane da naɗin da aka yi masa a matsayin Mataimakin Sakataren Rundunar Sojin Ruwa ta Amurka mai kula da harkokin kuɗi da gudanarwa.

  4. Yarjejeniya tsakanin ƙasashen turai za ta rage tsadar rayuwa - Birtaniya

    Birtaniya

    Firaministan Birtaniya ya yaba da yarjejeniyar da aka cimma kan ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da Tarayyar Turai (EU), yana mai cewa yarjejeniyar tana da matuƙar muhimmanci.

    Andy Burnham ya ce yarjejeniyar na iya rage tsadar rayuwa tare da rage cikas da ƙa'idojin da suka shafi harkokin kasuwanci a ƙasarsa da kuma a faɗin nahiyar Turai.

    Tattaunawar da aka yi a Brussels ta haifar da sabbin yarjeniyoyi kan ƴancin zirga-zirga ga matasa, dokokin da suka shafi kasuwancin abinci. Sai dai ba a cimma matsaya ba kan kuɗaɗen karatu ga ɗaliban Turai da ke karatu a jami'o'in Birtaniya.

    Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta ce yarjejeniyar ta zama wani muhimmin sauyi a dangantakar da ke tsakanin EU da Birtaniya.

    Sai dai wasu jami'an diflomasiyyar Tarayyar Turai sun yi gargadin cewa rashin cimma yarjejeniya kan kuɗaɗen karatu a watanni masu zuwa na iya hana aiwatar da sauran ɓangarorin yarjejeniyar da aka cimma yau Juma'a.

    Birtaniya ta kaɗa ƙuri'ar ficewa daga Tarayyar Turai shekaru goma da suka gabata, matakin da ake ganin ya janyo wa ƙasar asarar biliyoyin daloli ta fuskar haɓakar tattalin arziki.

  5. Mutum huɗu sun rasu bayan kifewar kwale-kwale a Najeriya

    Mutum huɗu ciki har da yara biyu sun mutu bayan wani jirgin ruwa da ke ɗauke da masu halartar jana'iza ya kife a jihar da ke kudancin Najeriya, kamar yadda ƴansanda suka bayyana.

    An ceto mutum 24, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin nema da ceto domin gano wasu fasinjojin da har yanzu ba a tabbatar da halin da suke ciki ba, a cewar sanarwar ƴansanda.

    Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe agogon Najeriya (10:00 GMT) a ranar Juma’a a mashigar ruwa tsakanin al’ummomin Oweikorogha da Otuan da ke ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu.

    Jirgin ruwan na kan hanyarsa daga Ayama zuwa Ukubie domin halartar jana’iza lokacin da aka ce ya samu matsalar na’ura.

    Rahotanni sun ce wasu daga cikin fasinjojin sun roƙi mai tuƙin jirgin ya karkata zuwa bakin kogi bayan matsalar ta bayyana, amma ya ci gaba da tafiya kafin jirgin ya kife, kamar yadda binciken farko na ƴansanda ya nuna.

    An kai gawarwakin mutanen huɗu da aka gano zuwa ɗakin ajiyar gawa na Asibitin Tarayya da ke Yenagoa, babban birnin jihar.

    Daga cikin mutum 24 da aka ceto, an kai mutum 19 zuwa Asibitin Ayama, yayin da mutum biyar da suka samu raunuka aka kai su Asibitin Family Care da ke Yenagoa domin jinya. Sauran waɗanda aka ceto sun koma garuruwansu, kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.

    Mai tukin jirgin, wanda aka bayyana sunansa da Omovie kawai, ya tsere daga wurin da lamarin ya faru, sannan ƴansanda sun ce an tsare manajan jirgin domin ci gaba da bincike.

    A Najeriya, irin waɗannan hadurran jiragen ruwa na yawan faruwa, galibi sakamakon loda jirgi fiye da ƙa’ida, rashin kula da jiragen yadda ya kamata, da kuma Ƙin bin dokoki.

  6. 'Burin mayaƙan JNIM shi ne kifar da gwamnatocin Nijar da Mali da Burkina Faso'

    AES

    Ƙungiyar International Crisis Group (ICG) ta buƙaci gwamnatocin sojin Mali, Nijar da Burkina Faso su shiga tattaunawa da ƙungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) mai alaƙa da al-Qaeda, tana mai bayyana cewa cimma matsaya ta hanyar tattaunawa ita ce hanya mafi sauƙi ga ɓangarorin da ke rikici da kuma miliyoyin mazauna yankin Sahel, kamar yadda gidan rediyon Faransa RFI ya ruwaito a ranar 20 ga Nuwamba.

