Wace irin rayuwa ƴaƴan shugabannin Afirka ke yi?

Nataashaa Museveenii
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Wasu daga cikin ƴaƴa mata na fitattun shugabannin Afirka da suka daɗe suna mulki sun taso ne cikin jin daɗi da walwala, kuma su ma sun zama shahararrun mutane masu tasiri a cikin al'umma.

Wasu sun samu karɓuwa saboda ayyukan da suke yi, yayin da wasu kuma suka fuskanci suka daga jama'a saboda salon rayuwarsu.

Wasu sun yi suna ne saboda kasancewarsu 'ya'yan shugabannin ƙasashensu, yayin da wasu kuma suka gina sunansu ta hanyar ayyukan da suka yi da kansu.

Ga taƙaitaccen nazari kan rayuwar 'ya'ya mata bakwai na shugabannin Afirka.

Natasha Karugiere Museveni - Ƴar shugaban ƙasar Uganda

Natasha Karugire ita ce ta biyu ga shugaban Uganda, Yoweri Museveni, da uwargidan shugaban ƙasar, Janet Museveni.

Ta taso ne a cikin iyalin shugaban ƙasa, amma tun tana ƙarama take da burin zama mai tsara kayan sawa.

Tun daga ƙuruciyarta ta fara inganta da kuma tallata fasaha da al'adun Uganda.

Maimakon dogaro da tasirin siyasa da ƙarfin iyalinta, Natasha ta zaɓi ta gina rayuwarta da sana'arta da kanta.

Domin cimma wannan buri, ta kafa nata kamfanin kayan sawa mai suna J&N Couture, inda take ƙirƙira da sayar da kayayyakin da suka samo asali daga al'adun Uganda.

Ayyukanta sun samu karɓuwa a cikin gida da kuma a matakin ƙasa da ƙasa.

Nataashaa Museveenii

Natasha Museveni ta samu karɓuwa ba kawai saboda aikinta na fasaha da tsara kayan sawa ba, har ma a masana'antar shirya fina-finai.

Ta rubuta tare da bada umarnin shirya fim ɗin "27 Guns", wani fim da ya ba da labarin gwagwarmayar mahaifinta a lokacin yaƙin basasa na Uganda.

A shekarar 2023, ta fitar da wani fim mai suna "Those Among Us".

Natasha ta mayar da hankali wajen ƙarfafa mata, tallata ci gaban Uganda a idon duniya, da kuma ƙarfafa gwiwar mata su fito su taka rawa tare da samun damar shiga kowane fanni na rayuwa.

Mata da dama a Uganda na kallon Natasha ba kawai a matsayin 'yar shugaban ƙasa ba, har ma a matsayin abin koyi.

Littafinta mai suna "Sowing the Mustard Seed", wanda ke bayar da labarin gwagwarmayar mahaifinta a dazuka kafin ya zama shugaban ƙasa tare da tarihin Uganda, na daga cikin ayyukanta da suka fi samun karɓuwa da yabo.

Habibat Oyindamola Tinubu - Ƴar shugaban Najeriya

Habibat Oyindamola mai shekara 32, ƴa ce ga shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

Baya ga kasancewarta 'yar shugaban ƙasa, ita ma abin koyi ce a harkar tallan kayan kwalliya da kuma waƙa.

Tana zaune a Amurka, inda ta yi karatun kiɗa a Kwalejin Kiɗa ta Berklee.

Ta yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashe daban-daban tare da kamfanonin tallan kayan kwalliya da kayan ado irin su Fenty Beauty.

Sai dai bayyana ra'ayoyinta na goyon bayan haƙƙin masu luwaɗi da maɗigo ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin wasu 'yan Najeriya.

Hakan ya zo ne bayan da ta rubuta a shafinta na X cewa za ta yi amfani da aikinta a fannin tallan kayan kwalliya wajen fafutukar kare haƙƙin masu luwaɗi da maɗigo.

Habiibaat Oyindaamoolaa Tinuubuu

Habibat Oyindamola ita ce ta biyu cikin 'ya'ya bakwai da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya haifa tare da uwargidansa, Remi Tinubu.

Duk da cewa 'yar shugaban Najeriyar ta bayyana ra'ayoyinta na goyon bayan haƙƙin masu luwaɗi da maɗigo, dokokin Najeriya sun haramta auren jinsi ɗaya da wasu ayyukan da suka shafi dangantakar masu jinsi ɗaya.

Wanu Hafidh Amir - Ƴar shugabar Tanzania

Waanuu Hafiidh Amiir

Wanu Hafidh Ameir, 'ya ce ga Shugabar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, kuma ta yi suna a ƙasar a matsayin 'yar siyasa kamar mahaifiyarta.

Mamba ce ta jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi (CCM), wadda ita ce jam'iyya mai mulki a Tanzania.

