Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Alhamis 14//05/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, da Usman Minjibir da Aisha Babangida

  1. Somalia na fuskantar yunwa mafi muni - MDD

    Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta dauki nauyi ya ce Somalia na fama da ƙarancin abinci da ka iya haifar da yunwa mafi muni a cikin shekaru a kudancin kasar.

    Rahoton ya kuma ce ƙasashen gabashin Afirka na fuskantar irin wannan matsalar tsawon shekara hudu yayin da mutane sama da dubu dari biyu suka rasu sakamakon ƙarancin abincin.

    Matsalar na karuwa ne sakamakon fari da aka fuskanta da kuma tsadar abinci da yakin gabas ta tsakiya ke kara ta'azzarawa

  2. Tinubu ya gargaɗi masu siyasar a mutu ko a yi rai a zaɓen fitar da ƴantakara

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi kira ga ƴan jam'iyyar APC da su fita su kaɗa ƙuri'a a zaɓen fitar da ƴantakarar da za su wakilci jam'iyyar a babban zaɓen ƙasar, inda ya buƙace su da su gudanar da zaɓen cikin lumana.

    A gobe Juma'a ne za a fara gudanar da zaɓen fitar da ƴantakarar APC, inda za a fara da zaɓen fitar da ƴatakarar majalisar wakilai.

    "Mun assasa APC ne domin ci gaban al'umma da haɓaka dimokuraɗiyya da sadaukarwa. Wannan sadaukarwar ta taimaka mana wajen zama tsintsiya, don haka akwai buƙatar mu cigaba da ɗabbaƙa ta," in ji shi.

    Ya ce zaɓe na cikin manyan ginshiƙan dimokuraɗiyya, sannan ya yi kira da a gudanar da zaɓen fitar da ƴantakarar a matsayin ƴanuwa.

    "Dukkan ƴantakara da masu zaɓe dole su tabbatar da zaman lafiya, sannan su fifita muradun jam'iyyar da ma ƙasar baki ɗaya. Dole a kowace takara akwai wanda zai yi nasara, da wanda zai yi rashin nasara. Ina fata dukkansu za su dunƙule su yi aiki tare."

    Tinubu ya kuma yi kira ga waɗanda za su yi nasara da su yi haƙuri su raka waɗanda suka yi nasarar, domin a cewarsa, " wanda ya yi nasara shi ne wanda ya yi haƙuri ya jira wani lokaci, ba wanda zai fasa kowa ya rasa ba."

    Shugaban ya kuma ce waɗanda suka yi nasara ya kamata su ja kowa a jiki, "mu guji siyasa a mutu ko a yi rai wadda aka wuce lokacinta."

  3. Isra'ila za ta shigar da jaridar New York Times ƙara

    Gwamnatin Isra'ila ta ce firaiministan ƙasar Benjamin Netanyahu da ministan harkokin wajen ƙasar sun ba da umarnin kai ƙarar jaridar New York Times kotu bisa zargin ɓata wa gwamnatin suna kan rahoton da ta wallafa da ke cewa cin zarafin Falasdinawan da ake tsare da su a ƙasar ya yawaita.

    Jaridar ta dogara ne da shaidar da ta tattara bayan tattaunawa da wasu Falasdinawa 14 a yankin Gabar Yamma, waɗanda suka ce dakarun Isra'ila sun ci zarafinsu ta hanyar lalata.

    A wani sako ta shafin sada zumunta, ma'aikatar harkokin waje ta Isra'ila ta bayyana rahoton a matsayin ɗaya daga cikin ƙarya mafi muni da aka taɓa wallafawa game da ƙasar Isra'ila.

    Babu ƙarin bayani kan ko a wace kotu ce za a shigar da ƙarar.

  4. Iran ta zargi Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da hannu a yaƙinta da Isra'ila da Amurka

    Ministan harkokin wajen Iran ya zargi Hadaddiyar Daular Larabawa da hannu kai tsaye a cikin yaƙin da suke da Isra'ila da Amurka.

    A wajen taron ministocin ƙungiyar BRICS Abbas Araqchi ya zargi wakilin Hadaddiyar Daular Larabawa da ba Isra'ila damar amfani da ƙasar wajen harba masu makamai masu linzami.

    Ya ce alaƙar dake tsakanin ƙasashen biyu barazana ce ga tsaron ƙasarsu.

    Wakiliyar BBC ta ce Iran ta kai hare-hare a Saudiya da hadaddiyar Daualar Larabawa a lokacin yaƙin, sai dai wasu rahotanni da ba a tantance ba sunce ƙasashen sun mayar da martamni.