    Rahoton ya ce burin JNIM na faɗaɗa tasirinta a yankin ya ƙara bayyana ƙarara, musamman bayan hare-haren da ta kai ranar 25 ga Afrilu kan manyan birane bakwai na Mali, waɗanda suka yi sanadin mutuwar Ministan Tsaro, Janar Sadio Camara, tare da jefa gwamnatin riƙon-ƙwarya cikin wani mawuyacin hali.

    Rahoton ya kuma ƙara da cewa JNIM na neman kifar da gwamnatocin sojin ƙasashen yankin, tare da ƙoƙarin jawo hankalin masu ilimi da shugabannin siyasa da ke gudun hijira.

    Sai dai gwamnatocin sojin sun ci gaba da matsa lamba ta fuskar soja, inda suka mayar da hankali kan tabbatar da tsaron birane, da kuma rakiyar ayarin motocin dakon man fetur.

    ICG ta ce samun nasarar kammala rikicin ta hanyar ƙarfin soja kaɗai ba abu ne mai yiwuwa ba bayan sama da shekaru goma ana gwabza faɗa. Saboda haka ta bukaci gwamnatocin sojin su fara tattaunawa da JNIM yayin da suke ci gaba da matsin lambar soja.

    Kungiyar ta kuma yi kira ga JNIM da ta yanke alakarta da al-Qaeda tare da amincewa da ci gaba da wanzuwar cibiyoyin gwamnatin farar hula da tsarin jamhuriya.

    JNIM ta faɗaɗa ayyukanta a Mali, Burkina Faso da Nijar, kuma yanzu tana nuna alamun maida hankali kan ƙasashen gabar tekun Yammacin Afirka, musamman Benin da Togo.

  7. Hare-haren Rasha sun kashe aƙalla mutum 8 a Ukraine

    Rasha

    Aƙalla mutum takwas aka kashe a hare-haren tsakar dare da Rasha ta kai kan wasu wurare a sassan Ukraine.

    Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce Rasha ta harba makamai masu linzami fiye da 110 a abin da ya kira ɗaya daga cikin hare-hare mafi girma tun bayan soma yaƙin.

    Makamai masu linzami sun faɗa kan wasu gadoji a Kyiv, babban birnin ƙasar yayin da wasu wuraren da harin ya shafa suka haɗa da wata majami'a da kuma ofisoshin jami'an diflomasiyya.

    Wakiliyar BBC ta ce wuraren da aka fi kai wa harin su ne gadoji a nan Kyiv da suka tashi daga kogin Dnipro da ya haɗa ɓangarorin birnin.

    Poland ta ce jirage marasa matuƙa na Rasha da wani makami mai linzami ya sun ƙetara sararin samaniyarta. Firaminista Donald Tusk ya ce hakan da alama ba kuskure ba ne.

  8. Dole mu haɗa kai domin magance matsalar tsaro - Shugaban Senegal

    Senegal

    Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya yi kira a ranar 19 ga Nuwamba da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar soji tsakanin ƙasashen Yammacin Afirka domin tunkarar ƙalubalen da suka haɗa da "ta'addanci" da ƙaruwar safarar haramtattun kayayyaki da rashin zaman lafiya, kamar yadda jaridar L'Observateur mai zaman kanta ta ruwaito a ranar 20 ga Nuwamba.

    Ya ce: "Tsaron Yammacin Afirka ba zai iya ci gaba da dogaro da tsarin tsaron kowace ƙasa daban-daban ba. Lokaci ya yi da za a haɗa ƙarfi da ƙarfe tare da amfani da ƙarfi da damar da yankin ke da su."

    Ya kuma buƙaci a ƙara inganta hangen nesa da ƙarfin soji, da musayar bayanan sirri ta hanyoyin da suka dace, tare da gudanar da atisayen hadin gwiwa akai-akai.

    Faye ya bayyana hakan ne a babban birnin ƙasar, Dakar, yayin bikin ranar rundunar sojin ƙasar.

    Yayin da yake jaddada muhimmancin kare haɗin gwiwar yankin duk da sauye-sauyen siyasa da na hukumomi da ake fuskanta, Faye ya tunatar da irin dogon tarihin da Senegal ke da shi na aiki tare da sojojin ƙasashe abokan hulɗa wajen hana ɓarkewar rikice-rikice da kuma magance su a faɗin yankin.

