'Ƴan jarida za su fara yi wa sojoji rakiya wajen ayyukan tsaro'
Gwamnatin Najeriya na nazarin wani sabon tsari da zai saka 'yan jarida yi wa sojoji rakiya yayin wasu zaɓaɓɓun ayyukan tsaro kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
An ce wannan mataki na da nufin inganta yadda ake ruwaito harkokin tsaro tare da bai wa jama’a damar fahimtar ainihin abin da ke faruwa a fagen yaki da ta’addanci da sauran barazanar cikin gida.
Ministan tsaro, Janar Christopher Musa, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taron tsaro na kasa da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) ta shirya a Abuja.
Ya ce wannan tsari zai kara dankon zumunci tsakanin kafafen yada labarai da hukumomin tsaro tare da karfafa gaskiya da fahimta a ayyukan soji.
Ya kara da cewa rawar da kafafen yada labarai ke takawa ba karama ba ce wajen gina fahimtar jama’a game da harkokin tsaro da tabbatar da zaman lafiya a kasa.
A cewarsa, a wannan zamani, yaki ba wai kawai a filin daga ake gwabzawa ba, har ma yana da nasaba da bayanai da labaran da ake yadawa, wanda ke sanya ‘yan jarida zama muhimman abokan hulda a tsarin tsaron kasa.
Ministan ya jaddada cewa nasarar ayyukan tsaro ba wai kawai auna ta ne da nasarorin soji ba, har ma da yadda jama’a ke da yarda da hukumomin tsaro.
Ya kara da cewa ingantacciyar hadin gwiwa tsakanin ‘yan jarida da jami’an tsaro za ta taimaka wajen kawar da yada jita-jita, sabani a rahotanni, da kuma kara amincewar jama’a yayin da Najeriya ke fuskantar kalubalen tsaro daban-daban.