Newcastle ta dage kan farashin Gordon, Liverpool na son Diomande

Anthony Gordon

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Newcastle United ta dage kan farashin fam miliyan 75 kan ɗan wasan Ingila Anthony Gordon, yayin da Bayern Munich ke dab da amincewa da ɗaukar ɗan wasan tsawon shekara biyar. (Times - subscription required)

Liverpool na son ci gaba da riƙe ɗan wasan gaban ta Alexander Isak, kuma suna son ɗauko ɗan wasan gefe Yan Diomande, da Antonio Nusa, dukkansu da ke taka leda a RB Leipzig, da ɗan wasan gaban Faransa Bradley Barcola da ke Paris St Germain, (The i Paper)

Har ila yau Liverpool ɗin na harin ɗan wasan Sunderland Robin Roefs, a matsayin mai tsaron raga, idan Alisson ya yanke shawarar komawa Juventus. (Caught Offside)

Duk da alakanta ɗan wasan bayan Italiya Michael Kayode da ake da komawa Juventus, ɗan wasan ya ce yana jin daɗin zamansa a Brentford, kuma baya tunanin barin ƙungiyar. (Tuttosport, via Football Italia)

Ɗan wasan tsakiya na Faransa Eduardo Camavinga na iya barin Real Madrid, sakamakon rashin shiga cikin tawagar ƙungiyar Faransa da za ta buga gasar cin Kofin Duniya, yayin daTottenham ke son ɗaukarsa. (Teamtalk, external)

Tottenham na harin ɗan wasan Monaco Maghnes Akliouche idan ƙungiyar ta yanke shawarar siyar da ɗan wasan . (Football Insider)

Inter Milan za ta siyar da ɗan wasan bayanta Denzel Dumfries, kan yuro miliyan 25, zuwa wani taƙaitacen wa'adi idan ɗan wasan ya yi niyyar zuwa watan Yulin. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Nottingham Forest na shirye-shiryen tsawaita waVitor Pereira kwantaraginsa mai tsayin wa'adi. Kociyan ɗan Portugal ya jagorancin horar da ƴan wasan tsawon watanni 18, kuma ya taka rawa wajen ƙoƙarin da ƙungiyar ta yi a gasar Firimiya. (Athletic - subscription required)