    A cewarsa, irin waɗannan gogewa da aka samu tare za su iya zama ginshiƙi wajen sake gina haɗin gwiwa mai karfi, wanda zai dogara kan zurfafa fahimtar sabbin barazanar tsaro da kuma samar da hanyoyin ɗaukar matakai cikin gaggawa.

    Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da manyan hafsoshin sojin kungiyar Ecowas suka gudanar da taro a Dakar domin tattauna hadin gwiwar tsaro, taron da kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar ba su halarta ba, bayan da suka fice daga kungiyar a watan Janairun 2025.

  9. Ana fargabar mutum 30 sun mutu sakamakon kifewar kwale-keale a Najeriya

    Rahotanni na cewa akalla mutum 30 sun mutu, yayin da wasu 300 suka ɓace bayan wani jirgin ruwa ɗauke da masu makoki ya kife a kusa da garin Oweikorogha, da ke ƙaramar hukumar Ijaw ta kudu, ta jihar Bayelsa, ranar Juma'a.

    Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa masu makokin na kan hanyarsu ta zuwa jana'iza a wani gari da ake kira Ukubie, lokacin da abin ya faru.

    An ce masu makokin sun yi amfani da wani babban jirgin ruwa wajen tafiya jana'izar, amma ya ɗauki fasinjoji fiye da ƙarfinsa kafin ya kife.

    Har yanzu ba a tabbatar da ainihin adadin mutanen da ke cikin jirgin da waɗanda suka ɓace ba, amma ana ci gaba da aikin ceto, inda mazauna yankin da sauran al'umma suka haɗa kai wajen neman waɗanda suka tsira.

    Rahotanni sun nuna cewa kafin faruwar lamarin wasu fasinjojin sun ba da shawarar cewa jirgin ya tsaya a Oweikorogha domin rage cunkoson mutanen da ke cikinsa, saboda yawan fasinjojin da ke cikin jirgin.

  10. Ƙasashen Larabawa sun gargaɗi fararen hula su fice daga yankin mayaƙan Houthi

    Houthi

    Ƙawancen ƙasashen Larabawa ƙarƙashin jagorancin Saudiyya da ke yaƙi da ƴan tawayen Houthi a Yemen ya gargaɗi farar hula da su fice daga tashar jiragen ruwa ta Hodeidah, bayan shafe makonni ana kai hare-hare a yankin.

    Cikin ƴan mintuna bayan saƙon da Riyadh ta wallafa a shafukan sada zumunta, ƴan Houthi masu samun goyon bayan Iran suka yi barazanar mayar da martani idan Saudiyya ta kai hari kan muhimmiyar tashar jiragen ruwan da ke gaɓar Tekun Maliya.

    Sun kuma gargadi mutane da su fice daga tashoshin jiragen ruwa na Saudiyya, tare da yin kira ga kamfanonin jigilar kaya ta ruwa da su cire jiragensu daga Tekun na Maliya.

    Ɓangarorin biyu sun ci gaba da kai wa junansu hare-hare. Ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta ya ce ya kakkabo jirage marasa matuƙa biyu da kuma makami mai linzami.

  11. Ƙasashe 10 da za su fi yawan Musulmai a duniya nan da 2050

    mata

    Musulmi na kan hanyar zarce Kiristoci a yawan mabiyansu a duniya nan da shekarar 2035, kamar yadda hasashen da Cibiyar Bincike ta Pew Research da ke Amurka (Pew Research Center) ta fitar ya nuna.

    Sai dai addinan biyu za su ci gaba da ƙaruwa a yawan mabiya.

    Tsakanin shekarar 2020 da 2070, ana sa ran yawan Musulmi zai ƙaru da kaso 80 cikin 100, daga biliyan 2.02 zuwa biliyan 3.64.

    A gefe guda kuma, ana hasashen yawan Kiristoci zai ƙaru da kaso 30 cikin 100 zuwa biliyan 2.96, daidai gwargwadon yadda ake sa ran yawan al'ummar duniya zai ƙaru.

    Rahoton ya ce ana sa ran Musulmi za su kasance rukuni mafi saurin ƙaruwa cikin manyan addinan duniya.

    Sai dai ana sa ran mabiya addinin Hindu da Yahudawa za su ƙaru ne a hankali fiye da yadda yawan al'ummar duniya ke ƙaruwa.

