Me zai faru idan kowanne ɗan Najeriya ya samu horon soji?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Imam Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- Aiko rahoto daga, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
A ƴankwanakin nan ne Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa yana da ra'ayin cewa ya kamata kowane ɗan Najeriya ya samu horon soji, saboda darussa masu muhimmanci da irin wannan horo ke koyarwa, ciki har da ɗa'a, da jajircewa da juriyar wahala.
Musa ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin African Leadership Podcast, wanda aka wallafa a shafin YouTube ranar Litinin.
A cewarsa, horon soji, na taimaka wa mutum ya fahimci muhimmancin sadaukar da kai wajen kare ƙasa, tare da koya masa yadda ake aiki tare da wasu domin cimma manufa guda.
"Hakan zai ba mutum wata sabuwar fahimta game da rayuwa. Za ka fahimci ma'anar yunwa, da yadda ake jimre wa tafiyar kwanaki ba tare da samun isasshen barci ba, tare da koyon yadda ake jure wa ƙalubale," in ji shi.
Sai dai kalaman ministan sun haifar da muhawara, inda wasu ke yabawa da ra'ayin, yayin da wasu ke nuna damuwa kan irin tasirin da hakan zai iya yi ga al'umma idan aka aiwatar da shi.
To amma babbar tambayar ita ce me zai faru idan kowanne ɗan Najeriya ya samu horon soji?
Tambayar kenan da BBC ta yi wa Farfesa Muhammad Kabiru Isah, masanin harkokin tsaro a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, wanda ya bayyana ra'ayinsa kan yiwuwar anfani da kuma ƙalubalen da irin wannan tsari zai iya haifarwa.
Karyewar doka da oda
Wani abin da masanin ke ganin zai iya faruwa shi ne karyewar doka da oda.
Ya ce ''Hukumomin tsaro kamar sojoji, da yan sanda da sauran jami'an tsaro na aiki ne karkashin dokoki da ka'idoji da ke tsara yadda suke amfani da karfi. Amma idan fararen hula suka fara ganin cewa suna da ikon shiga harkokin tsaro kai tsaye, hakan na iya haifar da rudani tsakanin abin da doka ta amince da shi da abin da ba ta amince da shi ba''
Ya ƙara da cewa wasu mutane na iya daukar cewa horon soja ya ba su damar daukar mataki kan duk wanda suke zargi da aikata laifi ba tare da bin hanyoyin doka ba. Wannan kuma na iya rage ikon hukumomin tsaro da kuma haddasa rashin bin umarnin gwamnati.
Ya ce a maimakon hakan, ya kamata a karfafa hukumomin tsaro da kuma samar musu da kayan aiki da horo domin su ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Yaɗuwar makamai
A cewarsa, ɗaya daga cikin manyan barazanar da ka iya tasowa ita ce yaduwar makamai cikin al'umma.
Ya bayyana cewa ''Horon soja kan haɗa da koyar da dabarun amfani da makamai da sauran hanyoyin yaƙi. Saboda haka, idan aka bai wa mutane da dama irin wannan horo ba tare da cikakken tsarin sa ido da tantancewa ba, akwai yiwuwar wasu su yi amfani da ilimin wajen aikata laifuka''
Masanin ya ce Najeriya na fama da kalubalen masu garkuwa da mutane, ƴan fashi da makami da kungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.
''Don haka kara yawaitar mutanen da suka kware a dabarun yaƙi na iya zama wata sabuwar barazana ga tsaro maimakon magance matsalar'' inji shi.
Ya ƙara da cewa idan irin wadannan dabaru suka fada hannun bata-gari, za su iya zama kayan aiki da za a yi amfani da su wajen kara haddasa rashin zaman lafiya.
Tashe-tashen hankula
Masanin ya kuma yi gargadin cewa hakan na iya haddasa tashe-tashen hankula a tsakanin al'ummomi.
Ya ce Najeriya kasa ce mai ƙabilu, da addinai da ra'ayoyi daban-daban, kuma a wasu lokuta ana samun saɓani tsakanin al'ummomi ko kungiyoyi.
A cewarsa ''Idan mutane da yawa sun samu horon da zai ba su kwarewa a fannin yaƙi ko dabarun tsaro, irin wadannan rikice-rikice na iya rikiɗewa zuwa manyan tashe-tashen hankula''
A cewarsa, abin da ka iya kasancewa sabani na yau da kullum tsakanin kungiyoyi ko al'ummomi na iya zama rikicin da zai yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi idan bangarorin suna da horo irin na soja.
Ya kara da cewa kasashe da dama suna kokarin rage yawan makamai da dabarun yaƙi a hannun fararen hula saboda gujewa irin wannan barazana.
Daukar doka a hannu
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Haka kuma, masanin ya ce bai wa jama'a irin wannan horo na iya karfafa dabi'ar daukar doka a hannu.
Ya bayyana cewa wasu mutane na iya ganin ba sai sun kai kara ga jami'an tsaro ko kotu ba idan suka samu sabani da wani.
Maimakon haka, za su iya yanke hukunci da kansu ko kuma su yi amfani da karfin da suka samu wajen hukunta wadanda suke zargi.
A cewarsa ''Wannan na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa rashin zaman lafiya a kowace al'umma, domin tsarin shari'a da hukumomin tsaro su ne aka kafa domin su binciki zarge-zarge tare da tabbatar da an yi adalci''
''Ya ce idan mutane suka fara dogaro da karfinsu wajen warware rikice-rikice, hakan na iya haifar da ramuwar gayya, rikice-rikice masu tsawo da kuma tabarbarewar zaman lafiya'' in ji shi.
Masanin ya jaddada cewa duk da muhimmancin koyar da matasa kishin kasa, jajircewa da taimakon al'umma, wajibi ne a yi hattara da duk wani shiri da zai iya sanya fararen hula shiga ayyukan da kundin tsarin mulki ya ware wa jami'an tsaro.































