Wane ne ya gaji Sheikh Dahiru Bauchi shekara ɗaya bayan rasuwarsa?

- Marubuci, Imam Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC World News
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
A ranar 27 ga watan Nuwamban 2025 ne Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, rasuwa, bayan shafe kusan shekara ɗari yana rayuwa, koyarwa da yaɗa ilimin addinin Musulunci.
Yanzu shekara guda kenan da rasuwarsa, amma tasirinsa na ci gaba da bayyana a tsakanin dubban almajiransa da mabiyansa, musamman a Najeriya da wasu sassan Afirka ta Yamma.
Sheikh Dahiru Bauchi ya shafe fiye da shekaru saba'in yana koyar da Alƙur'ani, tafsiri da sauran ilimomin addinin Musulunci, tare da taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya.
Rasuwarsa ta bar babban gibi, ba kawai a cikin iyalinsa da dubban almajiransa ba, har ma a fagen ilimin addini da jagorancin Tijjaniyya, inda ya kasance ɗaya daga cikin manyan jagororin da suka yi tasiri.
Yayin da ake cika shekara guda da rasuwarsa, tambayar da mutane da dama ke yi ita ce: Su waye suka karɓi nauyin ci gaba da ayyukan da ya assasa? Wa ke ci gaba da koyar da iliminsa, bayar da fatawowi da jagorantar mabiyansa a harkokin addini da na ɗarikar Tijjaniyya?
Domin amsa waɗannan tambayoyi, BBC ta tattauna da Malam Aminu Sheikh Dahiru Bauchi, ɗaya daga cikin 'ya'yan marigayin, domin jin yadda iyalinsa da almajiransa ke ci gaba da tafiyar da gadon da ya bari.
Gadon jagorancin Tijjaniyya

Asalin hoton, SHEIKH IBRAHIM SALEH
Kafin rasuwarsa, Sheikh Dahiru Usman Bauchi na daga cikin manyan jagororin ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya, ɗaya daga cikin ɗarikun Sufaye masu dimbin mabiya a Afirka.
A cewar ɗan marigayin, Malam Aminu Dahiru Bauchi, Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini ne ya ɗauki nauyin ci gaba da jagorancin mabiyan Tijjaniyya bayan rasuwar mahaifinsa.
Ya ce tun kafin rasuwar Sheikh Dahiru, shi da Sheikh Sharif Ibrahim Saleh sun kasance suna jagorantar harkokin ɗarikar tare.
Malam Aminu ya ce: "Tun kafin rasuwarsa, tare suke jagorancin Tijjaniyya da babanmu, Sheikh Sharif Ibrahim Saleh. Bayan rasuwarsa, a yanzu nauyin ya koma kansa, don haka shi ne yake ci gaba da jagorantarmu."
Ya ƙara da cewa: "Sheikh Sharif Ibrahim Saleh shi ne ubanmu, shi ne uban duk wani ɗan Tijjaniyya, don haka mu ba marayu ba ne."
Gadon ilimi: Wa ke ci gaba da koyarwarsa?

Asalin hoton, KHALIFA IBRAHIM DAHIRU BAUCHI
A cewar Malam Aminu, babban ɗan marigayin, Khalifa Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, ne ya gaji mahaifinsa ta fuskar bayar da fatawowi da kuma ci gaba da koyar da ilimin addinin Musulunci.
Haka kuma, sauran 'ya'yansa, waɗanda su ma fitattun malamai ne, na ci gaba da yaɗa ilimin da aka san Sheikh Dahiru Bauchi da shi, ta hanyar koyarwa da wa'azi.
Malam Aminu ya ce rasuwar Sheikh Dahiru ba ta kawo ƙarshen ayyukan ilimin da ya assasa ba, domin ana ci gaba da tafiyar da su ta hanyar makarantun da ya bari da kuma almajiran da ya horas.
Ya ce: "Bayan rasuwar Shehi, har yanzu muna ci gaba da koyarwar da ya yi. Ci gaba ma ake samu sakamakon makarantun da ya bari, waɗanda suka kai ɗaruruwa."
Ya ƙara da cewa sauran almajiransa ma na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da dorewar koyarwar da ya bari.
Gadon haɗa kan al'umma

Asalin hoton, SARAUTA TV
Baya ga fannin ilimi da jagorancin Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Bauchi ya kasance ɗaya daga cikin malaman addinin Musulunci da suka yi fice wajen haɗa kan al'umma da samar da fahimtar juna tsakanin mutane masu mabambantan ra'ayoyi.
A cewar Malam Aminu Sheikh Dahiru Bauchi, ɗaya daga cikin 'ya'yan marigayin, Khalifa Muhammadu Sanusi II, Sarkin Kano, ne ke ci gaba da wannan fanni na gadon mahaifinsa.
Ya ce hakan na da nasaba da irin kiraye-kirayen da Sarkin ke yi na tabbatar da adalci ga talakawa, da kuma ƙoƙarinsa na haɗa kan mabiya addinin Musulunci ba tare da la'akari da bambancin ra'ayoyinsu ba.
Malam Aminu ya ƙara da cewa irin waɗannan halaye na daga cikin abubuwan da suka sa yake ganin Khalifa Muhammadu Sanusi II na ci gaba da wata muhimmiyar manufa da Sheikh Dahiru ya shahara da ita.
Wanene Sheikh Dahiru Usman Bauchi?

Asalin hoton, SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wata tattaunawa da BBC ta yi da Sheikh Dahiru Bauchi a 2019 da kuma 2024 ya shaida cewa an haife shi ne a ranar 28 ga watan Yunin 1927, dai-dai da 2 ga watan Muharram 1346, wato Shehin malamin ya rasu yana da shekaru 98 kalandar Turawa amma a ta Musulunci ya rasu yana shekara 100 da ƴan watanni kenan.
An haife shi a wani gari da ake kira Nafada da ke jihar Gombe, wanda garin mahaifiyarsa ce, "kasancewar a al'adar Fulani ana haihuwar dan fari ne a gidansu mahaifiyarsa," in ji shi.
Ya kara da cewa: "Ni Bafulatani ne ta wurin uwa da uba. Dukkanin kakannina hudu Fulani ne.
"Sunan mahaifiyata Maryam 'yar Hardo Sulaiman. Sunan Mahaifina Alhaji Usman dan Alhaji Adam."
Sheikh Dahiru ya haddace kur'ani a wurin mahaifinsa kafin daga bisani ya tura shi Bauchi domin neman tilawa.
Mahaifinsa almajirin Shehu Ibrahim Nyass ne kuma mukaddami a cikin darikar Tijjaniyya ta hanyar Amadu Futiy kafin Shehi Ibrahim Nyass ya bayyana.
"Mahaifiyata ita ma ta je Kaulaha har sau biyu, kuma Shehu ya kaddamar da ita har ya ba ta carbi, saboda haka ni da mahaifina da mahaifiyata da 'ya'yana da jikokina duk gaba daya mun taru a cikin Shehu Ibrahim,"
Ya yi auren fari a shekarar 1948 lokacin yana da shekara 20 "da wata daya."



























