Chelsea na zawarcin Alexander-Arnold, Man United na harin Calvert-Lewin

Alexander-Arnold
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ana alaƙanta Chelsea da yiwuwar daukar ɗan wasan bayan Ingila Trent Alexander-Arnold, idan har ɗan wasan bayan na Real Madrid mai shekara 28 ya samu damar barin ƙungiyar. (Football Insider)

Manchester United na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan gaba na Leeds United, Dominic Calvert-Lewin mai shekara 29, a watan Janairu. (Athletic)

Manchester City ce ke kan gaba wajen zawarcin ɗan wasan gefe na Amurka mai shekara 17, Mathis Albert, daga Borussia Dortmund, yayin da Chelsea ma ke nuna sha'awar ɗaukar sa. (Teamtalk)

Akwai yiwuwar Chelsea ta cimma yarjejeniya da Bournemouth kan kuɗi kimanin fam miliyan 90 domin ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Ingila, Alex Scott mai shekara 23, kafin watan Janairu. (Mail)

Arsenal da Manchester United da Tottenham da Chelsea na sa ido sosai kan matashin ɗan wasan Jamus, Nicolo Tresoldi; sai dai Club Brugge ba ta da niyyar sayar da ɗan wasan gaban nata mai shekara 22 a watan Janairu. (Football Insider)

Chelsea na sanya ido kan ɗan wasan baya na Como mai shekara 21, Jacobo Ramon, yayin da ake alaƙanta Arsenal da Manchester United da ɗan wasan na ƙasar Spain. (Mail)

Paris St-Germain ko Barcelona na iya doke Liverpool da Arsenal wajen ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Galatasaray, Aleksey Batrakov, ɗan ƙasar Rasha mai shekara 21, wanda ke da sha'awar komawa ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin Turai. (Teamtalk)

Tottenham ba za ta samu ƙarin kuɗi daga Bayern Munich ba, kasancewar yarjejeniyar sauya sheƙar Harry Kane zuwa ƙungiyar ta Bundesliga a shekarar 2023 ba ta ƙunshi wani sharaɗi na kyautar Ballon d'Or ga ɗan wasan na Ingila mai shekara 33 ba. (Goal)

Shugaban Barcelona, ​​Joan Laporta, na da matuƙar sha'awar ɗaukar ɗan wasan baya na Tottenham kuma dan ƙasar Spain, Pedro Porro. (3Cat)