    Haka kuma ana hasashen yawan mabiya addinin Buddha da mutanen da ba su da wani addini zai ragu.

  12. Ƴansandan Afirka ta Kudu sun kama mutum 8 da zargin kashe mata 12

    Afirka ta Kudu

    Ƴansanda a Afirka ta Kudu sun ce sun kama mutum takwas da ake zargi da hannu a kisan mata goma sha biyu da aka yi a baya-bayan nan a kusa da Johannesburg.

    Masu bincike sun bayyana kamen a matsayin babban ci gaba a binciken da ake game da lamarin, wanda ake ɗauka a matsayin cin zarafin da ake yi wa mata.

    Afirka ta Kudu na daga cikin ƙasashen da aka fi samun yawan kashe-kashe a duniya. Sabbin alƙaluman hukuma sun nuna cewa kusan mutum sittin ake kashewa a kowace rana daga Yuli zuwa Satumba.

  13. An kama mutum takwas kan zargin kisan wasu 12 a Afirka ta Kudu

    'Yan sanda a Afirka ta Kudu sun ce sun kama mutum takwas da ake zargi da hannu a kisan mata 12 da aka yi a baya-bayan nan a kusa da Johannesburg.

    Masu bincike sun bayyana kamen a matsayin babban ci gaba a binciken da ake game da lamarin, wanda ake ɗauka a matsayin cin zarafin da ake yi wa mata.

    Afirka ta Kudu na daga cikin ƙasashen da aka fi samun yawan kashe-kashe a duniya.

    Sabbin alƙaluman hukuma sun nuna cewa kusan mutum sittin ake kashewa a kowace rana daga Yuli zuwa Satumba.

  14. Houthi ta zargi Saudiyya da kai hari kan jirgin fararen hula

    Jirgin ruwa

    Ƴan tawayen Houthi na Yemen sun zargi Saudiyya da kai hari kan wani jirgin ruwa ɗauke da fararen hula, wanda suka ce ya yi sanadin mutuwar mutum 19, a yayin da yaƙin basasar Yemen ya sake ƙara ƙamari bayan wani lokaci na kwanciyar hankali.

    Mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar Houthi, Anis Asaby, ya yi Allah wadai da harin.

    "Jiragen yaƙin ƙasar sun kai hari kan wani jirgin ruwa na fararen hula da ke ɗauke da fiye da ƴan gudun hijira 25, lamarin da ya kashe mutum 19 tare da jikkata wasu huɗu," in ji shi.

    "Kai hari kan fararen hula da ƴan gudun hijira babban laifin yaƙi ne, kuma keta dokokin jinƙai da na kare haƙƙin bil'adama na ƙasa da ƙasa ne ƙarara."

    Haka kuma, mai magana da yawun ma'aikatar lafiya ta Houthi ya wallafa a shafinsa na X cewa jirgin ruwan ya tashi ne daga yankin Ras al-Ara, yana kan hanyarsa ta zuwa birnin Hays da ke kudancin Yemen.

  15. ICG ta yi kira ga ƙasashen Sahel su yi sasanci da JNIM

    Ƙungiyar International Crisis Group (ICG) da ke Sanya idanu kan rikice-rikice a duniya ta buƙaci gwamnatocin mulkin soja a ƙasashen Mali da Nijar da kuma Burkina Faso su buɗe tattaunawar siyasa da ƙungiyar JNIM mai alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda.

    Ƙungiyar ta ce cimma yarjejeniya ta hanyar tattaunawa ita ce zaɓi mafi inganci ga ɓangarorin da ke rikici da kuma miliyoyin al'ummar yankin Sahel da tashe-tashen hankulan suka shafa.

    Ƙungiyar ICG ta bayyana cewa warware rikicin ta hanyar sulhu da tattaunawa na iya taimakawa wajen rage asarar rayuka da kuma wahalhalun da fararen hula ke fuskanta a yankin.

    Cikin wani rahoto da ta fitar, ICG ta ce faɗaɗar ayyukan ƙungiyar JNIM da tasirinta a yankin ya ƙara bayyana a fili, musamman bayan hare-haren da ta kai ranar 25 ga Afrilu kan manyan birane bakwai na Mali, waɗanda suka yi sanadin mutuwar Ministan Tsaron ƙasar, Janar Sadio Camara, tare da jefa hukumomin riƙon ƙwarya cikin wani hali da rahoton ya bayyana da ‘’matsi’’.

