Za mu fito da ƙarfinmu idan yaƙin ya sake dawowa sabo - Iran
Rundunar juyin juya halin Iran ta yi barazanar ɗaukar matakai masu tsauri da ƙarfin hare-hare idan har wani sabon yaƙi ya sake ɓarkewa tsakanin Iran da Amurka.
Kamfanin dillancin labarai na Fars, ya ambato wani babban jami'in rundunar, Rasoul Sanaei-Rad na cewa:
“Maƙiya na tunanin cewa ta hanyar haddasa rarrabuwar kawuna a cikin gida da matsin tattalin arziki za su iya maimaita irin abubuwan da suka faru a watan Janairu, kuma suna ɗaukar matakan cimma wannan buri.”
A jiya kuma, mataimakin babban hafsan hafsoshin sojojin Iran, Alireza Sheikh, ya bayyana cewa ƙasarsa ta shirya domin dogon yaƙi da kuma ci gaba da gudanar da ayyukan soji.
Ya ce manufar tsaron Iran ta sauya daga ta kare kai kawai zuwa manufar hana maƙiyi da kuma ɗaukar mataki kai tsaye idan buƙata ta taso.
Haka kuma ya ce ƙarfin Iran wajen ƙera makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa na daga cikin manyan abubuwan da ke ba ta damar ci gaba da gudanar da ayyukan soji na dogon lokaci.