Wuraren da aka samu rikici tun bayan fara yaƙin neman zaɓe a Najeriya

Asalin hoton, Amnesty International/FB
Tun daga lokacin da aka fara shirye-shiryen zaɓen 2027 a Najeriya, an fuskanci matsalolin hare-hare, musamman a wuraren tarukan siyasa da yaƙin zaɓe da sauran su.
Bayan ƴan jam'iyyu daban-daban da suke zargin juna da kai wa juna hare-hare, a ɗaya ɓangaren kuma ƴan takara ne suke maganganun masu zafi a kan abokan takararsu.
A watan Agustan bana, Hukumar INEC ta buƙaci ƴantakara, ciki har da jagororin jam'iyya su sa hannu a yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a lokacin kamfe da ma ranar zaɓe.
Irin waɗannan matsalolin ne suka sa aka yi sabuwar dokar zaɓe a shekarar 2026, wadda ta sa aka tilasta wa dukkan jagororin jam'iyya su sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya.
Hare-haren baya
Bayan hare-haren da aka kai a baya, kwanakin da suka gabata, an kai wani harin a jihar Delta, inda aka kashe mutum shida, sannan wasu da dama suka jikkata a lokacin.
A lokacin da Sanata Ovie Omo-Agege ya ke yaƙin zaɓe a garin Udeere ne taron ya hargitse zuwa rikici. Omo-Agege yana takarar sanata ne a ƙarƙashin jam'iyyar NDC, inda binciken farko ya tabbatar da cewa mutum shida sun rasu, sannan da dama sun jikkata.
Haka kuma a daren jiya, rundunar ƴansandan jihar Edo ta tabbatar da cewa an kai wani harin da ke da alaƙa da siyasa a jihar.
Ƴansandan sun ce ƴanbindiga ne suka kai hari a kan ƴaƴan jam'iyyar NDC da suke taron yaƙin zaɓe a birnin Benin.
Hare-hare da dama dai sun yi ajalin rayukan mutane da dama a 2026, a daidai lokacin da zaɓen 2027 ke tunkarowa.
Harin farko

Asalin hoton, Getty Images
Ita ma jam'iyyar ADC ta fuskanci hare-hare, haka ita ma jam'iyyar PDP ta fuskanci haka, inda jam'iyyun na hamayya suka fuskanci hare-hare a lokuta daban a wasu jihohi.
Daga cikin jihohin da aka samu rahoton kai hare-hare masu alaƙa da siyasa akwai Enugu da Benuwei da Legas.
A jihar Gombe, a ranar 11 ga Nuwamba, waɗanda ake zargin ƴan daba ne suka tare hanya, tare da kunna wa tayoyi wuta domin hana ɗantakarar gwamnan jihar a PDP, Isa Pantami wucewa.
A jihar Katsina, wasu ƴan daba ne suka kai farmaki kan ayarin motocin yaƙin zaɓen gwamnan jihar, Dikko Radda na jam'iyyar APC.
Ƴansanda sun ce masu zanga-zanga ne suka tare hanyar Ƴankara, sannan suka fara jifar ayarin da motoci, tare da ƙona fastocin kamfe bayan Gwamna Radda ya wuce a hanyarsa ta zuwa taron yaƙin zaɓe a Faskari.
Mutane da dama ne suka jikkata a farmakin, sannan an ruwaito cewa an ƙona wasu motoci.
Tsarin mulkin Najeriya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da wahala a iya cire zaɓe guda ɗaya da aka yi a Najeriya da ba za a samu rikice-rikice ba tun daga lokacin da ƙasar ta samu ƴancin kai a shekarar 1960.
An yi zaɓen farko a ƙasar ne a shekarar 1964-1965, kuma ya samo asali ne daga rikicin da aka samu kafin lokacin.
Mutane da dama ne suka rasa rayukansu a tsakankanin, musamman a yankin kudu maso yamma, kamar yadda rahoton HRW ya bayyana.
Haka kuma an samu irin wannan matsalar a zaɓen 1983, inda aka kashe mutane da dama, sannan aka yi asarar abubuwa da dama na dukiya.
Ga waɗanda za su tuna, a lokacin zaɓen 1993, wanda mutane da dama suka tunanin shi ne ya fi inganci a tarihin ƙasar, ba a samu rahoton hargitsi ba.
Amma bayan shugaban mulkin sojin ƙasar na lokacin, Janar Ibrahim Babangida ya soke zaɓen, sai rikici ya ɓarke.
A lokacin da aka fara gangamin 'Campaign for Democracy (CD),' a ƙarƙashin jagorancin Beko Ransom-Kuti, inda aka buɗe wuta kan mai uwa da wabi kan wasu mutane da rahotanni suka nuna cewa suna gudanar da zanga-zangar lumana ne a watan Yulin shekarar.
Zaɓukan da suka gabata
Amma har yanzu ba a samu wani babban sauyi ba wajen haddasa tashe-tashen hankula a lokacin zaɓe da bayan zaɓe tun bayan da Najeriya ta koma mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.
Bayan da Hukumar INEC ta ayyana Olusegun Obasanjo a matsayin wanda ya lashe zaɓen 1999, sai wani sabon rikicin ya kunno kai.
Haka kuma, aƙalla mutum 100 ne suka rasa rayukansu a jihohin Najeriya daban-daban yayin babban zaɓen shekarar 2003 da ya bai wa Obasanjo nasarar wa'adi na biyu.
Haka kuma ƴan ƙasar 300 ne aka ruwaito sun mutu a zaɓen shekarar 2007, yayin da sama da mutum 70 suka rasa rayukansu kafin gudanar da zaɓen.
A shekarar 2011 kuwa, bayan zaɓen da ya kai Goodluck Jonathan kan karagar mulki, aƙalla mutum 800 suka rasu a tarzomar da aka yi a jihohi 12 na Arewacin Najeriya.
Wannan lamari shi ne mafi muni a tarihin siyasar Najeriya.
Ba wannan kaɗai ba, kafin da bayan babban zaɓen shekarar 2015, sama da mutum 100 sun rasa rayukansu, a cewar ƙungiyar International Crisis Group (ICG).
Har ila yau, tawagar masu sa ido kan zaɓe ta Tarayyar Turai ta tabbatar da cewa aƙalla mutum 100 ne suka mutu a lokacin zaɓukan shekarun 2015 da 2019.
Sai dai kuma, tsakanin watan Afrilun 2014 da Mayun 2022, bincike ya nuna cewa aƙalla mutum 300,000 ne suka ɓace a lokacin manyan zaɓukan da aka gudanar a faɗin Najeriya.
Haka kuma, an yi garkuwa da jami'an zaɓe 51 a lokacin yakin neman zaɓe.
Sanadiyyar rikice-rikice
A wasu bincike da aka gudanar, an gano cewa akwai abubuwa da dama da suka yi sanadiyyar rikice-rikicen, waɗanda suka yi sanadiyyar muttane, da asarar dukiya mai ɗimbin yawa.
Daga cikin matsalolin da ake samu a rikice-rikicen akwai duka da kashe-kashe da satar akwatin zaɓe da garkuwa da mutane da kalaman tunzura da sauran matsalolin daban.
Bayan fararen hula da suka rasu, rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro da dama ma sukan rasu a lokacin zaɓe.



