    Rahoton ya ƙara da cewa JNIM na kira a fili da a hambarar da gwamnatocin mulkin soja na ƙasashen Sahel, tare da neman goyon bayan masu ilimi da shugabannin siyasa da ke gudun hijira.

    ICG ta ce JNIM ta faɗaɗa ayyukanta daga sansanoninta da ke Mali zuwa ƙasashen Burkina Faso da Nijar, kuma yanzu da alama tana ƙara karkata hankalinta zuwa ƙasashen yammacin Afirka da ke gabar teku, musamman Benin da Togo.

    Zuwa yanzu dai hukumomin ƙasashen uku basu mayar da martani ba game da wannan kira.

    Amma wani bayani daga ƙasashen na cewa suna ci gaba da matsa mata lamba ta fuskar soji ga ƙungiyar, inda suka mayar da hankali kan kare manyan birane tare da ƙoƙarin rusa shigayen da ƙungiyar ke kafawa don farmakar ayarin motocin dakon man fetur a yankin.

    To sai dai a cewar ICG samun nasara ta hanyar ƙarfin soja na ƙara rasa tasiri cikin fiye da shekara 10 na rikicin.

    Kan haka ne ta buƙaci gwamnatocin mulkin sojan su shiga tattaunawa da JNIM, tare da ci gaba da matsin lambar soji a lokaci guda.

    Ƙasahen na yankin uku sun jima suna fukantar matsalar ayyukan ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi, wani abu da suke kafa hujja da shi a lokacin juyin mulkin sojin ƙasashen.

    Bayan juyin mulkin sojin ƙasashen sun kori dakarun ƙasashen waje da ke yaƙi da masu ikirarin jihadi a ƙasashen, wani da masana tsaro ke alaƙanta da ƙaruwar ayyukan ƙungiyoyin a yankin.

  16. Dakarun Iraƙi na shirin farmakar ƙungiyar kataib Hezbollah a ƙasar

    Dakarun tsaron Iraƙi sun shiga wani yanki da ke kudancin Baghdad wanda ƙungiyar masu ɗauke da makamai mai samun goyon bayan Iran, Kataib Hezbollah, ke iko da shi.

    Wani kakakin rundunar sojin ƙasar ya ce dakarun sun shiga yankin Jurf al-Sakhar ne a ranar Juma'a bisa umarnin Firaministan Iraki, Ali al-Zaidi.

    Gwamnatin Iraki ta zargi Kataib Hezbollah da gudanar da wata harkar safarar ɗanyen mai ta haramtacciyar hanya, wadda ta yi sanadin asarar kuɗaɗen shiga na daruruwan miliyoyin daloli ga gwamnati.

    Sai dai ƙungiyar ta musanta wannan zargi.

    Kataib Hezbollah, wadda ke cikin ƙungiyoyin mayaƙa mafi ƙarfi masu goyon bayan Iran a Iraki, ta kasance mai iko da yankin Jurf al-Sakhar tun bayan da aka ƙwato shi daga hannun mayaƙan ƙungiyar Da'ish (Islamic State) kimanin shekara goma da suka gabata.

  17. Ƴan ƙasarmu na da ra'ayin mu mallaki makamin nukiliya - Iran

    Ɗan majalisar dokokin Iran, kuma mamba kwmaitin tsaron ƙasar, Ahmad Bakhshish Ardestani, ya ce wani ɓangare na al'ummar ƙasar da kuma ra'ayin jama'a sun nuna buƙatar ƙasar na mallakar makamin nukiliya.

    A cewarsa, matsin lambar da Amurka ke yi wa Iran ya sa batun ƙera makamin nukiliya ya ƙara fitowa fili a tattaunawar siyasar ƙasar, kuma da alama wani ɓangare na jama'a na nuna goyon baya ga irin wannan sauyi.

    Ɗan majalisar ya kuma jaddada cewa akwai wasu muhimman la'akari da ya kamata a yi dangane da wannan batu, yana mai nuni da dangantakar Iran da ƙasashe irin su China da Rasha.

    Mista Ardestani ya ce:

    "Waɗannan ƙasashe na ba Iran shawarar ta yi taka-tsantsan sosai, kuma kada ta ɗauki irin wannan mataki a halin yanzu."

    Ya kuma ce masu goyon bayan Iran ta mallaki makamin nukiliya na ganin cewa samun irin waɗannan makamai zai iya ƙara wa ƙasar ƙarfin daƙile barazana daga abokan gaba.

