Everton na zawarcin Vardy, Arsenal za ta dawo da Ethan Nwaneri

Asalin hoton, Getty Images
Everton na tunanin ɗaukar Jamie Vardy a kyauta, mai shekara 39 bayan gaza sayen ɗanwasan gaba har zuwa lokacin da aka rufe kasuwar cinikin ƴanwasa, kuma tsohon ɗanwasan gaban Ingilan na shirin barin Cremonese. (The Sun)
Da alama David Moyes zai tuntuɓi tsohon ɗanwasan gaban Faransa mai shekara 30, Anthony Martial, wanda kwangilar sa da Monterrey ta Mexico. (Talksport)
Ɗanwasan gefen Ivory Coast mai shekara 33, Wilfried Zaha, na cikin zaɓin da AC Milan ke da shi a ƙoƙarin ta na ɗauko ɗaya daga cikin ƴanwasan da kwangilar su ta ƙare a ƙungiyoyin da suke taka leda.(Gazzetta dello Sport - in Italian)
Ɗanwasan tsakiyar Brazil mai shekara 19, ya damu kan damar buga wasa da ya ke da ita a tawagar Chelsea ƙarƙashin sabon kocinta Xabi Alonso kuma zai iya neman barin ƙungiyar a watan Janairu. (ESPN Brazil)
Arsenal ta zartar da ƴancin sake mallakar ɗanwasan gefen Ingila mai shekara 19, Ethan Nwaneri, wanda ya koma Borussia Dortmund a zaman aro. (Sky Sports Germany)
Ɗanwasan gefen Sunderland mai shekara 21 na tattaunawa da ƙungiyar gasar Saudiyya Al-Ittihad, kuma Fenerbahce da Galatasaray suna zawarcin ɗanwasan Moroccon. (Talksport)
Arabian Falcons, wadda Jonjo Shelvey ke horar wa a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa tana bibiyar tsohon ɗanwasan gefen Manchester United da Ingila mai shekara 26, Jadon Sancho. (Daily Mirror)
Ɗanwasan gaban Argentina mai shekara 29, Lautaro Martinez, ya ce abin alfahari ne a ce ƙungiya irin Barcelona tana neman shi, amma ya ce yana son ci gaba da zama a Inter Milan.(Sky Sports Italia)














