Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sharuɗɗa huɗu na sabuwar yarjejeniyar Musulmai da Kiristocin Najeriya
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Shugabannin addinin Musulunci da Kiristoci fiye da 50 ne suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin mabiya addinan biyu a Najeriya, a yayin ƙaddamar da wata sabuwar ƙungiya da za ta mayar da hankali wajen inganta fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin addinai.
Najeriya na da al'umma sama da mutum miliyan 200 da kuma manyan addinai guda biyu Musulmai da mabiya addinin Kirista.
Galibi Musulmai ne suka fi yawa a yankin arewaci, Kiristoci kuma a kudancin Najeriya. Haka kuma, akwai wasu al'ummomi da ke gudanar da addinan gargajiya.
Rabuwar kan al'umma saboda batun addini ya ɗauki hankali sosai a watannin baya, musamman bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Najeriya da gazawa wajen kare Kiristoci, tare da yin barazanar daukar matakin soji kan ƙasar.
Trump ya alakanta zargin da hare-haren ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya kamar Boko Haram da ISWAP, waɗanda suka shafe sama da shekaru 15 suna kai hare-hare a Najeriya tare da kashe dubban mutane.
Sai dai masu nazari da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun ce duk da cewa Kiristoci na cikin waɗanda aka kashe, mafi yawan waɗanda hare-haren ƙungiyoyin ke kashewa Musulmai ne.
Sakamakon hakan ne shugabannin Musulmi da Kiristocin suka rattaba hannu kan yarjejeniyar, wadda ke da nufin ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna tare da rage tashe-tashen hankula da ake alakanta su da bambancin addini.
BBC ta tattauna da wasu daga cikin jagororin wannan taro domin jin yarjeniyoyin da aka cimma.
Abin da wasu shugabanni suka ce
Ba a yi magana kan kalaman Trump ba a yarjejeniyar da aka rattaba hannu a kanta ranar Laraba, a taron da ƙungiyar Musulmi ta Duniya da ke da hedikwata a Saudiyya ta shirya.
Sai dai gwamnatin Najeriya da wasu ƙungiyoyi daban-daban sun bayyana ƙoƙarin da suke yi na ci gaba da magance matsalar tsaro a ƙasar.
Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, Babban Sakatare na ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI) a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa shugabannin Kiristocin da suka halarci taron sun amince da yarjejeniyar, tare da nuna aniyarsu ta taimakawa wajen ganin ta yi nasara.
"Daga cikin waɗanda suka halarta har da shugaban Kiristoci na Najeriya da sauran jagororin majami'u a Najeriya," in ji shi.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato Sakatare Janar na ƙungiyar Musulmi ta Duniya, Mohammad Al-Issa, yana cewa dukkanin mabiya addinan biyu na maraba da wannan tsari da ya ce ya "buɗe sabon shafi".
"Ba ma musun cewa tsattsauran ra'ayi ya cutar da kowa; kowa ya ga matsalar hakan," in ji shi.
Shugabannin Kiristoci da Musulmi daga Najeriya sun bayyana yarjejeniyar a matsayin wani muhimmin sauyi.
John Praise Daniel, shugaban ƙungiyar shugabannin Kisirocin Arewacin Najeriya, ya ce yana fatan yarjejeniyar za ta rage furta kalaman rarrabuwar kawuna daga wasu malamai.
"Babu buƙatar a riƙa furta kalaman ƙiyayya, babu raina sauran ƙungiyoyin addini, babu kiran wasu mutane kafirai," in ji shi.
Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin ne ya wakilci Shugaba Bola Tinubu wajen taron da aka rattaba hannun, yayin da gwamnonin jihohin arewa uku suka halarta.
Jibrin ya ce: "Gwamnati ta ƙuduri aniyar tabbatar da cewa mun ci gaba da kasancewa haɗe a matsayin ƙasa, duk da bambance-bambancenmu."
