Mai haƙa ƙabarin da ya binne gawarwaki 18,000 a Gaza cikin shekaru uku

....
    • Marubuci, Marwa Gamal
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

"Shekaruna 61, kuma tun shekarar 1986 nake aikin binne gawa. Amma duk tsawon shekarun da na yi ina wannan aiki, ban taɓa binne gawarwaki da yawa kamar waɗanda na binne a cikin shekaru ukun da suka gabata ba."

" tun bayan ɓarkewar yaƙin, na binne gawarwaki sama da 18,000. Ban taɓa tunanin cewa zan binne gawarwaki masu yawa haka ba, ko da kuwa zan rayu tsawon rayuwa biyu ko uku maimakon guda ɗaya."

Da waɗannan kalamai ne Youssef Ahmed Salim Abu Hatab, wani mai haƙa ƙaburbura a Gaza, ke bayyana ba wai yawan mutanen da suka mutu a yaƙin kaɗai ba, waɗanda a ganinsa ba a taɓa ganin irinsu ba, har ma da ƙarancin makabartu a Gaza idan aka kwatanta da dimbin gawarwakin da ake binnewa.

Matsalar ba ta tsaya ga yawan gawarwakin da ake binne wa ba, domin akwai kuma ƙarancin abubuwan da ake buƙata wajen yi musu sutura da kuma binne su. Abu Hatab ya ce:

"Muna cikin mawuyacin hali. Babu likkafani da za a yi wa mamata sutura, babu ko sabulun wanka da za a yi musu tsarki, sannan babu isasshen fili da za a haƙa ƙarin ƙaburbura.

"Idan har masu rai ba su da wurin zuwa saboda raguwar wuraren da mutane za su iya rayuwa a cikinsu, da kuma sauye-sauyen da aka yi wa layin raba yankunan da Isra'ila ke iko da su fiye da sau ɗaya, ina ga matattu fa?"

Girmana mamata ko kuma zaginsu!

...

Matsalar ta ƙara tsananta saboda ƙarancin kayan gini na asali da ake buƙata wajen gina ƙaburbura. Abu Hatab ya tambaya da cewa: "Ashe duwatsu da fale-fale ba su ne mafi sauƙin abubuwan da ake buƙata wajen gina ƙaburbura ba?!"

Irin waɗannan kayan da ake ganin ba su da wahalar samu, sun yi ƙaranci a Gaza, lamarin da ya sa wasu ke cire su daga gidajen da aka bari aka raba da su, waɗanda hare-haren bama-bamai suka lalata. Daga nan sai su zo wurinmu kamar 'yan kasuwa, suna sayar mana da dutse ko fale-falen a kan kuɗin shekel bakwai, wato sama da dala biyu.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Girmama mamaci na nufin binne shi, to abin da ke faruwa a Gaza yanzu wulaƙanta mamata ne. Sau da dama na sha samun kaina a halin binne iyalai baki ɗaya kai tsaye a ƙarƙashin yashi, ba tare da haƙa musu kabari ba."

Abu Hatab ya ci gaba da cewa: "Wannan ba shi ne kaɗai abin da na tilasta wa kaina yi a wannan yaƙin ba. Na kuma sha buɗe ƙaburburan mutanen da suka rasu shekaru masu yawa da suka gabata, domin binne gawar shahidai daga cikin iyalansu da suka mutu a wannan yaƙin, waɗanda ba a samu wasu ƙaburbura da za a binne su a ciki ba.

"Mun buɗe ƙaburburan mutanen da suka rasu shekaru 30 ko 40 da suka gabata domin binne wani shahidi daga cikin iyalansu tare da su. Bayan wani lokaci kuma, sai mu sake buɗe kabarin domin binne wasu sabbin shahidai daga cikin iyalin. Haka dai ake ci gaba. Duk lokacin da wani ɗan iyali ya mutu a matsayin shahidi, sai mu buɗe kabarin iyalinsa mu binne shi a saman waɗanda aka binne a baya."

Ya ƙara da cewa: "Makabartar da aka tsara za ta ɗauki gawarwaki 20, yanzu an binne gawarwaki 60 a cikinta. Wannan ƙarancin wuraren binne gawa ya sa farashin kowane sabon kabari ya kai kwatankwacin dala 300, kuɗin da mafi yawan mutanen Gaza ba za su iya biya a halin yanzu ba.

"Saboda haka, idan wani sabon yaƙi ya ɓarke aka kuma samu dimbin waɗanda suka mutu, za mu binne su ne a kan tituna. Ba mu da makabartu. Shin akwai wanda zai iya fahimtar ainihin ma'anar wannan magana? Kun fahimci abin da nake nufi?"

Yana fama da cutar daji yana haƙa ƙaburbura

...

Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsunduma cikin wannan sana'a shi ne Siraj Siam, mai shekara 16. Siraj na fama da cutar dajin hanji, kuma ba ya samun magani saboda babu shi a Gaza. Halin ƙuncin da yake ciki ne ya tilasta masa shiga wannan sana'a, bayan ya tsinci kansa cikin rashin ikon ɗaukar nauyin iyalinsa mai mutum huɗu.

