Halin da ake ciki a DR Kongo bayan ɓarkewar cutar Ebola

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, James Gallagher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health and science correspondent
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Ɓarkewar cutar Ebola da ake fama da ita a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo na haifar da damuwa mai tsanani ga al'ummar ƙasar.
Cutar ta fara yaɗuwa na tsawon makonni kenan ba tare da an gano ta da wuri ba a wani yanki da rikicin yaƙi ke wahalar da aikin agaji da kula da lafiya.
Nau'in cutar Ebola ɗin da ke yawo a wannan karon yana daga cikin nau'ikan da ba kasafai ake samunsu ba, abin da ke nufin akwai ƙarancin hanyoyin magance ta idan ta kama mutum, duk da cewa tana kashe kusan mutum ɗaya cikin uku da suka kamu da ita.
Hukumomi sun ce akwai kusan mutane 250 da ake zargi sun kamu da wannan nau'in cutar Ebola, yayin da aka riga aka samu mutuwar kusan 80. Wannan yana nuna cewa cutar ta riga ta bazu fiye da yadda ake tunani tun farko, lamarin da ke sa wannan lokaci ya zama mai muhimmanci wajen daƙile yaduwar ta kafin ta ƙara yaɗuwa zuwa yankuna masu yawa.
Ko da yake yawanci, ɓarkewar Ebola kan tsaya ne a ƙananan yanki, masana lafiya na tunawa da mummunan ɓarkewar cutar a shekarar 2014 zuwa 2016 a yammacin Afirka, inda mutane 28,600 suka kamu da cutar.
Wannan tarihin ne ke sa a riƙa ɗaukar duk wani sabon ɓarkewa da matuƙar muhimmanci, duk da cewa ba kowanne yake kai irin wannan mataki ba.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana lamarin a matsayin abin da ke buƙatar kulawa ta duniya, amma ba yana nufin cutar na gab da zama annobar duniya kamar Covid-19 ba.
Hadarin da ke tattare da yaɗuwar Ebola zuwa ƙasashen duniya yana da ƙanƙanta, kamar yadda aka gani a bɓarkewar cutar a baya inda aka samu 'yan kaso kaɗan a ƙasashe irin su Birtaniya, duk da haka dukkan su ma'aikatan lafiya ne da suka dawo daga aikin agaji.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai barazanar ta fi shafar ƙasashen makwabta kamar Uganda da Sudan ta Kudu da Rwanda, saboda hulɗar kasuwanci da zirga-zirgar mutane.
A Uganda ma an riga an tabbatar da wasu mutane biyu da suka kamu da cutar, inda ɗaya daga cikinsu ya rasu, abin da ke nuna cewa yaɗuwar na iya wuce iyakar Kongo idan ba a ƙara ƙaimi wajen shawo kanta ba.
Ebola cuta ce mai tsanani kuma mai kisa, duk da cewa ba ta yawaita ba. A dabi'ance, ƙwayoyin cutar Ebola na rayuwa ne a cikin dabbobi, musamman jemage masu cin 'ya'yan itatuwa saboda hakan mutane na iya kamuwa idan sun kusanci dabbobin da ke ɗauke da cutar ko suka taɓa su kai tsaye.
Wannan sabon ɓarkewar cutar na da nasaba da nau'in Ebola mai suna Bundibugyo, wanda yana daga cikin nau'o'i uku da aka sani suna haddasa ɓarkewar cutar, amma shi ba a saba jin sa sosai ba.
Wannan nau'in ya taɓa haddasa ɓarkewa sau biyu kacal, a shekarar 2007 da 2012, inda ya kashe kusan kashi 30 cikin 100 na waɗanda suka kamu.
Bundibugyo na kawo ƙalubale masu yawa ga masana lafiya. Har yanzu babu allurar rigakafi ko magani da aka amince da shi kai tsaye don wannan nau'in, ko da yake akwai wasu gwaje-gwajen magunguna da ake ci gaba da yi. Wannan ya bambanta shi da wasu nau'o'in Ebola da ake da wasu matakan kariya ko magani a kansu.
Haka kuma, gwaje-gwajen gano cutar ba sa yin aiki yadda ya kamata a farko. A farkon wannan ɓarkewar, sakamakon gwaje-gwaje ya nuna ba Ebola ba ne, har sai da aka yi amfani da ƙarin kayan bincike na dakin gwaje-gwaje aka tabbatar cewa Bundibugyo ne ke haddasa cutar. Masana lafiya na cewa wannan na daga cikin manyan ƙalubale a wannan lokaci.
Alamu na cutar kan fara bayyana tsakanin kwanaki 2 zuwa 21 bayan kamuwa. A farko, tana kama da mura da zazzaɓi, ciwon kai da gajiya. Amma daga baya tana tsananta, ta haifar da amai, zawo, sannan gaɓoɓin jiki su fara kasa aiki. Wasu marasa lafiya kan fara zubar jini a ciki ko a waje.
Saboda babu magani da aka ƙera musamman don wannan nau'i na cutar Ebola wato Bundibugyo, kulawa ta dogara ne kan taimakon jiki kawai, kamar rage zafi, magance sauran cututtuka, shan ruwa mai yawa da kulawa da abinci. Idan aka fara kula da mara lafiya da wuri, damar samun sauƙi ko tsira daga cutar na ƙaruwa.
Ebola na yaɗuwa ne ta hanyar ruwan jikin mai cuta kamar jini da amai, amma yawanci hakan yana faruwa ne bayan mutum ya fara nuna alamomi.
A wannan ɓarkewar, an gano cewa ma'aikaciyar jinya ce ta farko da ta fara nuna alamomi a ranar 24 ga Afrilu, sannan aka ɗauki kusan makonni uku kafin aka tabbatar da cewa cutar ce ta ɓarkewar.
Masana lafiya sun ce wannan jinkiri wajen gano cutar yana da matuƙar damuwa, domin yana nufin cutar ta riga ta bazu fiye da yadda aka gano ta a hukumance. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargaɗin cewa hakan na iya nuna akwai yaɗuwar cutar fiye da abin da ake gani a yanzu.
Matakan daƙile cutar sun haɗa da gano masu ɗauke da ita cikin gaggawa, bin diddigin waɗanda suka yi hulɗa da su, hana yaɗuwa a asibitoci, da kuma tabbatar da cewa an yi jana'izar waɗanda suka mutu sakamakon cutar cikin tsari mai hana yaɗuwa.
Sai dai wannan aiki na da wahala saboda yankunan da abin ya shafa suna cikin rikicin da ya saka mutane sama da 250,000 suka rasa matsugunansu. Haka kuma wasu yankuna cibiyoyin hakar ma'adinai ne, inda mutane ke yawan motsi daga wuri zuwa wuri, abin da ke ƙara saurin yaɗuwar cutar.
Duk da haka, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo na da ƙwarewa wajen yaƙi da Ebola, kuma masana lafiya sun ce yanzu an fi shiri fiye da shekaru goma da suka wuce. Makomar wannan sabuwar ɓarkewar za ta dogara ne da yadda za a gaggauta daƙile ta a yanzu.