  5. Wani jigo a gwamnatin Birtaniya ya aje muƙaminsa

    Sakataren lafiya na Birtaniya Wes Streeting ya ce baya da ƙwarin gwiwa kan shugabancin Firaministan ƙasar Keir Starmer, wanda a cewarsa hakan ya sa ya ajiye muƙamin.

    A cikin takardar ajiye aiki da ya rubuta Mr Wes ya ce ƙasar na buƙatar hangen nesa a maimakon barin giɓi. Ya dauki matakin ne bayan da sakamakon zaɓen da ya gabata bai yi ma jam'iyar Labour dadi ba.

    Sai dai a cikin takardar ta shi bai nuna wata alama da ke nuna kai tsaye yana goyon bayan Starmer ya sauka daga muƙaminsa ba.

    Wakilin BBC ya ce dukkaninmu mun san cewa yana shirin shiga cikin masu son shugabanci, babban abinda yafi jan hankali a cikin takardar da ya rubuta shine ya ce ƙasar na fuskantar babban kalubale.

  6. Shin China na taka muhimmiyar rawar bayan fage a rikicin Iran?, Anthony Zucker da Laura Baker - BBC

    Ziyarar da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya kai birnin Beijing a makon da ya gabata ta ƙara fito da irin tasirin da China ke da shi a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Rahotanni sun nuna cewa Amurka na sanya ido sosai kan wannan al’amari, musamman dangane da yadda China ke hulɗa da Iran a lokacin da rikici ke ƙaruwa a yankin.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce yana fatan China za ta faɗa wa Iran abin da ya kamata ta sani.

    “Ina fatan China za ta gaya masa abin da ya kamata a faɗa, wato abin da suke yi a mashigar Hormuz ya sa duniya ta ware su. Su ne ake gani a matsayin masu laifi a wannan rikicin,” in ji Rubio.

    Shi ma Ali Wine, babban mai ba da shawara kan hulɗar Amurka da China a ƙungiyar International Crisis Group, ya ce Amurka ta fahimci cewa China za ta taka muhimmiyar rawa idan ana son dawo da Iran teburin tattaunawa cikin hanya mai ɗorewa.

    “Ina ganin Amurka ta fahimci cewa idan ana son dawo da Iran kan teburin sulhu ta hanya mai ɗorewa na dogon lokaci, to lallai China za ta taka rawa,” in ji shi.

    A nasa ɓangaren, shugaban Amurka Donald Trump ya nuna kamar ba ya damuwa sosai da kusancin da ke tsakanin China da Tehran.

    Ko da yake Amurka ta kakaba wa wani matatar mai da ke China takunkumi saboda safarar man Iran, Trump ya rage muhimmancin duk wata goyon bayan da China ke bai wa Iran yayin rikicin.

  7. Makinde ya yanki takardar tsayawa takarar shugaban Najeriya

    Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban Najeriya a zaɓen shekarar 2027, inda ya bayyana cewa zai nemi kujerar ne ƙarƙashin jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM).

    Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani babban gangamin haɗakar jam’iyyun PDP da APM da aka gudanar a Ibadan.

    Sanarwar ta Makinde ta ja hankalin dubban magoya baya da masu ruwa da tsaki da kuma abokan siyasarsa, lamarin da masana ke gani a matsayin wani muhimmin mataki a sauye-sauyen siyasa da ke ci gaba da faruwa gabanin babban zaɓen gaba.

    Sanarwar tasa dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun shirye-shiryen siyasa gabanin zaɓen 2027, inda masana ke ganin matakin na iya sauya yanayin siyasar ƙasar, musamman a yankin Kudu maso Yamma.

  8. 'Iran na bai wa jiragen China damar wucewa ta mashigar Hormuz'

    Rahotanni na cewa Iran ta bai wa ƙarin jiragen ruwan ƙasar China damar wucewa ta mashigar Hormuz tun daga daren jiya.

    Kamfanin dillancin labarai na Fars, wanda ya ambato wata majiya mai tushe, ya ce an ɗauki matakin ne bayan buƙatun da ministan harkokin wajen China da kuma jakadan Beijing da ke Iran suka gabatar.

    Fars ta ce a cikin kwanakin nan, aƙalla jiragen dakon mai da manyan jiragen ruwa guda shida mallakin China ko masu aiki da ita sun ratsa mashigin Hormuz.

    Sashen bincike na BBC Verify ya kuma tabbatar da cewa aƙalla wani babban jirgin dakon mai na China ya bi ta mashigar Hormuz a jiya.

