Yadda cutar Ebola ke neman sake zama annoba a duniya

Asalin hoton, Reuters
Hukumar lafiya ta duniya ta ayyana ɓarkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Dumukuradiyyar Kongo a matsayin, matsalar lafiya ta duniya da ke buƙatar matakin gaggawa.
Hukumar ta ƙara da cewar ɓarkewar cutar, a gabashin ƙasar, duk da mutum 246 ne suka kamu da ita, kuma kusan 90 suka mutu, lamarin bai kai matsayin annoba ba.
Shugaban hukumar ta lafiya Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi gargadin cewar akwai babban rashin tabbas kan ainahin adadin mutane da suka kamu da cutar da ƴaduwar cutar a yankunan da ke sassan ƙasar.
WHO din dai ta ce zuwa yanzu babu magani ko rigakafin da aka amince da shi
a kan nau'in Bundibugyo na cutar ta Ebolar da ta bayyana a wannan karon
Ministan lafiya na kasar ta Kongo, Samuel-Roger Kamba, ya ce a yanzu babu wani magani ko rigakafin cutar da ke akwai.
Ya kara da cewa yawancin wadanda suka mutu, ba su nemi zuwa asibiti ba - illa dai sun buge da ziyartar wuraren ibada domin neman taimako.
WHO ɗin ta ce akwai ɗakunan gwaje-gwaje takwas da aka suka tabbatar da barkewar cutar, tare da sauran cibiyoyin lafiya uku da ke Bunia babban birnin Ituri, da biranen Mongwalu da Rwampara.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hukumar lafiya ta duniyar ta ce ba wai a iya Kongo aka samu ɓarkewar cutar ba, an samu ɓullar cutar a maƙociyar ƙasar Uganda, inda mutum biyu suka kamu.
Hukumomi a Uganda sun ce an gano wani mutum mai shekara 56 da ya mutu yana ɗauke da cutar ta Ebola, ranar Alhamis.
An tabbatar da wani da ke dauke da cutar a babban birnin Kongon, Kinshasa, mutumin da ake gani ya koma can ne daga Ituri.
A wata sanarwa gwamnatin Uganda ta ce mutumin da ya mutu dan Kongo ne wanda kuma tuni aka mayar da gawarsa kasarsa ta Kongo.
Ana ci gaba da yi wa ƙasashen da ke da iyaka da Kongo kallon su ma suna cikin babbar barazana ta yaɗuwar cutar, dogaro da yawan al'umma da ke gwamatsuwa a motocin haya, da harkokin kasuwanci, da tafiye-tafiye.
Hukumar ta lafiya ta shawarci Kongo da Uganda su kafa cibiyon gaggawa na bayar da kulawa da magani ga wadanda suka kamu da cutar, tare da bin diddigin wadanda suka yi mu'amulla, da kuma aiwatar da matakan kariya.
Domin takaita bazuwar cutar, hukumar ta ce mutanen da aka samu wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, nan da nan a rika ware su daga cikin jama'a, a yi musu magani har sai an gudanar da gwaji akalla sa'a 48 tsakani na nau'ukan cutar biyu an tabbatar ba sa dauke da cutar.
Ga kasashen da ke da iyaka a yankin da aka tabbatar da mutanen da suka kamu da cutar, dole gwamnati ta karfafa sa ido da bincike da bayar da rahoton abubbuwan da suka shsfi lafiya.
WHO ta kara da cewa bai kamata kasashen da ba sa yankin da cutar da bayyana ba su rufe kan iyakokinsu, ko takaita zirga-zirga da kasuwanci ba, kasancewar yin hakan yawanci ana yi ne domin tsoro, wanda hakan ba shi da wata madogara ta kimiyya.












