Gordon ya amince da komawa Bayern, Greenwood zai ci gaba da zama a Marseille

Anthony Gordon

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Bayern Munich ta cimma yarjejeniya da Anthony Gordon kuma ta fara tattaunawa da Newcastle United kan sayen ɗan wasan gaban na Ingila, mai shekara 25. (Bild)

Tsohon ɗan wasan Ingila Mason Greenwood, mai shekara 24, yana shirin ci gaba da zama a Marseille duk da cewa ana alaƙanta shi da manyan ƙungiyoyin Turai kamar Juventus, da Borussia Dortmund da Atletico Madrid. (Sun)

Chelsea da Manchester United sun sanya ɗan wasan gaban Real Sociedad ɗan ƙasar Sifaniya Ander Barrenetxea, mai shekara 24, a jerin sunayen waɗanda za su yi zawarci a wannan bazarar. (Marca)

Manchester United ta shirya zawarcin ɗan wasan tsakiyar Nottingham Forest ɗan ƙasar Ingila Elliot Anderson, mai shekara 23. (Give Me Sport)

Chelsea da Galatasaray na sha'awar sayen ɗan wasan gaban Ingila Jonathan Rowe mai shekara 23 daga Bologna. (Gazzetta dello Sport)

Ɗan wasan gaban Jamus Nick Woltemade ba ya jin daɗin zamansa a Newcastle kuma Atletico Madrid na cikin ƙungiyoyin da ke sanya ido kan lamarin ɗan wasan mai shekara 24. (Bild)

Marseille ba za ta yi amfani da zaɓin da ta ke da shi na ɗaukar ɗan wasan baya na Faransa Benjamin Pavard mai shekara 30 ba, wanda a halin yanzu yake zaman aro daga Inter Milan. (Bild)

Tottenham na neman ɗan wasan bayan Sassuolo da Bosnia-Herzegovina Tarik Muharemovic, mai shekara 23. (Caught Offside)

Ɗan wasan gaba na Ivory Coast Yan Diomande, wanda rahotanni suka ce farashinsa zai kai fam miliyan 80, na jan hankalin Chelsea da Liverpool amma ɗan wasan mai shekara 19 ba zai yi gaggawar barin RB Leipzig ba. (The Athletic)

Leeds na zawarcin ɗan wasan gaban Belgium Lois Openda, wanda ke shirin komawa Juventus daga RB Leipzig, amma kulob ɗin na Italiya na fatan cefanar da ɗan wasan mai shekara 26, sakamakon rashin tagomashi da ya samu a zaman aron da ya ke yi a ƙungiyar. (TeamTalk)

Manchester United na neman matsuguni na dindindin ga golan Kamaru Andre Onana, mai shekara 30, wanda a halin yanzu ya ke zaman aro a ƙungiyar Trabzonspor ta Turkiyya. (ESPN)

Har ila yau United a shirye take ta miƙa sabuwar yarjejeniya ga mai tsaron gida Tom Heaton, mai shekara 40. (Caught Offside)