Abubuwa 4 da aka yi yarjejeniya a kai
Farfesa Khalid ya ce wannan yarjejeniyar tana sake tabbatar da yyarejejeniyar zamantakewa tsakanin addinai da ƙabilu daban-daban.
"Ba ana kira mutum ya bar addininsa ba ne, amma haɗin gwiwa ne domin yin aiki tare da samun jituwa," in ji shi.
Ya ce yanayin da ake ciki ne ya sa suka ga dacewar a yi wannan yarjejeniya musamman saboda yanayin da ƙasar ke ciki.
Ga muhimman abubuwa huɗu da yarejejeniyar ta ƙunsa kamar yadda Farfesa Khalid ya bayyana wa BBC:
- Samar da haɗaka: Za a samar da wata ƙungiya da za ta yi aiki tare tsakanin al'ummar ƙasar ba tare da nuna bambance-bancen addini da kabila ba wajen haɗa kan al'umma.
- Bunƙasa harkar ilimi: A ƙarƙashin yarjejeniyar akwai yadda za a inganta harkar koyarwa ta yadda malamai za su riƙa da'awa da gudanar da karatuttukansu a kan mimbari, da kuam ganin sun bi tsarin bayar da ilimi mai kyau ba tare da cusa ƙiyayya a tsakanin juna ba.
- Malamai su daina furta kalaman ƙiyayya: An cimma matsayar cewa kowane bangare ya ja hankali duk malaman da suke wa'azi da su kiyaye daga furta kalaman da za su iya harzuƙa al''umma da "jefa mutane cikin halin ha'ula'i".
- Inganta rayuwar matasa: A ƙarƙashin yarjejeniyar za a ɓullo da tsare-tsaren da za su taimaki rayuwar matasa su samu makoma mai kyau da ilimi ba tare da kauce hanya ko cusa ƙiyayya a zukatansu ba.
Farfesa Khalid ya ce waɗannan matsaya da aka cimma za su taimaka matuƙa wajen daƙile matsalar tsaron Najeriya, domin ya ce: "yardar ma a zo a zauna wani abu ne".
Ya kuma ce an buƙaci malamai su daina amfani da addini don biyan buƙatar siyasa, saboda hakan ne ke sa ana jifar juna da kalaman da za su haifar da ƙiyayya da gaba da juna.
Ta wace hanya za a aiwatar da yarjejeniyar
Sakatare Janar na JNI ya bayyana cewa an tsara hanyoyin da za a cimma wannan nasara.
Daga ciki akwai manyan ƙasa da za su riƙa sanya ido kan yadda lamuran ke tafiya domin bayar da shawarwarin wajen da ya kamata a gyara.
Farfesa Khalid ya ƙara da cewa akwai ma'aikatan da za a ɗora wa alhakin bibiyar tsarin da ɓullo da hanyoyin da za su sa yarjejeniyar ta yi tasiri.
"Akwai ma'aikata na musamman da za a ɗora musu nauyin shimfida wadannan shirye-shirye da kuma bibiya don ganin ina abin ya yi tasiri da inda bai yi tasiri ba. Kuma mene ne dalilin da ya sa bai yi tasiri ba, idan kuma ya yi tasiri ta ina za a inganta wannan idan ya yi amfani.
Wannan yarjejeniyar ta zo ne a daidai lokacin da Najeriyar ke tunkarar zaɓen watan Janairun 2027, kuma ana ganin addini da ƙabilanci za su sake taka rawa a siyasar Najeriya.
Jam'iyyar APC mai mulki za ta sake tsayawa takarar shugaban ƙasa da tikitin Musulm da Musulmi, abin da ya haifar da zazzafar muhawara a ƙasar, kamar yadda ta yi a 2023.
Matakin dai ya karya tsohuwar al'adar daidaita tikitin shugaban ƙasa tsakanin manyan addinan biyu na ƙasar wato Musulmi da Kirista.