Keir Starmer yayi murabus daga muƙamin firaministan Birtaniya

Asalin hoton, Getty Images
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya sanar da cewa zai sauka daga muƙaminsa na jagoran ƙasar da kuma shugaban jam’iyyar Labour, bayan ya fuskanci matsin lamba daga cikin jam’iyyarsa.
Ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar, inda ya ce ya riga ya sanar da Sarkin ƙasar, Charles game da matakin da ya ɗauka.
Starmer ya ce kafin ya karɓi jagoranci, jam’iyyar Labour tana cikin wani hali na rauni a fannonin siyasa da tattalin arziki. Duk da wannan, ya jaddada cewa ya yi aiki tukuru wajen sauya alkiblar jam’iyyar, inda ya magance wasu manyan matsaloli da suka addabe ta, ciki har da zarge-zargen wariyar addini, tare da dawo da martaba a fannoni kamar tsaro da tattalin arziki.
Ya kuma bayyana cewa a yanzu jam’iyyarsa tana tambayar ko shi ne mafi dacewa da zai jagorance ta zuwa babban zaɓe mai zuwa
Starmer ya kuma ce zai ci gaba da riƙe mukamin firaminista na ɗan lokaci har sai an zaɓi sabon shugaban jam’iyyar kafin dawowar majalisar dokoki daga hutun bazara.
Ya kuma yi alkawarin tabbatar da mika mulki cikin natsuwa, tare da mika cikakken goyon baya ga wanda zai gaje shi, yayin da ya gode wa abokan aikinsa da ma’aikatan gwamnati kan gudunmawar da suka bayar.




