Manyan kamfanonin ƙasashen waje da suka fice daga Najeriya

Unilever

Asalin hoton, Getty Images/Cheng Xin

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

A ranar Laraba ne ƴan Najeriya suka wayi gari da labarin cewa kamfanin sufuri Uber, ya dakatar da ayyukansa a Najeriya tare da ficewa daga ƙasar.

Uber ya ce ya yanke shawarar barin Najeriya ne bayan shafe kusan shekara 12 yana gudanar da ayyukansa a ƙasar.

Kamfanin ya ce matakin ya kasance "shawara mai matuƙar wahalar yankewa", amma dole ne ya ɗauke shi bisa la'akari da "manyan abubuwan da ya sa a gaba a kasuwancinsa."

A cewarsa, matakin ya shafi Najeriya da Uganda ne kawai, kuma ba zai shafi ayyukan Uber a sauran ƙasashen Afirka ba.

Kamar Uber, wasu manyan kamfanonin ƙasashen waje da dama sun rage ayyukansu ko kuma sun fice daga Najeriya saboda dalilai daban-daban.

Ga wasu daga cikin manyan kamfanonin da suka fice ko suka rage ayyukansu a Najeriya cikin shekaru biyar da suka gabata.

GlaxoSmithKline (GSK)

Glaxo

Asalin hoton, Getty Images/BEN STANSALL

GSK ya dakatar da ayyukansa na kasuwanci a Najeriya a shekarar 2023 tare da ficewa daga ƙasar.

Kamfanin bai bayyana takamaiman dalilin ficewarsa ba. Sai dai watanni da shekaru kafin ficewar, GSK ya sha bayyana damuwarsa kan ƙarancin kuɗin waje a Najeriya.

A rahotonsa na rubu'in farko na shekarar 2023, kamfanin ya ce yanayin kasuwancin Najeriya yana ci gaba da kasancewa mai matuƙar wahala, yayin da ƙarancin kuɗin waje ke shafar yadda yake biyan wasu buƙatun kasuwancinsa da ake buƙatar kuɗin waje.

GSK Nigeria ya ce ya fara samun matsala wajen "ci gaba da samar da kayayyaki ga kasuwa yadda ya kamata."

Kamfanin ya kwashe shekara 51 yana aiki a Najeriya kafin ya rufe kasuwancinsa kai tsaye.

Yanzu GSK yana amfani da tsarin da masu rarraba kayayyaki ke kula da samar da kayayyakin kamfanin a Najeriya.

GSK ya kuma nuna damuwa kan ƙara samun gasa daga kamfanonin cikin gida da kuma kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashe kamar Indiya da China.

ShopRite

Shoprite

Asalin hoton, Getty Images/PIUS UTOMI EKPEI

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A shekarar 2021, masu kamfanin ShopRite na Afirka ta Kudu sun sayar da hannayensu a kasuwancin Najeriya.

Ƴan Najeriya ne suka saya hannayen jarin, inda suka ci gaba da gudanar da kasuwancin a matsayin franchise.

An bayyana cewa matsanancin yanayin gudanar da kasuwanci, faɗuwar darajar naira da ƙarancin kuɗin waje na daga cikin abubuwan da suka sa aka ɗauki matakin.

Sai dai kamfanin gida mai suna Ketron Investment ya ci gaba da gudanar da harkokin ShopRite a Najeriya.

A watan Maris na 2026, reshen ShopRite na ƙarshe da ya rage a Najeriya shi ma ya rufe, sakamakon halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.

Kamfanin ya shigo Najeriya ne a shekarar 2005, kuma cikin sauri ya zama ɗaya daga cikin manyan wuraren sayayya a ƙasar.

Iyalan Najeriya da dama sun dogara da shagunan ShopRite wajen sayen kayan amfanin gida, yayin da farashinsa ya kasance mai sauƙin samu ga mutane da dama.

Tun bayan ficewar kamfanin, wasu manyan kantuna da shaguna sun fara ƙoƙarin cike gibin da ya bari a kasuwar.

Procter & Gamble (P&G)

P and G

Asalin hoton, Getty Images/VCG

Procter & Gamble (P&G) na daga cikin manyan kamfanonin da ke ƙera kayayyakin amfanin gida.