    Babban jirgin mai mai suna Yuan Huahu, wanda ke ɗauke da tutar China, ya tsaya a Basra da ke Iraq a farkon watan Maris inda ya ɗauki kayan mai, kamar yadda bayanan siginar motsinsa suka nuna.

    Rahotanni sun ce jirgin ya ratsa mashigar Hormuz da sanyin safiyar Laraba 13 ga watan Mayu, inda ya bayyana matsayinsa na kusan minti 90 kacal a ruwan Iran kusa da tsibirin Lark.

    Daga baya, bayan fiye da sa'o'i 12, jirgin ya sake bayyana matsayinsa yayin da yake tsakiyar Tekun Oman gabashin birnin Sohar na ƙasar Oman, a cewar BBC.

    An bayyana cewa jirgin na kan hanyarsa ta zuwa tashar jiragen ruwa ta Zhoushan da ke China, inda ake sa ran zai isa a farkon watan Yuni.

    Har zuwa yanzu dai hukumomin China ba su tabbatar da wannan rahoto ba.

  9. Manyan ƙalubale da ke hana matasa yin takara a Najeriya

    Duk da cewa tsohon shugaban Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari ya saka hannu a dokar da ta bai wa matasa damar tsayawa takara a 2018, amma har yanzu masu karancin shekaru na fuskantar tarnaƙi iri-iri a siyasa ƙasar.

    A duk lokacin da zaɓe ya ƙarato a Najeriya, ana ganin matasa ne suka fi cika filayen yaƙin neman zaɓe da tarukan siyasa - su ne ke liƙa fastoci da yaɗa saƙonni a kafafen sada zumunta da kuma zagaya unguwanni suna neman ƙuri'u domin 'yan takara.

    To amma idan aka duba cikin jerin masu neman kujerun siyasa, sai a tarar cewa matasa kaɗan ne ke samun damar shiga takara.

    Wannan lamari ya daɗe yana jawo muhawara a tsakanin al'umma, musamman ganin cewa matasa su ne mafi rinjaye a Najeriya.

    Duk da yawan kiraye-kirayen da ake yi na bai wa matasa dama a shugabanci, har yanzu da yawa daga cikinsu na kallon siyasa a matsayin wata hanya mai cike da wahala, kuɗi da kuma tasirin masu ruwa da tsaki.

  10. 'Ba makawa kan ƙara farashin tikitin jirgin sama a Turai'

    Shugaban Ƙungiyar kula da sufurin Jiragen Sama ta Duniya ya yi gargaɗin cewa babu makawa kan batun ƙarin farashin tikitin jiragen sama a Turai saboda tsadar man jiragen sama da yaƙin Iran ya haddasa.

    Willie Walsh ya shaida wa BBC cewa ko da za a kawo ƙarshen yaƙin gobe, tasirinsa kan masana'antar sufurin jiragen sama zai ci gaba har cikin watanni masu zuwa.

    Ya ce idan har ba a samu wata kafar samar da isasshen man ba, za a iya fuskantar tsaiko idan aka shiga watannin bazara na Yuni da Yuli da kuma Agusta.

    Ƙasashen Turai, da Birtaniya, sun dogara ne kacokan kan shigo da mai daga Gabas ta Tsakiya, wanda a halin yanzu ba su iya samu sakamakon datse mashigar Hormuz.

  11. Tsawa da ruwan sama sun yi ajalin fiye da mutum 100 a Indiya

    Tsawa da ruwan sama mai ƙarfi sun halaka aƙalla mutum fiye da 100 a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin Indiya.

    Wani jami'i daga hukumar kare bala'oi ya ce sama da mutum 50 sun jikkata sannan lamarin ya yi ɓarna a gidaje da dama da ke gundumomi.

    An samu mutane da dama da lamarin ya rutsa da su sakamakon rushewar bango da faɗuwar bishiyoyi da kuma tsawa.

    Masu hasashen yanayi sun yi gargaɗin za a iya samun tsawa a sassan arewacin Indiya a ƴan kwanaki masu zuwa.

  12. Dizel da man fetur sun ƙare a Cuba - ministan makamashi

    Ministan makamashi a Cuba ya ce dizel da man fetur sun ƙare gaba ɗaya a ƙasar.

    A wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai a ƙasar, Vicente de la O Levy ya ce akwai ƙarancin gas kasancewar makamasshin Cuba yana cikin garari sakamakon toshe zirga-zirga a mashiar Hormuz.

    A ranar Laraba ne zanga-zanga ta ɓarke kan rashin wuta a Havana, babban birnin ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

    A makon nan ne Amurka ta jaddada tayin tura dala miliyan 100 zuwa ƙasar don zama musaya na gyare-gyare masu muhimmanci na tsarin kwamunisanci na Cuba.

