Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ke janyo kuɗin cizo kuma ta yaya za a kawar da su?
Kuɗin cizo sun haddasa jinkirin tashin wani jirgin saman Qantas daga Italiya zuwa Ostiraliya bayan an gano waɗannan ƙananan kwari a cikin jirgin.
Jirgin da ke kan hanyar Rome zuwa Perth ya samu jinkiri na kusan sa'o'i 17 bayan wasu fasinjoji sun koka cewa ƙwarin sun cije su a lokacin tafiya. Rahotanni sun ce an ba fasinjojin magungunan rage ƙaiƙayi da alamomin rashin lafiyan da cizon ya haifar, sai dai daga baya magungunan sun ƙare.
Mai magana da yawun kamfanin Qantas ya ce an dakatar da jirgin kirar Boeing 787 Dreamliner domin a yi masa cikakken tsaftacewa bayan an gano matsalar kuɗin cizon a wasu kujerun jirgin.
Ya ce kamfanin na ba fasinjojinsa haƙuri kan soke jirgin daga Rome zuwa Perth, yana mai cewa hakan ya bai wa injiniyoyi da ma'aikatan kula da jirage damar gudanar da cikakken aikin tsaftacewa da bincike.
Qantas ya kuma tabbatar da cewa an samar wa duk fasinjojin da abin ya shafa masauki, tare da sake tsara musu tafiye-tafiye cikin sa'o'i 48 daga lokacin tafiyarsu na asali.
Kuɗin cizo ƙananan kwari ne marasa fuka-fuki da ke rayuwa a cikin tufafi, kayan ɗaki da kuma shimfiɗar gado. Cizonsu kan jawo ƙaiƙayi da rashin jin daɗi, amma a mafi yawan lokuta ba sa haddasa wata babbar matsalar lafiya.
Sai dai kuma, kawar da kuɗin cizo abu ne mai wahala, kuma kashe su gaba ɗaya na iya zama mai tsada.
Daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen magance matsalar akwai wanke zanin gado, tufafi da sauran kayan gida kamar labulai da ruwan zafi, sannan a busar da su da injin busar da kaya ko cikin rana. Haka kuma, ana iya sanya waɗannan kayayyaki a cikin jakar leda tare da ajiye su a cikin firiji na tsawon kwanaki uku zuwa huɗu.
Ƙasa da makonni biyu kafin wannan lamari, an gano irin wannan matsala a wasu jiragen ƙasa na kamfanin Southeastern a Birtaniya, lamarin da ya sa aka soke wasu tafiye-tafiye bayan direbobi sun gano kuɗin cizo a cikin taragon jiragen.
A shekarar 2017, kamfanin British Airways ya nemi afuwar wata iyali da ke tafiya daga Vancouver zuwa London bayan da suka fuskanci cizon kuɗin cizo a wani jirgin dare.
Haka kuma, kamfanin jirgin saman Turkiyya ya fuskanci suka a shekarar da ta gabata bayan jaridar New York Times ta ruwaito wasu rahotanni da ke cewa an gano kuɗin cizo a wasu jiragen kamfanin.
A wancan lokacin, an kuma yi zargin cewa kamfanin bai ɗauki matakin da ya dace wajen magance matsalar ba.
Me ke kawo kuɗin cizo?
Kuɗin cizo kan shiga gida ne ta hanyar manne wa jakunkunan tafiya, tufafi ko kayan ɗaki da aka riga aka yi amfani da su.
Da zarar sun shiga gida, sukan ɓuya a wuraren da mutane ke kwana, kamar katifa, gadon kwanciya, kayan ɗaki da ƙananan tsagewa ko a katakon gado ko a bango.
A cewar NHS, kasancewar waɗannan ƙwari a gida ba yana nufin rashin tsafta ba ne, domin ana iya samun su a gidaje masu tsafta da kuma marasa tsafta.
Yadda za a iya rabuwa da kuɗin cizo
Kawar da kuɗin cizo na iya zama da wahala, amma akwai matakan da za a iya ɗauka, ciki har da:
- Wanke zanin gado da tufafin da suka yi dauɗa da ruwan zafi, sannan a busar da su a wuri mai zafi na akalla mintuna 30.
- Sanya tufafi ko zanin gado a cikin jakar leda sannan a ajiye su a cikin firiji na tsawon kwanaki uku zuwa huɗu.
- Tsaftace gida akai-akai, domin ana iya samun waɗannan ƙwari a wurare masu tsafta da marasa tsafta, amma tsaftacewa a kai a kai na taimakawa wajen gano