Mene ne tallafin 70,000 da gwamnatin Tinubu ta amince ga ma'aikata duk wata?

Tinubu
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Shirin gwamnatin Najeriya na bai wa ma'aikatan gwamnati tallafin kuɗin sufuri na naira 70,000 duk wata har tsawon wata shida, ya tayar da muhawara kan yadda ake ƙoƙarin rage raɗaɗin matsin tattalin arzikin da jama'a ke fama da shi a faɗin ƙasar.

Gwamnatin ta sanar da hakan ne a ranar Talata bayan wani zama tsakanin wakilan gwamnati da na ƙungiyar Ƙwadogon ƙasar NLC.

Tallafin na zuwa ne a lokacin da hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa ke ci gaba da ƙara wa ma'aikata da iyalansu nauyi, lamarin da ya sa ƙungiyoyin ƙwadago ke ta neman ƙarin matakan da za su sauƙaƙa musu halin da suke ciki.

Kodayake gwamnati ta ce manufar tallafin ita ce rage tasirin matsalolin tattalin arziki ga ma'aikata, wasu na ganin adadin kuɗin ba zai wadatar ba idan aka yi la'akari da yadda farashin abinci da sufuri da sauran muhimman buƙatun rayuwa ke ƙaruwa.

Haka kuma, tambayoyi na ci gaba da tasowa game da waɗanda za su amfana da tallafin da kuma ko matakin zai iya haifar da wani gagarumin sauyi ga rayuwar ma'aikatan da ake son tallafawa.

Me shirin ya ƙunsa?

Cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, kuma ɗaya daga cikin masu taimaka wa shugaban ƙasar kan harkokin sadarwa, Dada Olusegun ya wallafa a shafinsa na X ta ƙunshi abubuwa da dama.

A cikin sanarwar gwamnatin ta fitar da wasu alƙawura da aka cimma a zaman da aka yi takanin NLC da kuma wakilan gwamnati.

Mafi ƙanƙantar albashi

Ɓangarorin biyu sun amince wa da fara tattaunawa kan aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi, tare da cimma matsaya kan ranar da za a fara aiwatar da shi.

Ita dai ƙungiyar ƙwadagon ƙasar na buƙatar gwamnati ta ƙara yawan albashin ma'aikatan ƙasar, la'akari da halin matsi da ta ce ma'aikatan ƙasar na ciki.

A shekarar 2024 ne dai gwamnatin ƙasar ta amince da ƙara mafi ƙanƙantar albashi zuwa naira 70,000 ga ma'aikatan kasar.

Tallafin 70,000 ga ma'aikata

Haka kuma gwamnatin ta amince da biyan ma'aikatan tallafin sufuri na naira 70,000 a kowane wata.

Sanarwar ta ce za biya ma'iakatan gwamnatin tarayya wannan kudi a kowane matakin albashi suke.

Sannan gwamnatin za ta ɗauki tsawon wata shida tana bayar da wannan tallafin wanda ta zai fara daga watan Nuwamba.

Tallafin rage raɗaɗi

Gwamnatin Najeriya ta kuma amince da biyan ma'aikatan wani alawus na musamman da ta bayyana da ''Peculiar Allowance'' domin rage raɗaɗi.

A cewar yarjejeniyar za a fara biyan kuɗin adaga watan Nuwamba, amma gwamnati ta amince ya fara aiki tun daga watan 1 ga watan Mayun 2026.

Biyan bashin alawus na ma'aikatan lafiya

A cikin sanarwar gwamnatin ta kuma amince da biyan ma'aikatan lafiya bashin alawus-alawus na watanni 19 da suke bin gwamnati.

Gwamnatin ta ce za ta yi hakan ane a cikin watanni uku masu zuwa. wanda zai fara daga watan Disamba mai zuwa.

Rage wa ma'aikata haraji

Ma'aikatan Najeriya sun jima suna kiraye-kirayen rage musu harajin da ake cire musu daga albashinsu.

To amma a zaman na jiya wakilan gwamnati sun ce wannan batu yana buƙatar a gabatar da shi gaban Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (NEC) domin tattaunawa da duba yiwuwar aiwatar da hakan.

Ma'aikatan johohi da na ƙananan hukumomi

Haka kuma sanarwar ta ce ɓangarorin biyu sun bukaci gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi su ɗauki matakan aiwatar da tallafin ga ma'aikatansu.

A lokuta da dama dai ma'aikan jihohi da na kananan hukumomi kan koka kan yadda gwamnatocin da suke yi wa aiki ba sa aiwatar da ire-iren tallafin da gwamnatin tarayya ke yi wa ma'aikatanta.

Matakan Tinubu na rage raɗaɗi a baya-bayan nan

A baya-bayan nan gwamnatin Najeriya ta riƙa ɓullo da matakan rage raɗaɗi ga ƴan ƙasar da nufin magane matsin tatalin arzikin da suke ciki.

Da farko a watan da ya gabata ne gwamnatin ta ɓullo da matakin rage farashin man fetru a gidajen fan fetur na ƙasar mallakin gwamnati.

Haka kuma a wannan watan ta ɓullo da wasu matakai da ta ce na rage raɗaɗi ne na tsawon watanni uku.

Sai kuma yanzu da ta sanar da bai wa ma'aikatan gwamnatin tarayya tallafin naira 70,000 a kowane wata.

Tuni dai wasu ƴansiyasa suka fara tsokacin cewa matakan na da alaƙa da siyasa, yayin da a nata ɓangare gwamnatin ke cewa tana yi don tallafa wa ƴan ƙasarta.