    Asibitoci sun shiga wani hali yayin da lamarin ya tilasta rufe makarantu da ofisohin gwamnati. Kazalika, halin da ake ciki ya yi tasiri kan al'amuran yawon buɗe ido wanda ya sakance babbar hanyar samun kuɗi ga Cuba.

    Cuba ta dogara kan Venezuela da Mexico domin samun mai sai dai ƙasashen biyu sun daina samar da man tun bayan da Shugaba Donald Trump ya yi barazanar ƙaƙaba haraji kan ƙasashen da suka kuskura suka tura mai zuwa Cuba.

  13. Dangote ya yi watsi da tayin NNPC na ƙara hannun jari a matatarsa

    Shugaban Kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya ce kamfaninsa ya yi watsi da buƙatar da kamfanin mai na Najeriya NNPC ya gabatar ta neman ƙara yawan hannun jarinsa a matatar man Dangote da kashi 7.25 cikin 100.

    Dangote ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da shugaban asusun zuba jari na Norway, Nicolai Tangen.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa an samu ƙaruwar man da ake tacewa a matatar mai da ke Lekki zuwa lita biliyan 3.18 a watanni uku na farkon 2026 yayin da man da ake shigowa da shi ya ragu sosai da lita miliyan 965.52.

    Binciken da aka ƙara yi ya nuna cewa yaƙin Amurka da Iran da ya janyo matsalar mai ya haifar da ƙaruwar kuɗin shiga ga matatar Dangote yayin da matatar ta ƙara yawan tataccen man da take fitarwa.

    A cewar Dangote, an ƙi amincewa da tayin NNPC na ƙara kashi 7.25 na hannun jarinsa a matatar saboda kamfanin yana shirin bai wa sauran ƴan Najeriya damar zuba hannun jarinsu a kamfanin.

  14. Shugaba Ramaphosa zai je majalisa don amsa tambayoyi

    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa zai bayyana gaban majalisar dokoki a yau inda ake sa ran zai fuskanci matsin lamba daga ƴanmajalisa na ɓangaren hamayya.

    Wannan ne karon farko da Shugaba Ramaphosa zai fuskanci ƴanmajalisa tun bayan da wata kotu a ƙasar ta yanke cewa ya kamata majalisar ta fara shiri kan ko za a tsige shugaban.

    A cewar kafar yaɗa labarai ta SABC, ba lalle a tado da batun Kotun Tsarin mulkin ba sai dai wasu ƴanmajalisar na ɓangaren hamayya za su iya taɓo batun.

    Ramaphosa zai yi magana ne kan ayyukan soji na kakkaɓ yankuna daga masu aikata miyagun laifuka da kuma wuraren da ake haƙon ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba.

    Zai kuma yi magana kan hanyoyin da ya bi na dakatar da kwamishinan ƴansanda, Fannie Masemola da kuma abin da gwamnatinsa take yi game da ƙaruwar rashin ayyukan yi.

  15. An zaƙulo matattu daga ɓuraguzai a Kyiv

    Jami'ai a Kyiv sun ce an zaƙulo gawawwakin mutum uku daga ɓuraguzan ginin da Rasha ta kai wa hari a Kyiv inda ake ci gaba da aikin ceto sakamakon ɓarnar da hare-haren suka yi.

    Aƙalla mutum 144 ne suka ji rauni har da yara biyu, in ji magajin garin. 21 cikinsu suna samun kulawa a asibiti, har da yaro guda.

    Rana ta uku ne nan da Ukraine ke bayar da rahoton mace-mace yayin da Rasha ke zafafa hare-hare bayan da yarjejenyar tsagaita wuta ta ƙare ranar Litinin.

    A hare-haren na cikin dare, an harba fiye da jirage marasa matuƙa 670 sai makamai masu linzami 56 zuwa sassan Ukraine, kamar yadda Shugaba Volodomyr Zelensky ya bayyana.

  16. 'Bakin Amurka da China ya zo ɗaya kan hana Iran mallakar makamin nukiliya'

    Fadar White House ta ce Shugaba Trump da takwaransa na China, Xi - da ke ganawa a Beijing - sun amince cewa bai kamata Iran ta mallaki makamin nukiliya ba kuma ya zama dole a buɗe Mashigar Hormuz.

    Wata sanarwa daga Amurka game da ganawar ta tsawon sa'a biyu ta ce akwai fahimtar juna tsakaninsu kuma shugabannin biyu suna aiki don inganta alaƙarsu ta tattalin arziki sai dai sanarwar ba ta ambaci ɗaya daga cikin batutuwan da suke taƙaddama a kai ba - Taiwan.