    A cikin ƴan makonnin da suka gabata, wasu jami'an siyasa da na soja da na addini a Iran sun fara tattauna yiwuwar sake nazarin manufofin nukiliyar ƙasar, har ma da yiwuwar ficewa daga yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya ta duniya (NPT).

    Batun ya zama ɗaya daga cikin muhimman kuma mafi jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar Iran a wannan lokaci.

  18. Harin Houthi ya lalata gini mafi tsayi a babban birnin Saudiyya

    Gini

    Saudiyya ta tabbatar da cewa harin mayaƙan tawayen Houthi ya lalata gini mafi tsayi a Riyadh, babban birnin ƙasar.

    Hukumar Kare Farar Hula ta Saudiya ta ce wasu benaye na ginin, wanda ke ɗauke da hedikwatar asusun babban birnin ƙasar, sun samu lahani.

    Sa'o'i kaɗan da suka gabata, kakakin ƙawancen sojojin Saudiya ya ce tarkacen wani makami mai linzami da aka yi nasarar kakkaɓowa ne ya haddasa ɓarnar da aka gani a Riyadh.

    A lokaci guda kuma, shaidun gani da ido sun ce sun ga alamun ɓarna a hasumiyar.

    A kwanakin baya-bayan nan, hare-haren da ƴan tawayen Houthi na Yemen ke kai wa biranen Saudiya sun ƙaru.

    Mintuna kaɗan bayan bayyana wannan labari, ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar da sanarwar Allah wadai da abin da ta kira "ci gaba da kai hare-hare" kan Masarautar Saudiyya, waɗanda suka haifar da ɓarna a babbar cibiyar kasuwanci ta Sarki Abdullah da ke Riyadh.

    Haka ma ma'aikatar harkokin wajen Kuwait ta bayyana harin a matsayin "keta hurumin ikon mallakar ƙasa na Masarautar Saudiyya a fili."

  19. Ba gaggawa nake don cimma matsaya da Iran ba - Trump

    Trump

    Shafin labarai na Axios ya rawaito cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ba gaggawa yake kan cimma matsaya da Iran ba.

    A cewar wakilin shafin, Barak Ravid, Mista Trump ya ce:

    "Sai mun ga abin da zai faru a farkon shekara mai zuwa."

    Wannan na zuwa ne bayan rahotannin da suka gabata sun ce ana sa ran Mista Trump zai tattauna batun Iran yayin ganawarsa da shugabannin China da Rasha a taron ƙasashe uku da za a gudanar a Shenzhen.

  20. Yaƙin Iran ya laƙume mana sama da dala biliyan 48 - Amurka

    Kudi

    Wani jami'in ma'aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ya sanar a ranar Alhamis cewa kuɗin da aka kashe a yaƙin da ake yi da Iran yanzu ya haura dala biliyan 48 tun bayan da rikicin ya fara a ƙarshen watan Fabrairu.

    "Wannan adadi ya haɗa da kuɗin alburusai da, maye gurbin kayan aiki da kuma kuɗaɗen gudanar da ayyukan soja," in ji mataimakin sakataren harkokin kuɗi na Pentagon, Arthur Miller.

    Ya bayyana hakan ne lokacin da Majalisar Dattawan Amurka ke zaman tantance shi don naɗa shi mataimakin sakataren Rundunar Ruwa mai kula da harkokin kuɗi.

    Sai dai wannan adadi bai haɗa da asarar da sansanonin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya suka yi ba, ko kuma makaman sojin da aka lalata a wuraren, waɗanda wasu daga cikinsu suka yi mummunar ɓarna sakamakon hare-haren jiragen sama marasa matuƙi da makamai masu linzami da Iran ta kai.

    Wannan ne karo na farko da aka fitar da sabon bayani kan kuɗin yaƙin tun tsakiyar watan Oktoba, lokacin da rundunar CENTCOM ta ce kuɗin da aka kashe ya kai dala biliyan 47.1.

    Bisa ga kimantawar da aka yi a baya, mafi yawan kuɗin da aka kashe, kimanin dala biliyan 29, sun tafi ne wajen maye gurbin alburusan da aka yi amfani da su.

    Haka kuma asarar kayan aiki, ciki har da jiragen sama da jirage marasa matuƙi, ta kai kusan dala biliyan 6 daga cikin jimillar kuɗin da aka kashe.