Hare-haren jirage marassa matuƙa sun faɗa Otal a yankin Tigray
Mazauna da ma’aikatan agaji a garin Adwa na yankin Tigray sun ce hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da dama da aka kai a garin Adwa da ke tsakiyar yankin Tigray sun yi sanadin mutuwar fararen hula tare da lalata otal-otal da wuraren kasuwanci.
A cewar mazauna garin da suka zanta da BBC Tigrigna, hare-haren guda huɗu da aka kai a ƙarshen daren Asabar sun afkawa Otal ɗin Segen da kewaye, inda suka kashe mutum 11. Shaidu sun ce mutum tara sun mutu nan take, yayin da wasu biyu suka rasu a asibiti sakamakon raunukan da suka samu. Hudu daga cikin waɗanda suka mutu mata ne.
Wani ma’aikacin Otal ɗin Segen mai suna Zerit Assefa ya bayyana harin a matsayin mai matuƙar muni, yana cewa an harbi wata mota da ke ajiye a harabar otal ɗin, lamarin da ya kashe masu mashaya da kuma wasu da ke haya a ƙarƙashin ginin.
“Harin ya zo ne ba zato ba tsammani, kuma ya tayar da hankali matuƙa. Mun ga gawarwakin da idanunmu,” in ji shi, yana mai ƙara da cewa yanzu otal ɗin ba ya aiki.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa mutum tara sun mutu a Adwa, tare da ambato ma’aikatan agaji da suka tabbatar da mutuwar wasu mutum takwas a wani hari da aka kai sansanin ’yan gudun hijira a Sheraro, wanda ya sa adadin waɗanda suka mutu ya kai 17. Reuters ya ce bai samu damar tantance ko su wa suka kai hare-haren ta sama ba.
Shaidu sun kuma ce an kai hare-hare kan Otal ɗin Shewit International da kuma Pan Africa Hotel a Adwa a yammacin ranar Asabar.
Wata mai sayar da kofi a yankin mai suna Leya Grimay ta ce firgici ya bazu a faɗin garin yayin da shaguna suka rufe, tituna kuma suka yi tsit. Ta ce an yi mummunar barna ga gine-ginen otal-otal ɗin, amma ba a samu rahoton rasa rai ba.
Manajan Otal ɗin Shewit ya tabbatar wa BBC cewa an kai harin, sai dai ya ƙi bayar da ƙarin bayani.
BBC ba ta samu damar tabbatar da inda hare-haren jiragen marasa matuƙa suka fito ba, ko adadin waɗanda aka ce sun mutu, ko kuma tantance waɗanda suka rasa rayukansu.
A birnin Mekelle, hedikwatar yankin Tigray, inda dakarun gwamnati suka shiga ba tare da fuskantar turjiya ba a makon da ya gabata, mazauna yankin sun ce rayuwa na ci gaba da komawa yadda take a hankali, inda shaguna ke buɗewa, sannan an dawo da ayyukan wayar salula da intanet bayan katsewar da ta shafe mako guda.
Sai dai mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa har yanzu akwai fargaba a tsakanin jama’a.
Mazauna yankin Gabashin Tigray, waɗanda suka ce sun ga yadda dakarun Tigray ke sake shirya kansu a kusa da garin Wukro, sun bayyana damuwa kan yiwuwar barkewar sabon rikici.
Bayan arangamar soji da aka yi a kudancin yankin Tigray tun daga ranar 23 ga Satumba, gwamnatin Tigray karkashin jagorancin TPLF ta sanar da cewa za ta ci gaba da gwagwarmayar makami a wajen birnin Mekelle.