    Mista Xi ya ce ya kamata Amurka da China su zama "abokan hulɗa ba abokan gaba ba" sai dai ya yi gargaɗin za a iya samun saɓani kan maganar Taiwan.

  17. NEMA ta buƙaci jihohi su ɗauki matakan kariya daga ambaliya

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta yi kira ga gwamnonin jihohi da u fara ɗaukan matakan riigakafi da nufin kaucewa matsalar ambaliya sakamakon hasashen da aka yi cewa fiye da jihohi 30 na iya fuskantar gagarumar matsalar ambaliya a daminar bana.

    A cewar saƙon da NEMA ta wallafa a shafinta na X, Shugabar hukumar Zubaida Umar ta yi kira ga jihohin da su gaggauta ɗaukan mataki domin rage tasirin ambaliyar da aka yi hasashen za a samu a wasu yankunan ƙasar.

    Sanarwar ta ce wasu daga cikin matakan da ake tsammanin jihohin su ɗauka sun haɗa da sake farfaɗo da shirin tsaftar muhalli duk wata da yawan gyara magudanan ruwa da hanyoyin wucewar ruwa.

    Shugabar NEMA ta kuma ce yi kira ga sarakunan gargajiya da malaman addini da ƙungiyoyin matasa da kafafen yaɗa labarai da kamfanoni masu zaman kansu da su tallafa wa ƙoƙarin hukumar wajen kare afkuwar ambaliya a ƙasar

  18. ‘Netanyahu bai ziyarci Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a asirce ba’

    Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta musanta cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya kai wata ziyarar sirri ƙasar, duk da cewa ofishin Mista Netanyahu ya sanar da ziyarar ne sa'o'i kaɗan kafin hakan.

    Wakiliyar BBC ta ce Ma'aikatar harkokin wajen haɗaɗɗiyar daular larabawar ta musanta batun ziyarar da kakkausar murya inda ta ce dangantaka da Isra'ila a fili ake gudanar da ita kuma duk wani iƙirari game da ziyarar da ba a sanar ba "ba ta da tushe.

    Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen Larabawa da dama da suka ƙulla hulɗar jakadanci da Isra'ila bayan yarjejeniyar Abraham Accords a wa'adin shugabancin Trump na farko.

  19. Ana laluben mutanen da suka mutu bayan harin Rasha a Kyiv

    Magajin garin Kyiv ya ce Rasha ta kai wani gagarumin hari ta sama kan babban birnin na Ukraine kuma tuni jami'ai suka duƙufa domin duba ɓuraguzai don zaƙulo waɗanda lamarin ya rutsa da su.

    Lamarin ya yi ajalin mutum biyu sai wasu 40 da suka ji rauni kamar yadda jami'ai suka bayyana.

    Vitaliy Klitschko, wanda ya ziyarci ginin da lamarin ya shafa, ya ce lamarin ya shafi ɗakuna 18.

    A cewar shi, harin ya lalata hanyoyin samar da ruwa na birnin.

    A ranar Laraba Rasha ta kai hari mafi girma da aka kai ta sama kan Ukraine tun bayan fara yaƙi tsakanin ƙasashen.

    Shugaba Zelensky ya ce Moscow ta harba wasu jiragen sama marasa matuƙa sama da ɗari takwas kuma tuni aka kuɓutar da mutane gommai daga ginin.

  20. Ministan harkokin wajen Iran ya halarci taron BRICS a Indiya

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya isa ƙasar Indiya domin halartar taron ministocin harkokin wajen ƙasashen BRICS.

    Yayin wannan ziyara, ana sa ran Mista Araghchi zai gana tare da tattaunawa da takwarorinsa daga sauran ƙasashe yayin da yake halartar taron.

    Rahotanni sun ce yaƙin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran shi ne babban abin da ke jan hankali a tattaunawar da mambobin ƙungiyar ke yi.

    Ana gudanar da taron ministocin harkokin wajen BRICS na kwanaki biyu ne a birnin New Delhi na ƙasar Indiya.

    BRICS ƙungiya ce da ta ƙunshi manyan ƙasashe masu tasowa a duniya. Brazil da Rasha da Indiya da China da kuma Afirka ta Kudu su ne manyan mambobin ƙungiyar. Sunan BRICS ya samo asali ne daga haruffan farko na sunayen ƙasashen a harshen Igilishi.

    Iran ta zama cikakkiyar mamba a ƙungiyar shekaru biyu da suka gabata.