Kamfanin na ƙera kayayyaki da dama da suka haɗa da Ariel, Tide, Downy, Gain, Cascade, Dawn da Febreze.

Haka kuma yana ƙera Pampers, Always da Tampax, da kuma Bounty da Charmin.

A fannin kula da baƙi da lafiya, kamfanin na ƙera Crest, Oral-B da Vicks, sannan yana da kayayyakin Gillette da Braun.

P&G ya dakatar da ayyukan samar da kayayyaki a masana'antunsa na Najeriya a shekarar 2023.

Dalilan da kamfanin ya bayyana sun haɗa da tsadar samar da kayayyaki da kuma wahalar samun kuɗin waje.

Sai dai kamfanin bai daina sayar da kayayyakinsa a Najeriya gaba ɗaya ba. Yanzu yana shigo da wasu daga cikin kayayyakin daga wasu ƙasashe.

Diageo PLC

Diego

Asalin hoton, Ghetty Images/John Keeble

Diageo PLC shi ne babban kamfanin da ke da alhakin samar da Guinness.

A shekarar 2024, kamfanin ya yanke shawarar ficewa daga kasuwar Najeriya ta hanyar sayar da mafi yawan hannayen jarinsa a Guinness Nigeria ga Tolaram Group.

Diageo ya sayar da kashi 58.02% na hannayen jarinsa a Guinness Nigeria saboda matsanancin hauhawar farashi, faduwar darajar naira da kuma tsadar gudanar da kasuwanci.

Kamfanin ya ce wannan mummunan yanayin tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki cikin sauri, tare da sauye-sauyen manufofin tattalin arziki, sun sa gudanar da manyan masana'antun cikin gida ya zama mai tsada kuma ba shi da riba sosai.

Ya kuma nuna damuwa kan faduwar darajar naira, wadda ta ƙara tsadar kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje da kuma sauran harkokin kasuwanci.

Bugu da ƙari, kamfanin ya ce hauhawar farashi ta rage ƙarfin sayen 'yan Najeriya, lamarin da ya haifar da raguwar buƙatar kayayyaki.

Bayan sayar da hannayen jarin, Tolaram Group mai hedikwata a Singapore ya karɓi ragamar mafi yawan hannayen jarin Guinness Nigeria.

Sai dai Diageo zai ci gaba da mallakar tambarin Guinness a duniya, yayin da ya bai wa Guinness Nigeria lasisin ci gaba da samar da abin shan a Najeriya na dogon lokaci.

Unilever

Unilever na daga cikin manyan kamfanonin da miliyoyin ƴan Najeriya ke amfani da kayayyakin da suke samarwa a rayuwarsu ta yau da kullum.

Kamfanin na samar da kayayyakin wanke-wanke kamar Omo da Sunlight, da kuma sabulun Lux.

Sai dai Unilever bai fice daga Najeriya gaba ɗaya ba. Kamfanin ya dakatar da samarwa da sayar da wasu kayayyaki a Najeriya, inda ya mayar da samar da su zuwa wasu ƙasashe.

A lokaci guda, ya ƙara mayar da hankali kan wasu kayayyaki da yake ganin za su iya samun riba a kasuwar Najeriya.

Masu nazarin tattalin arziki sun ce wasu matsalolin tattalin arziki ne suka tilasta Unilever Nigeria rage ayyukansa.

Kamfanin ya koka kan ƙarancin dalar Amurka da kuma faduwar darajar naira, yana cewa hakan ya ƙara tsadar shigo da albarkatun da ake amfani da su wajen samar da kayayyaki da kuma biyan basussukan da ke cikin kuɗin waje.

Haka kuma, kamfanin ya fuskanci babban raguwar kuɗaɗen shiga saboda hauhawar farashin kayayyaki, yayin da mutane ke rage kashe kuɗi wajen sayen kayayyaki.

Wata matsalar da kamfanin ya ambata ita ce tsadar samar da wutar lantarki da rashin tabbas wajen samun ta, da kuma sauye-sauyen manufofin gwamnati da ba a iya hasashen su, waɗanda suke shafar masana'antun cikin gida.