A kowace rana, Siraj kan tashi ya je makabarta domin haƙa ƙaburbura da shimfiɗa musu bulo, aikin da yake samun kuɗin da ya kama daga shekel 20 zuwa 30 a rana, kwatankwacin dala shida zuwa tara.

Siraj ya bayyana sana'arsa da kalma guda da ya maimaita cikin sauri sau da dama, yana cewa: "Gajiya, gajiya, gajiya."

Kafin ya ƙara da cewa: "Abubuwan da suka fi wannan muni ne suka tilasta mini shiga wannan sana'a mai wahala. Mahaifina da mahaifiyata sun tsufa kuma ba su da lafiya, don haka ba sa iya aiki. Babu wani a gidan da zai iya yin aiki ya nemo abin da za a ci, sai ni. Kuma ban samu wata sana'a da zan yi ba face wannan."

Siraj ya yi shiru na wasu mintuna kafin ya ci gaba da magana, inda ya ce:

"Kafin yaƙin, na kasance ɗalibi mai ƙwazo, kuma ina samun maki masu kyau a dukkan darussa. Amma yanzu har na kusa mantawa da karatu, baya ga cutar da nake fama da ita da kuma rashin samun magungunan da ba su samuwa."

Yadda ake binne gawa a ƙabari ɗaya cikin ƙunci

شخص يدفن جثة

A wani labari da ke ƙara bayyana halin da ake ciki na binne gawarwaki a kabari ɗaya a Zirin Gaza, Abu Ahmed ya bayyana cewa an tilasta masa binne dukkan gawarwakin 'yan uwansa da aka gano kwanan nan a ƙarƙashin baraguzan gine-gine a kabari guda.

Ya ce: "Gawarwakin, ko kuma a ce ragowar jikunan da ake binne wa tare, galibi ba su cika ba. Ƙarancin wuraren binne gawa da kuma halin da aka tilasta mana rayuwa a ciki ne suka sa aka koma binne mutane da yawa a kabari ɗaya.

"Abin da ya ɗan rage mini zafin wannan lamari shi ne yadda nake tunatar da kaina cewa waɗannan shahidai ne, waɗanda tun daga lokacin da aka jefa musu bama-bamai rayukansu suka koma ga Mahaliccinsu. Ba sa jin komai game da abin da ya faru da gawarwakinsu bayan haka, tun daga kwanciya a ƙarƙashin baraguzan gine-gine na tsawon shekaru, har zuwa gano ragowar jikunansu da binne su a kabari ɗaya. Rai na wurin Allah yake, ƙasa kuma ta ƙasa ce."

Ya kammala da cewa: "Zan gaya maka wani abu da ƙila zai ba ka mamaki. Idan aka ba ni zaɓi tsakanin binne kowane ɗan iyalina a kabarinsa na daban, ko kuma ba da wannan fili ga wani iyali mai rai su kafa tanti su zauna a wurin, zan zaɓi na biyun.

"Masu rai sun fi muhimmanci fiye da matattu. A wurin da kake son haƙa sabon kabari, ka kafa tanti ka zauna a ciki. Wannan ba raina mamatanmu ba ne, a'a, imani ne cewa rayukansu suna cikin ni'imar Mahaliccinsu a Aljanna, kuma abin da ya faru da ragowar jikunansu a wannan duniya ba zai cutar da su ko kaɗan ba."

'Ƙaburbura cike da gawarwaki'

Abu Omar ya sha bamban da ra'ayin Abu Ahmed kan binne gawarwaki fiye da ɗaya a kabari guda. Ya ce sun yi duk mai yiwuwa domin binne kowane ɗan iyalinsa a kabarinsa na daban bayan an gano gawarwakinsu.

"Ya isa kawai sun shafe shekaru ba tare da an binne su yadda ya kamata da mutunta mutuncinsu na bil Adama ba. Amma duk ƙoƙarin da na yi ya ci tura."

Abu Omar ya ja dogon numfashi kafin ya ci gaba da cewa:

"Na duba duk inda nake... A ina zan binne 'yan iyalina? Ban samu ko ɗan ƙaramin fili ba. Hatta wuraren da ke kewaye da makabartu sun cika da tantunan 'yan gudun hijira, waɗanda suka bazu a wuraren bayan filin da sojojin Isra'ila suka ware domin fararen hula su zauna a Gaza ya yi ƙanƙanta da ba zai iya ɗaukar su ba."

Ya ƙara da cewa: "Na miƙa al'amarina ga Allah. Babu abin da zan iya yi. Na buɗe kabarin iyalina, na tattara ƙasusuwan waɗanda aka riga aka binne a ciki na mayar da su gefe guda, domin in samar da wurin da zan sanya gawarwakin 'yan iyalina da muka ciro daga ƙarƙashin baraguzan gine-gine."

Ma'aikatar Lafiya ta Gaza da Hamas ke gudanarwa ta ce yaƙin ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa 74,645. Majalisar Ɗinkin Duniya na ɗaukar alkaluman ma'aikatar a matsayin abin dogaro.

Fiye da mutum 1,600 ne suka mutu tun bayan tsagaita wutar da aka cimma a watan Oktoban shekarar da ta gabata.