Mamba ce a Kwamiti na jam'iyyar mahaifiyarta.

An haifi Wanu a Zanzibar a shekarar 1982, kuma ta riƙe muƙamai daban-daban a fannin siyasa tsawon shekaru.

Ta kuma kafa tare da gudanar da gidauniyar MIF (Mwanamke Initiative Foundation), wata ƙungiyar agaji da ta mayar da hankali kan ilimantarwa da ƙarfafa yara da matasa, musamman mata, domin su samu damar cimma burinsu a rayuwa.

Charlie Ruto - Ƴar shugaban Kenya

Chaarliin Ruutoo
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Charlie Ruto ita ce ta uku ga shugaban Kenya, William Ruto, da uwargidansa, Rachel Ruto.

Baya ga kasancewarta 'yar shugaban ƙasa, Charlie na ƙoƙarin gudanar da ayyukan da ke ƙarfafa matasan Kenya da samar musu da damammakin ci gaba.

Sai dai kuma ta fuskanci suka daga wasu ƴan Kenya da ke zarginta da amfani da tasirin muƙamin mahaifinta wajen gudanar da wasu ayyuka da suke ganin bai kamata ta yi ba.

Ta fuskanci suka musamman bayan da ta musanta zarge-zargen da ake yi na amfani da kuɗaɗen jama'a wajen gudanar da wani ofishi da ake kira "Ofishin 'Yar Shugaban Ƙasa". Masu sukar ta sun jaddada cewa babu wani tanadi a dokokin Kenya da ya kafa irin wannan ofishi.

Duk da haka, bayan mahaifinta William Ruto ya hau mulki, Charlie ta gudanar da tarurruka da dama tare da manyan jami'an gwamnati a madadin ayyukan da take jagoranta, lamarin da ya jawo muhawara a tsakanin jama'a.

Duk da suka da ƙalubalen da take fuskanta, Charlie na ci gaba da ayyukan da ta ce manufarsu ita ce samar wa matasa damammaki a fannonin jagoranci, fafutukar ci gaban al'umma da kasuwanci.

Ta kafa ƙungiyar Smart Mechanized Agriculture and Climate Action for Humanity and Sustainability (SMACHS), wadda ke wayar da kan matasa tare da ƙarfafa su su shiga harkokin noma na zamani da ayyukan da suka shafi sauyin yanayi da dorewar ci gaba.

Ange Kagame - Ƴar shugaban Rwanda

Rwandan President Paul Kagame has two children, one of whom is Ange Kagame.

She is known for her work in empowering women, expanding education, reducing poverty, caring for the environment and improving public health campaigns.

She serves as deputy director of the Strategic and Policy Council under the Office of the President of Rwanda.

Ange Kaagaamee

Ange Kagame is known for attending crucial meetings on the country's affairs.

She frequently attends National Conference meetings that discuss national development and other issues.

Tariro Mnangagwa - Ƴar shugaban Zimbabwe

Tariiroo Manangaaguwaa

Ange Kagame na ɗaya daga cikin 'ya'yan shugaban Rwanda, Paul Kagame.

Ta yi fice saboda ayyukanta da suka shafi ƙarfafa mata, faɗaɗa ilimi, rage talauci, kare muhalli da kuma inganta shirye-shiryen kiwon lafiyar jama'a.

Ange ta kasance cikin fitattun matasan da ke taka rawa a harkokin ci gaban al'umma a Rwanda, inda ta mayar da hankali kan tallafa wa shirye-shiryen da ke ƙarfafa matasa da mata.

A halin yanzu, tana aiki a matsayin mataimakiyar darakta a wata hukuma da ke ƙarƙashin Ofishin Shugaban Ƙasar Rwanda, inda take taimakawa wajen tsara manufofi da dabarun ci gaban ƙasar.

Brenda Biya - Ƴar shugaban Kamaru

Bireendaa Biiyaa

Brenda Biya 'ya ce ga shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya, wanda ya kasance ɗaya daga cikin shugabannin da suka fi daɗewa suna mulki a duniya.

Ta yi karatu a makarantu masu tsada tun tana ƙarama, kuma ta kasance a cikin fitattun 'ya'yan shugabannin Afirka da ake yawan magana a kansu saboda salon rayuwarta.

Wasu 'yan Kamaru na sukar salon rayuwarta, suna zarginta da nuna rayuwa ta jin daɗi a lokacin da mutane da dama a ƙasar ke fama da talauci da matsin tattalin arziki.

Brenda ta kuma fuskanci suka daga wasu jama'a bayan ta fito fili ta bayyana cewa ita ƴar luwaɗi ce, inda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce musamman saboda dokokin Kamaru na haramta alaƙar soyayya tsakanin masu jinsi ɗaya.