Jihohin da Tinubu ya fi samun ƙuri'a a zaɓen fitar da gwani

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Wasu masana siyasa a Najeriya, na nuna shakku a kan yawan kuri'un da aka ce Shugaba Bola Tinubu ya samu a zaben fitar da gwani da jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta gudanar.

Masanan sun ce nasarar da Tinubun ya samu ba abin mamaki ba ne, amma yawan kuri'un da aka bayyana su ne abin mamakin.

Farfesa Abubakar Kari, na jami'ar Abuja, ya ce akwai ayar tambaya wadda za a sa a kan jumullar kuri'un da Shugaba Tinubu ya samu.

Cikin wata hira da ya yi da BBC, Farfesa Kari, ya ce," Ba makawa dama zai samu wannan takara domin wanda suka yi takara da shi ba a san shi ba.

To amma babban abin mamakin shi ne zaben da aka yi a dubban rumfuna ya samu miliyan takwas da 'yan kai, to sai ga shi wanda aka ce an yi a daidaikun wurare a ce an samu kuri'a fiye da miliyan 10, gaskiya wannan jumulla mutane da dama za su yi shakku a kanta."

" Baya ga shakku a kan wannan zabe ko kuma yawan kuri'un da aka ce Tinubun ya samu a zaben fitar da gwanin da mutane za su yi, tsoro ma zai shiga zukatan jama'a a kan abin da zai je ya dawo." In ji Kari.

A ranar Asabar, 23 ga watan Mayun 2026, ne jam'iyyar APC ta gudanar da zaben fitar da gwamnoni inda a washe gari kuma jam'iyyar ta tabbatar da shugaban ƙasar, Bola Tinubu a matsayin dantakararta a zaɓen 2027 bayan nasarar da ya samu.

APC ta ce Tinubu ya samu ƙuri'u kusan miliyan 11 inda ya doke abokin hamayyarsa Stanley Osifo da suka fafata a zaɓen fitar da gwanin da aka gudanar.

Shugaban na Najeriya ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓukan fitar da 'yan takara a jam'iyyarsu ta APC, inda ya ce ba wa kowa dama ya tabbatar da ci gaban dimokraɗiyyar musamman a jam'iyyarsu.

APC dai ta ce ta gudanar da zaɓen da ya tabbatar da Tinubun a matsayin ɗan takararta na shugaban kasa a kananan hukumomi 774 na jihohin Najeriya 36.

Shugaban kwamitin zaɓen shugaban ƙasa na APC, Sanata Anyim Pius Anyim ne ya sanar da sakamakon ranar Lahadi, bayan kammala tattara ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen na ranar Asabar a faɗin Najeriya.

Ya ce Tinubu ya samu ƙuri'u 10,999,162 yayin da abokin karawarsa kuma ya samu ƙuri'u 16,503.

Jam'iyyar ta miƙa shaidar lashe zaɓen ga Tinubu da kuma tutar jam'iyyar a matsayinsa na ɗantakararta na 2027.

Daga bisani Osifo ya taya Tinubu murnar lashe zaɓen, inda ya gaisa da shugaban a wajen taron.

Tuni dai Shugaba Bola Tinubu ya karɓi shedar lashe zaɓen fi da gwani na jam'iyyar APC ranar Lahadi.

Shugaban Jam'iyyar a Najeriya, Farfesa Nentawe Yilwatda ne ya miƙa wa Tinubu shedar a cibiyar taro ta ICC da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

Hakan ya zo ne bayan da Tinubu ya doke mai ƙalubalantarsa a zaɓen Stanley Osifo.

Yadda aka yi zaɓen a jihohi

Jam'iyyar APC ta gudanar da zaɓenta na fitar da ɗantakarar shugaban ƙasa a mazaɓu 8,809 a ƙananan hukumomi 774 da ake da su a ƙasar.

Wasu gwamnonin APC ne suka zama jami'an tattara sakamakon zaɓe a jihohinsu.

Bayanai sun nuna cewa an samu masu zaɓe da aka yi wa rajista 12,643,306.

Ga yadda aka yi zaɓe a jihohin Najeriya har da Abuja, babban birnin ƙasar.

Lagos - 814,988

Adamawa - 644,149

Kaduna - 618,914

Imo - 582,960

Kano - 500,852

Katsina - 467,003

Gombe - 450,517

Borno - 414,988

Delta - 407,646

Akwa Ibom - 389,197

Enugu - 383,382

Benue - 374,787

Plateau - 241,720

Bayelsa - 227,192

Ebonyi - 207,579

Jigawa - 206,520

Kogi - 197,370

Taraba - 183,698

Ondo - 181,996

Niger - 175,487

Abia - 161,005

Bauchi - 156,541

Ogun - 322,485

Zamfara - 321,579

Kwara - 310,990

Sokoto - 301,000

Kebbi - 292,972

Nasarawa - 285,436

Rivers - 280,082

Yobe - 253,804

Cross River - 113,911

Edo - 121,098

Oyo - 142,754

Osun - 100,888

Ekiti - 85,340

Anambra - 43,034

FCT - 36,103